Daga Sagir Kano Saleh
Aisha ta bayyana cewa rashin yardar ta kai matsayin da har Buhari yakan kulle kansa a daki tare da kin cin abinci.
Aisha, mai dakin tsohon Shugaban Kasa, Marigayi Muhammadu Buhari, ta bayyana ji-ta-ji-tar da aka yi ta yadawa a Fadar Shugaban Kasa a lokacin mulkinsa, ta kai ga har ya yarda cewa tana neman hallaka shi.
Aisha ta bayyana cewa zargin ya kawo matsala a yanayin cin abincin Buhari, wanda hakan ya yi sanadiyyar tabarbarewar lafiyarsa, har ta kai ga ya shafe watanni yana jinya har da karin jini a kasar waje a shekarar 2017.
Ta yi wannan bayanai ne a cikin littafin tarihin rayuwar Buhari mai suna ‘Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari,’ wanda Charles Omole, ya wallafa.
Aisha ta bayyana cewa rashin yarda da rade-radin ya haifar a tsakaninta da Buhari, ta kai matsayin da har yakan kulle kansa a daki tare da kin cin abinci yadda ya saba.
Ta ce tsawon shekaru, ita ke kula da abincinsa da magungunan da yake sha, masu matukar muhimmanci ga yanayin lafiyarsa, amma daga baya rashin cin abincinsa yadda ya kamata ya fara shafar lafiyarsa.
A ranar Litinin, kimanin wata shida bayan rasuwar Buhari, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci kaddamar da littafin, a Fadar Shugaban Kasa, bikin da ya samu halarcin Aisha da iyalan Buhari.
Ta bayyana cewa, “Rashin lafiyar Buhari ba shu’umi ba ce, ba kuma guba ba ne. Tsawon lokacin da sha’anin lafiyar abincinsa ya dauka ne.”
Littafin ya bayyana bayan zaman Buhari shugaban kasa da dawowarsa Fadar Aso Rock, kula da abincinsa ya koma hannun masu kula da shi, wanda haka ya rika haifar da jinkiri, rashin cin abinci a-kai-a-kai da kuma rashin shan magungunansa yadda ya kamata.
Ta ce marigayin ya shafe kusan shekara guda ba ya cin abincin rana yadda ya kamata, sa’annan rashin kula da cin abincinsa yadda ya sa ya yi rauni sosai.
Wannan ya yi sanadin tabarbarewar lafiyarsa, har ya yi wata tafiya ta tsawon kwana 154 zuwa kasar Ingila domin kula da lafiyarsa a shekarar 2017, ya mika ragamar shugabanci ga mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.
Bayan dawowarsa ya bayyana cewa bai taba yin rashin lafiya kamar wannan lokacin ba, inda har aka yi masa karin jini a kasar waje.
Littafin ya bayyana cewa dadewar Buhari a kasar waje ta haifar da ce-ce-ku-ce, inda wasu ke zargin cewa an ba shi guba, wasu kuma na cewa mutum mutuminsa ne aka maye gurbinsa da shi.
Amma Aisha ta karyata wannan tunanin, tana jaddada cewa rashin kula da cin abincin yadda ya saba ne tushen matsalar rashin lafiyarsa.
Ta bayyana cewa likitoci a asibitin da ya je a London sun rubuta masa tsarin cin abinci da shan magunguna masu kara sinadarai sosai, kuma ta tsaya kai da fata wajen ganin ana bi sau da kafa.
A cewar littafin, Buhari ya samu murmurewa bayan da aka bi umarnin likitocin yadda ya kamata, inda Aisha ta bayyana cewa, cikin ’yan kwanaki ya murmure, har ya fara karbar baki.

