Labarai da Ra'ayi
Labarai, Makaloli da Ra'ayoyi

Koma zuwa "Labarai, Makaloli da Ra'ayoyi"

Labarai, Makaloli da Ra'ayoyi
MediaHausa
Site Admin
Masu rubutu: 121
An haɗa: Talata Oct 21, 2025 9:40 am
Lambobi:

     MediaHausa Site Admin    Masu rubutu: 121    An haɗa: Talata Oct 21, 2025 9:40 am    Lambobi:   


Buga by MediaHausa »

Esin127 *Legacy Post Number 4 from MediaHausa
Topic: Kishin Kasa
Timeline: 2010-06-14 22:53:44


Kishin Kasa

A Rubuce Da Buhari Daure

Akan sami kowane irin ci gaba da kishi. Hakan ya tabbatar mana da cewa kishi shi yake ba mutum matsayi da sanin darajar kansa, ta yadda zai kare mutuncin kansa.

Amma ta yaya za mu raba kasar mu, ko mu bi shawarar wani kan cewa ba za mu warware matsalolin da suka addabe kasar nan ba sai an raba ta. Tabbas a tarihin Najeriya an sha samun tashe-tashen hankali, har yaki aka yi a sunan kwatar kai, yayin da sojoji suka yi nasarar dunkule kasar nan a waje daya, amma daga bisani akwai bangarori da suke da burin kama gaban kansu. Shugaba Mu’amar Gaddafi ya ba da shawarar a datsa kasar gida biyu, daga bisani ya ce ya kamata a kacal-cala kasar gwargwadon kabilunta, bisa barazanar da ake fuskanta a dalilin rikice-rikice addninai da kabilanci.

Yayin da wasu mutane daga cikin manyan Kiristoci da kabilun kasar nan suka goyi bayansa, har suke cewa ya yi hikima, ya yi hange, abin tambaya shi ne shin raba kasar nan zai kawo zaman lafiya tsakanin mutanen kasa. Ko a ganinsu Musulmi da Kirista ba su iya zama tare, sai ana rikici? Tabbas duk wanda ya kalli tarihi ya san Musulmi da Kirista sun yi zaman lafiya, kuma ko a yau suna zama lafiya a kasashe da dama, kuma a wasu kasashen ba a taba ji sun yi rikici ba!.

Bari in warware zaren da abawa. Da farko wai waye Gaddafi, kuma wa ya ba shi izinin da zai ba wasu daliban Najeriya a Tarabulus shawara a kan kasar da ta linka Libya a yawan jama’a da addinai, mutumin da wasu shuwaganni ke kallo kamar mahaukaci, mutumin da ya yi jifa a kasuwa, har a ce wasu na neman ganin ya hango mana abin da zai fi mana alheri, idan da za a raba kasar nan da an raba ta tun kafin ya ba da shawara.
A raba ko kar a raba ana tare, dole sai mu ci gaba da dogaro da juna, koda a sunan makwaftaka ce, sannan idan maganar Jos ce, a ganina idan an so za a iya binciko da hukunta wadanda ke da hannu a cikin ta’addanci da ake a sunan addini da rashin tsaro, har kowa ya sami zaman lafiya tsakanin mazauna da baki, a hukunta duk wanda ya yi laifi mana a yi tsarin ba sani ba sabo a gani idan kowa bai shiga taitayinsa ba, amma a yanzu wa zai je Jos?

Maimakon mu yi gaba sai mu rabu! idan kuka lura duk wanda ya rabu ya ragu, in son samu ne mu kara dunkulewa a sunan Afrika, domin ko an raba sai an ci gaba da samun matsaloli idan mu ka dubi kasashen da suka rabu har yau su na zaune a inda suke kuma sun a samun matsalolin da suka fi yadda suke a da, misali; kamar Pakisatan da Indiya, ai ba ma sai mun je nesa ba har yau kuna jin ana rikici akan iyakar Najeriya da Kamaru duk da mun bar musu Bakasi!, ana kashe-kashe a iyakar Habasha da Eritiriya, sannan a iyakar Arewa da Kudancin Koriya an dana tarko. Kuma idan muka kalli Czechoslobakia da aka raba ta tsakani Czech da Slobak ai kabilu biyu ne dama a kasar, kuma har yanzu a dabaibaye suke.

Idan muka waiwaya baya zamu ga irin fahinmtar manyan mutane irin su Kwame Nkurma na Ghana wanda ya karfafa da’awarsa ta; “mu yi kishin kanmu, mu karfafa juna sune sirrin kowane irin ci gaba”, idan mu kasance mu sami ci gaba bayan an sami ‘yancin kai, a yi dimokuradiyya tsantsa. Ya zaka hada shi da irinsu Gadafi masu nuna a hade kasashen Afirka, kuma su shugabanci Afirka, duk da kasar na da wuyar shiga, shi kansa bai nuna misalin za a tafi tare ba, amma so yake ya jagoranci mutanen Afirka, shi kansa soja ya yi juyin mulki, bai sauka ya ba farar hula ba, kuma ya shafe sama da arba’in yana kan karagar mulki, sannan ya wayi gari a zamanin dimokuradiyya, yayin da gogan ya gaza fahimtar cewa Bakaken sun yi wayo!, ba mamaki suka yi hannun riga da Larabawa a Gabas ta Tsakiya, sannan ya nemi shiga a wajen Turawa don ya ci gaba da kwanciya akan gadonsa.
Mutanen Najeriya sun koyi zama tare da dadi kuma ko cikin wahala, idan muka biye wa wasu za mu kara shiga uku, shin baku taba ji ana cewa babban banza ba?, ko don muna da yawan jama’a da man fetur ana cewa mune manya ko giwar Afirka, amma ai akan ce manya kutare, ko Najeriyar ta kamu da kuturta. Zan rufe da kawo maganar Janar Muhammadu Buhari “Bamu da kasar da ta fi Najeriya, dole mu tsaya mu raya kasarmu, mu rayu tare”.

Buhari Daure
buharidaure@ymail.com


**{Legacy activities, comments etc counter: 882; topic series: 1; forum: MediaHausa; legacy score: 5; legacy ratings: 1; rating_ip: **.*3.55.209; associated: 1- /*}

Aika amsa

Kishin Kasa



Bayar da Amsa

Koma zuwa "Labarai, Makaloli da Ra'ayoyi"

Bayar da Amsa