Topic: Arewa da tsarin karba-karba
Timeline: 2010-10-05 18:41:21
Arewa da tsarin karba-karba
A Rubuce Da Aminu Jibril
Yarjejeniyar karba-karba da ’yan Jam’iyyar PDP ta tsara tana dago muhimman batutuwa, ba ma a cikin jam’iyyar kadai ba, har da masu adawa da ita, da wadanda ba ’yan siyasa ba.
Wannan tsari na PDP ya haddasa rabuwar kawuna a Arewa, a kuma daidai lokacin da Arewar ba ta ci amfanin tsarin ba, don ko rabin-rabin amfanin da Kudu ta samu, ba ta samu ba, sakamakon rasuwar Shugaba Umaru Musa ’Yar’aduwa. Allah Ya jikansa, amin.
kungiyoyi da daidaikun jama’a mabambanta ra’ayi kan batun sai kara bayyana suke. Daga cikinsu akwai dattijai da matasa. Kowane kuwa yana ba da hujjojinsa na kare matsayinsa. Sai dai, gaskiya daya ce, kuma za ta yi halinta. Masu hankali na kallo da nazarin rawar da kowa ke takawa.
Abin mamaki, hatta jiga-jigan ’yan siyasar Arewa, kamar gwamnoni da sanatoci da ’yan majalisun tarayya na PDP sun kasa fitowa su kwato wa kansu hakki balle na al’ummarsu. Kowa ya yi gum, saboda tsoro ko dakikanci, ko dai wani dalili da su suka fi kowa sani.
A taronsu na ranar 1 ga watan Yulin nan, gwamnonin Arewa sun karbi bakuncin wasu dattijan Arewa, inda suka nuna musu muhimmancin tabbatar da ganin an ba yankinsu hakkinsa na cigaba da mulki har zuwa shekara ta 2015, sun kuma dage a kan hakan.
A nasu bangaren, gwamnonin sun ce za su tuntubi al’ummominsu don sanin matsayinsu, kai ka ce ra’ayoyin al’ummarsu na da tasiri a wurinsu. Ana cikin haka sai ga shugaban gwamnonin Arewa, Gwamna Babangida Aliyu na Jihar Neja yana cewa, babu abin da zai hana Goodluck takara a shekarar 2011.
Na san akwai wadanda ke kallon batun ta fuskar addini, har suna cewa, a tsame su daga hankoron barin mulki a Arewa zuwa 2015, domin a nasu ganin, ba mabiyin addininsu ne zai yi shugabanci ba, saboda haka gara mulkin ya zauna a Kudu.
Masu neman Goodluck ya fito takara, ba wani abu suke so ba illa su ma a ci ganimar kasa da su, domin sun san abin da shugabannin ke yi na dibar dukiyar jama’a, suna raba wa masu yi musu kamfe a kafafen watsa labarai.
Abin haushi kungiyoyin suna fakewa cewa, tsarin mulki bai hana Goodluck takara ba, suna yawo da hankalin jama’a. Abin da kurum ya rage su fada mana shi ne, kada ma Goodluck ya bata lokaci wajen takara, ya ci gaba da mulki kawai har shekara ta 2015.
Wadansu kuma cewa suke yi ai an yi shugabanni a Arewa amma babu abin da suka tsinana wa yankin. Wannan shi ne dalilinsu na amincewa da duk wanda zai yi shugabanci ya yi. Haka ne, akwai shugabanni a Arewa da babu ruwansu da talakawa, kuma su suka fi yawa. Har yanzu, kuma har duniya ta nade, ba za a daina samun na kwarai ba. Misali marigayi Umaru Musa ya kwatanta kishin kasa da Arewa. Yashe Kogin Neja wani babban aiki ne da aka dade ana begen ya tabbata, sai a lokacinsa aka fara aikin. Ya fara gyara wutar lantarki, duk da ba a sami kaiwa ga yadda ake so ba. Uwa-uba, ba a zarge shi da sace dukiyar jama’a ba.
Kamar yadda muke da miyagun shugabanni a Arewa, su ma Kudu suna fama da wannan annoba. Tun da haka lamarin yake, me zai sa mu sadaukar da hakkinmu a bagas?
Bayan rantsar da Jonathan shugaban kasa duk da mutanen Neja-Delta suna kuka da shi da sauran shugabannin da suka fito daga yankin bisa rashin adalci da suke yi musu na kwashe biliyoyin kudinsu suna kai wa kasashen waje, duk da haka sun ce masa kada ya kuskura ya dawo gida muddin ya ki fitowa takara a shekara ta 2011, saboda sun san muhimmancin shugabanci.
Amma mu an sami wadansu manya da kanananmu suna zubar da mutuncinsu wajen kiran ya fito takarar. Wadansu saboda a ba su kwangila ko mukaman siyasa ko kudi ko a ba ’ya’yansu mukamai. Tsofai-tsofai za ka ga suna zuwa wurin Jonathan suna zubar da mutuncinsu da sunan nuna masa goyon baya da mubaya’a.
Amma ba a taru an zama daya ba, domin muna da zaratan dattijai da matasa irin su Dattijo Tanko Yakasai da Lawal Kaita da sauransu. Kuma muna matasa da za su yi duk abin da za su iya wajen ganin ba a tauye wa yankinmu ’yancinsa ba.
Abubuwa sun tabarbare a Arewa, shugabanninmu daga su sai iyalansu da ’yan kanzaginsu, sun ki yi wa talakawa abubuwan da za su amfane su da dukiyarsu, sai bushasha da gasar tara dukiyar da ba za ta amfane su ba.
Komai lalacewar al’umma ba a rasa na kwarai, don haka mu neme su, mu sanya su gaba su jagorance mu. Irin wadannan mutane na kwarai ba za su yarda a hada baki da su a cuce mu ba. Ba za su yarda suna sane a cutar da mu ba.
bincent Ogbulafor Ibon kirki, saboda Arewa aka yi masa bi-ta-da-kulli, aka raba shi da shugabancin Jam’iyyar PDP. Laifinsa ya ce Arewa ce ke da gurbin shugabancin kasa a PDP a zaben badi. Da jiga-jigan jam’iyyar daga Arewa aka yi masa wulakanci.
Yanzu sun kawo Cif Okwesileze Nwodo ya shugabanci jam’iyyar, kuma ya ce za su sake nazarin tsarin karbar-karba. Yanzu mun gane an kori kare ne daga gindin kanya don a ci. Kuma manufarsu ita ce a yi wa Arewa kwace da murdiya da fashi.
Abin da za mu gaya wa Jonathan da Nwodo da Babangida Aliyu da duk mai cewa Jonathan ya fito takara a badi, shi ne a bari Arewa ta kammala nata zangon a 2015, kamar yadda Kudu suka yi a lokacin Obasanjo, in ya so sai a yi watsi da karba-karbar dungurungum.
Muddin ba haka aka yi ba, an ci amanarmu, an cuce mu, an yaudare mu, an tauye mana hakki, kuma duk wanda ke da hannu cikin wannan zalunci, daga cikinmu yake, ko daga waje, a fili yake ko a boye, Allah Ya isa! Ba mu yafe masa ba.
Wace irin magiya ce ba a yi mana a lokacin da Obasanjo ya fito, ko aka fito da shi don takarar shugaban kasa ba? An ce mana mutumin kirki ne, ba ya nuna bambancin kabila. Me gari ya waya, musamman a zangonsa na biyu, wace irin aya ce bai soya mana a hannu ba? Mun yi kuka da hawaye. Da rokon Allah muka samu ya tafi. Sai ga shi an manta, ana son a maimaita wancan kuskure.
Duk da wancan cin zarafi da Obasanjo ya yi mana, ba a sami wani daga wannan bangare ko nasa bangare da ya fito ya kalubalanci tsarin karba-karba ba, sai da ya zo nan. Shi kansa Obasanjo ya nuna dacewar sake nazarin tsarin saboda ya san ya ci moriyarsa, yanzu kuma nasa ne ke ci, don haka gaba ta kai shi.
Aminu Jibril,
Unguwar Sanusi, Kaduna.
**{Legacy activities, comments etc counter: 963; topic series: 1; forum: MediaHausa; associated: 4- /*}