Topic: Siyasar Kano a kan Sikeli
Timeline: 2010-10-05 18:44:00
Siyasar Kano a kan Sikeli
A Rubuce Da Ado Musa, Unguwar kauragoje, Kano
Siyasa rigar ’yanci, a siyasa ba a aboki tabbatacce sai dai a tabbata a kan ra’ayi daya.
Siyasa ke nan, ko dimokuradiyya wacce ake yi wa kirari da gwamnati ta jama’a , wacce jama’a suka zaba.
Don haka ya sa na yi wani dan takaitaccen nazari tare da waiwaye wanda Hausawa sukan ce adon tafiya, wato duk mutumin da yake bibiyar siyasar Kano a yau to hakika zai san cewa tukunyar siyasar jihar ta dauki sabon salo, wanda manazartan siyasa su ka yi hasashe cewa duk jam’iyyar da ta kasa zama tsintsiya madauri daya wajen zaben fitar da gwani a matakin gwamna hakika tarihi zai maimaita kansa. Ma’ana tarihin siyasar Jihar Kano ba bakon abu ba ne, A siyasar kasar nan , an yarda talaka ke yin juyin juya hali a cikin dare daya kamar dai yadda ya faru a 1991 tsakanin S.D.P da N.R.C da kuma 2003 tsakanain P.D.P da A.N.P.P
Danbarwar siyasa da rikicin cikin gida da ya dabaibaye kowacce jam’iya a Jihar Kano. Da hakilo da’ yan takara suke yi a tsayar da su a kujerar Gwamna, wannan rikicin na cikin gida da yake faruwa tun da ga jam’iya mai rike da madafun iko a jihar (A.N.P.P ) wacce take rike da mulki tun shekarar 2003 zuwa yau karkashin shugabancin Malam Ibrahim Shekarau (Sardaunan Kano).Kafin a zo zaben fitar da gwani a matakin gwamna, abin ya zo wa jam’iya cikin sarkakiya ya kawo rabuwar kan ‘ya’yan jam’iya gida biyu abin takaici ne a sahihiyar dimokuradiya a Jihar Kano.
Haka su ma babbar jam’iyar adawa ta P.D.P ke rikicin cikin gida wanda ya hana su kaiwa ga gaci tuntuni ya sa suka kasa cin zabe tun shekarar (2003) saboda bangarorin biyu da kowanne yake gogayyar son fada a ji a cikin jam’iyar.Kamar,bangaren marigayi Dakta Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi wanda suke kiran kansu P.D.P garkuwa wanda ako da yaushe suke korafin an kasa yi musu adalci wajen hana su fada a ji a jam’iya duk da su suna ganin cewa da su aka kirkiro da jam iyar P.D. P kuma shugabansu Abubakar Rimi shi ne ma ya rada mata suna a gidansa da ake kira gidan akida
Su kuma bangaren kwankwasiya wanda Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ke shugabanta, su suna gani dole ne su rika fada aj i a jam’iyar, domin su suke kashe mata kudi da duk wata da wainiya tun bayan faduwar su zabe a (2003).
Jam’iyar C.P.C kuwa wacce ta yi fitowar bazata duk da yake manazarta sun yi hassahen futowarta kuma babban jigo daga cikin ta Janaral Muhammadu Buhari ya kara wa jam’iyar farin jini tare da samun dimbin magoya baya musamman talakawa masu son canji na gari wannan ta sa jam’iyar ta sa mu karbuwa a Jihar Kano amma rikicin cikin gida da kokawar shugabanci a cikin jam’iyar na so ya sa su kasa cin zabe.
Shawara ta ga jam’iyu musamman masu fada a cikin ta, ya kamata adalci ya rika zuwa farko wajen gudanar da zabe na cikin gida a kan gaskiya da adalci. Domin a mafiya yawan jam’iyu su na kagawa jam’iya dan takarar da ba shi da farin jini ga jama’a ballantana al’umar da za a wakilta Ta haka za ka ga ‘ya’yan jam’iya su na samun sabani da shugabaninsu, shugabani jam’iyu su hankalta wajen fitar da dan takara don kada tafiyar ku ta yi gargada kafin babban zabe mai zuwa.
Shawara ta biyu ita ce, duk wanda Allah Ya bawa mulkin Jihar Kano a ko wacce jam’iya yake to mu Talakawa ba abin da muke nema sai ya dora a kan ayyukan da gwamnatin da ta gabata ta tsaya kamar, fadada tituna da kirkiro sababbi,da inganta harkar lafiya,da samar da wadataccen ruwan sha mai tsafta birni da karkara da , inganta harkar ilimi, da samawa matasa ayyukan.
da mu al umar Jihar Kano ba za mu taba manta wa da gwamnatin mai girma Sardauna Kano ba sabo da ya kirkiro ma’akatu guda uku domin sama wa matasa ayyukan yi wato Hisba da adaidaita sahu da kumma ma`aikantar shara. Haka kuma, ga `yancin fadar albarkacin baki da ya bawa kowaacce jam’iyar adawa. Ya kamata a kullum mu kasance masu dogaro da kan mu da kuma tsayawa da kafafunmu Mu guji bangar siyasa ko jagaliya abin bakin ciki za ka ga matashi yana wulakanta rayuwarsa lokacin kamfen. da yawo da makamai tsirara a rumfunan zabe.
Ya ‘yan uwana matasa ku sani su ‘ya’yansu ba sa zuwa kamfen ko gurin zabe, kuma da zarar dan takara ya kai ga gaci ba za ya kara wata mu’amala da ku ba sai dai kawai da sassafe ya rarraba ‘yan kudadan da ba su taka kara sun karya ba a kofar gidansa ko ofis dinsa mu kasance masu fadakar da su alkawauran da su ka daukar mana a lokacin kamfen in kuma sun ki lokaci na gaba sai mu hana su kuri’un mu a saka mu kuma raka sannan komai dadewa kada mu karaya mu jira don karbo abin da mu ka zaba ta haka za mu kwato wa kawunanmu ‘yancin a cikin ruwan sanyi ba tare da mun kashe wani ko raunata ‘yan uwan mu ba.
A karshe a sani cewa Allah Ya na ba da mulki ga wanda Ya so alokacin da Ya so don haka Allah Ya ce duk mutumin da na bawa mulki to ya kwatanta gaskiya da adalci domin samun kyakkywan rabo gobe kiyama.
Ado Musa, Unguwar kauragoje, Kano mamba a kungiyar muryar talaka
08069186916
**{Legacy activities, comments etc counter: 1367; topic series: 3; forum: MediaHausa; legacy score: 9; legacy ratings: 2; rating_ip: ***.*14.31.188; associated: 3- /*}