Topic: Rijistar layukan sadarwa na salula a Najeriya illa ce ko muhimmanci?
Timeline: 2010-10-05 18:59:49
Rijistar layukan sadarwa na salula a Najeriya illa ce ko muhimmanci?
A Rubuce Da Ahmad Abubakar Arab Azare
Tun bayan bayyanar wayar salula a Najeriya ne al’ummar kasar ta samu kyakkyawan sauyin muhimmancin isar da sako, na kar-ta- kwana cikin kankanen lokaci.Hakika wannan zamani da ya taho mana da guguwar sauyin rayuwa ta ci gaba na yin mu’amala da wayar sadarwa ta salula cikin sauki. Sai dai kuma ba a nan gizo ke sakar ba, masana sun tabbatar da gaskiyar dukkan wani abu na ci gaban da zai zo wa al’umma, yana da nasa alfanu da kuma illa.
Yanzu haka jama’a sun zama shaidu na hakika, dole ne a samu bata-gari masu ci da gumin wadanda ba su ji ba ba su gani ba. Wasu kuma sukan kirkiro da wata manufarsu boyayya ta daban da za ta kasance babbar illa da hadari ga al’umma masu hada- hada da layukan wayoyin salula. Najeriya ta yi kaurin suna wajen ayyukan damfara da baba-kere. ’Yan damfara suna daukar hankulan mutane da yin kwakkwaran tunanin a zaton su za su iya dace wa aiken sakon 419 ya fada jakar akwatin makwadaita masu son banza su ne aka fi yawan damfara.
Hanyoyin damfarar sukan aikata su salo iri-iri. Samfurin damfara guda daya kamar haka:na daya daga cikin wadanda suka dace da lashe garabasar Naira dubu dari biyu, saboda haka cikin kankanen lokaci ka aiko mana da lambar ajiyar bankinka, ko ka aiko mana da wani kaso na kudi daga cikin kudin da ka yi nasarar samu. Kadan ke nan daga cikin sakonnin damfara. Su kansu kamfanonin layukan salula suna daya daga cikin wadanda suke aikewa da sakonni cewa ka aika wata lamba da suke bayarwa domin neman dacewa da nasarar lashe garabasa. A bayan-baya nan sun sake sabon salon aike wa duk masu amfani da layukansu sakonni wanda ya yi kusa da na yan damfarar. Suna cewa ka dace da lashe nasarar gasar kaza da kaza. Shin irin wadannan sakonni anya ba sa matsarwa duk masu aiko da layukan salula? Wadane irin matakai hukuma za ta iya dauka?Ke nan ana yaki da `yan damfara ga kuma `yan damfara da suke da rijista da gwamnati.
Hukumar sadarwa hadin gwiwa da hukumar sanya idanu kan tsaro na ta binciken yadda ta’addanci da miyagun ayyuka suke karuwa. Domin ragewa ko dakile ayyukan cikin gaggawa ya sa ala tilas umartar kamfanonin layukan salula da ke cikin Najeriya. Su dauki mataki da hanyar binciko duk mai yin irin haka cikin hikima. Kamfanonin sun sha alwashin dakilewa ko rage wani kashi daga ciki. Jim kadan bayan wani lokaci ne kamfanonin layukan suka dukufa ka’in da na’in aiken nan take na sakonni zuwa ga ilahirin mai mu’amala da layukansu cewa ya garzaya ofishinsu mafi kusa domin ya tabbatar an yi masa rajistar layin wayarsa. Ba don komai ba sai don tabbatar da tsaro ga al’umma,da sanin cikekken bayanin alkaluman illahirin duk masu amfani da layukan wayoyin salula a Najeriya.A ciki har da gano yawan kira da karba, yawan aikewa da sakonni da duk wani abu da mai amfani da layin salula zai aikata to cikin sauki zai tattare ko wane irin abu. Sharadi rijistar ya kunshi cikakken adireshi, shekarar haihuwa da jinsi da daukar hoto da daukar zanen dan yatsa da kuma lambar wayar salula da sauransu.Tuni har wasu masu amfani da layukan sun fara garzayawa ana musu rijistar jim kadan bayan bayyana sakon.
A cikn watan Agusta ne doka za ta fara aiki duk wani mai sayen layin wayar salula sai an yi ma sa rijistar layin . Sannan a cikin watanni masu zuwa hukumar sadarwa ta Najeriya za ta fara ba da umarnin aiwatar da rufe layukan wayoyin salula wadanda ba a yi musu rijista ba. To wannan ba karamin aiki ba ne, dole ne sai an kebance wani lokaci mai tsawo kafin cimma burin karade dukkan lungu da sako na kasar nan.
A karshe wane irin tsatstsauran mataki hukumar za ta dauka ga masu ayyukan cin zarafi damfara, sace-sace, kuma abaya ana kama masu lai*****a hukuncin ne kuma sai ya kasance mai dokar barci ….Akwai masu amfani da layukan wasu su yi laifi alhali kuma ba mai layin ba ne ya aikata wannan laifi, imam dai an sace wayar bai kai sanarwar gaggawa ba zuwa ofishin `yan sanda. Kuma a boye, wani zai iya amfani da layin wani, hukunci ya hau kan mai layin da bai san hawa ba, balle sauka ko ya za bi a kwato masa hakkinsa?. Wayoyi kirar kasar Caina wadanda ake iya sauya murya zuwa mace ko karamin yaro, ya za a yi a gano masu aikata laifi ta wannan hanyar. Ko ma dai wane irin laifi ne, tabbas wanda zai iya shiga tsaka mai wuya wanda ya yi rajista ne komai nashi yana wurin kamfanin masu kula da shige da ficen kira. babu wanda ya yi laifi sai shi, shin ko ya batun manyan mutane da aka sani suna aikata tsiya? Da sauran abubuwa iri iri. Fatanmu dai a yi adalci da binciken kwakwaf kafin hukunta mai laifi, ko tuntubar shi.
Daga: Ahmad Arab Abubakar Azare Katagum Jihar Bauci. I-mel arab.34@hotmail.com
**{Legacy activities, comments etc counter: 1287; topic series: 1; forum: MediaHausa; associated: 1- /*}