Topic: Su waye matsalar Najeriya?
Timeline: 2010-10-05 19:05:31
Su waye matsalar Najeriya?
A Rubuce Da Abyy-Rumaisa’u, Abdullahi Bn Yusuf
Bayan dogon hutu,sakamakon karo ilimi da na tafi,Allah Ya sa yau na fara da wannan tsokacin.
Ganin yadda kasa ta Najeriya ke kara tabarbarewa kullum.Duk wanda zai fadi gaskiya ko kuma ya ba ka tahirin kasa ce maka zai yi gara jiya da yau.To,don Allah su waye matsalar Nijeriya? Talakawa ko shugabanni?Bincike ya nuna cewa duk wanda ya rayu a Nijeriya, tabbas zai iya rayuwa a cikin Aljannu,kuma ya yi nasara. Kodayake a Nijeriya an ce wai, (Inji Jaridar Aminiya) bakaken Aljannu kan tilasta Uba ya tara da ‘yarsa. Hodi jam! Sharrin dan-Nijerya ya wuce mutum har ya dangana da aljan, to don Allah kada a wuce nan, domin bayan aljan sai Mala’iku, ko kuma wani ya ce Allah (SWT) ne Ya kaddara masa hakan. Nijeriya kasa ce mai fadi da yawan jama’a, wannan ya sa ni zan takaita batu na a kwaryar gari na kawai, domin nan ne zan iya fadin abin da yake na gaskiya, idan na ketare gari na kuwa to zan iya yin kure. Amma zan fara ne da shugabannin kauyenmu.
Allah sarkin zaki (Inji barawon takanda), yau a kauyenmu shugabanni sun mayar da ran talaka ba komai ba, duk wanda ya saba musu, ko ya ki bin ra’ayinsu, tabbas zai kwana lahira. Kada ku manta a kauyen ne aka kashe Liman, mahaddacin Al’kur’ani a masallaci yana bada sallah. Har ila yau, a kauyen ba ka jin dan wani mai-hali ya bace, kullum sai Dan-talaka. Wani abun mamaki shi ne,idan an kama wani babba ko mai kudi da yaro ko sassan jikin mutum, kwana biyu sai ka ji labarin ya mutu, wai mai ke faruwa ne? wannan ko shi ne KITIFIFI?
Yau an wayi gari a kauyen masarauta masu mulki da masu kudi sun mai da fagen taron saukar karatun Al’ku’anin yara dandalin zaben ‘yammata.Duk lokacin da aka ba su katin gayyata suna zuwa don su zabi wacce za su yi lalata da ita ko ta so ko ta ki. Idan har wani nata ya yi kokarin ba ta kariya,‘yan barandar ya haji sa yi maganin sa. Ita ma idan ta yi gigin fallasawa, to ta san kwanan zancen. To don Allah mene ne hukuncin mai aikata hakan,? Wurin murnan kammala karatun littafin Allah ya koma filin zabi-ka-darje ke nan? Ina zamu ne? ‘yammata da yawa sun sami ciki, uba ko dan-uwa ko waye bai isa ya yi magana ba. Ko su je su zubar da cikin ko a haifa musu dan zina ko dan fyade, wanda duk ka zaba. Wannan shi ne KUTUBALBAL.
Wata kwamacalar ita ce gida da mata hudu, da ‘ya’ya maza da mata masu yawa, yaron wani dakin na iya yin tarayya da ‘yar-wani dakin, tunda ba uwarsu daya ba. Mai gidan yakan je wajen saukar karatun Al’kur’ani don ya darje, ya kan tafi Ingila don ya more, ko zuwa Dubai da Amurka don ya gwangwaje. Haba tsoho, kana tunani yau shekarunka nawa? A iya tunani na, ka kai shekarun “YIN TASBIHI DA NEMAN GAFARAR UBANGIJIN KA”.
Harkar masu gidan rana kuwa, duk wata hanya don tara dukiya ana bi tare da aika alfasha saduwa da maza ta dubura, kashe yara, mata masu ciki, shan jini, tsafi, kwana da jaka,ko mahaukaciya, cin naman mutum, shan jininsa, kwakule ido, cire al’aura (mace ko namiji), cin naman jarirai,da idan hakkin talaka ya biyo hannunsu a danne.duk wani mummunan aiki da baza ka iya hararowa ba. Irin wannan ayyukan sune shugabanni a kauye na suke yi, suna jagoranci al’umma zuwa ga nasarar duniya da lahira. Anya kuwa? Shin wadanan ba su ne Allah ke fadi abokan fir’auna ba kuwa, wadan da za su jagoranci mutane su gangara da su cikin wuta a ranar kiyama? Ni dai ina jin tsoron hakan zai iya faruwa. Amma ina rokon Allah (SWT) Ya kawo mana mafita. Amma kuma dole mu dauki mataki don kubutar da kawunanmu,da ‘ya’yanmu da kasarmu daga sharrin wadannan miyagun shugabannin (DUJAL KO SHEdANU).
tuni na dauki matakin raba Rumaisa da ‘yan-uwanta da cudanya da ‘ya’yan wadannan miyagun, kuma idan ranar walimar saukan karatunta ta zo, to ba inda zata, idan ya so daga baya a karbo mata shahadar ta.Haka kuma, kullum ina gaya wa Mahalicci na cewa shi kadai ya isa ya kare mu daga kutungwilar wadannan tsofaffin najadu. Allah ka isa, ka isar mana, ka kare mu da duk mumini mai kaunar shari’arKa ta hanyar Al’kur’ani da Sunnah ta tabbata.nan gaba, insha Allah zan fuskantar da alkalami na kan shi kuma talaka.in sha Allah.Shin duk talakan da ya rayu a irin wannan halin zai iya rayuwa cikin bakaken aljannu? Domin abokan karatu na Olarewaju da Oluchi sun ce suna da irin wadanan shugabannin a yankin su duk haka suke. Na gode.
Daga ABUU-RUMAISA’U, ABDULLAHI BN YUSUF.
**{Legacy activities, comments etc counter: 6167; topic series: 3; forum: MediaHausa; legacy score: 15; legacy ratings: 3; rating_ip: ***.*14.31.188; associated: 3- /*}