Topic: Ko ya cancanta ’yan Arewa su goyi bayan Goodluck Jonathan?
Timeline: 2010-10-05 19:57:03
Ko ya cancanta ’yan Arewa su goyi bayan Goodluck Jonathan?
A Rubuce Da Babagana Z. Ibrahim
Na kasance ina biye da mahawarorin da ake yi dangane da zaben 2011 a tsanake, kuma sau da kafa.
Bari ma dai na fara da cewa ni dan Arewa ne mai alfahari da wannan yanki nawa, da ya fito daga yankin da a yau ake kira Jihar Yobe. Na kasance na samu damar yin karatun zamani har zuwa matakin digiri na farko da na biyu, damar da kusan kashi 90 na wasu ’yan jihar ba su samu ba.Ni dai ko kadan ban gamsu da irin yadda ake tafiyar da wannan al’umma ta mu a irin tsarin da ake wanzarwa ba, musamman kuma idan aka yi la’akari da cewa ’yar damar da irin mu ’yan kalilan su ka samu, to kuma fa akwai dimbin wadanda su ka kasa samun wannan dama ninkin-ba-ninkin a yanzu, kuma idan za a cigaba da wanzuwa a hakan, to nan gaba ma ahakan za a cigaba da wanzuwa.
Yayin da na ke yin digiri na biyu, na samu damar yin nazarin yadda sabbon gawurtattun kasashen yankin Asiya su ka yi fafutukar tserar da kawunansu daga kuncin rayuwar koma-baya, su ka tsara wa kansu kyakkyawar turba wadda su ka bi har ta kai su mafita, inda a yau wadannan kasashen sun zama gagarabadau. To yanzu dai ni daga nan ne na fahimci cewa lallai shi cigaban kowacce kasa da al’ummar ta, ba ya tabbata hara sa an wanzar da kyakkywan hangen nesa da kuma kudirun jajircewar kishin aiwatar da manufofin, ba wai kabilanci, bambancin addini ko fifikon wani yare akan wani ne ke tabbatar da hakan ba. Yanzu ga shi Najeriya na kan matakin zaben sabbin shugabanni, sai na ke ganin ya kamata na bayyana wa ’yan’uwa na ’yan Najeriya wasu darussa da fahimta ta, domin mu yi tarayya wajen zabar wa kasar mu kyakkyawar makoma.
Wato haushi da takaici kan kama ni a duk lokacin da na ji wani dan Kudancin kasar nan ya fito ya na kururuwar cewa ’yan Kudu sun zama saniyar-ware a fuskar amfanar tattalin arzikin kasar nan ko kuma su ce yankinsu ya kai ma}urar malejin talauci da zama cikin mayuwancin kuncin rayuwa. To babbar matsalar masu rubuce-rubuce ko yawan yin sharhi, shi ne ba su cika yin tafiye-tafiye ba su na ganin hali da yanayin da wasu yankuna ke ciki, sai dai kawai su tsuguna wuri ]aya a yankin su, su na bayyana yadda daukacin duniya ta ke dai dai fahimtar karamin sanin daga gare su wanda dama kowa ya sani karamin sani kukumi ne.
Ban ki ba don wani ya ce da ni ko ban san abin da na ke fada ba, amma duk da hakan bari na fito karara na bugi kirji na, cewa tantagaryar talaucin kasar nan, ya zarce na Kudancin kasar nan fiye da tunanin mai tunani. Sannan kuma wani abin lura shi ne, yara kanana da ke karatu a Kudu, sun zarta yaranmu na Arewa wa]anda ke makarantu ne sa ba ku sa ba. Baya ga haka kuma an fi gudanar da sabat-ta-juyat-tar- kasuwanci mai karsashi a Kudancin kasar nan fiye da Arewa.
Ni fa kusan babu jihar da ban je fa kafa ta a kasar nan ba. Na ga abin da na gani, kuma akwai kwarararun hujjoji da ke nuni da hakan.
Mun dan fara ganin sauyi a zamanin Jamhuriya ta biyu, ta fuskokin kyakyyawar manufofin su Waziri Ibrahim, Rimi da irin su Balarabe Musa. Sai dai abin bakin ciki duk mun ga yadda su ka karke.
Lokaci ya yi da za mu ceto daukacin al’ummu, kuma wasun mu sun fito domin fafata wannan jan aiki, ina kalubalantar wadanda ke kiran kansu shugabanin Arewa da su fito da ’ya’yansu su kalubalance mu, mu da ke neman kunna wa Arewa fitilar canji. Ba za mu sa ke yarda ’yan siyasa na amfani da ’ya’yan talakawa su na haddasa ru]ani da husuma ba. Idan ma har akwai bukatar yin wata zanga-zanga a gaba, to mu na nanatawa cewa tilas su masu kiran kansu ’yan siyasar Arewa, su saka ’ya’yansu a gaba su jagoranci zanga-zangar ba, ’ya’yan talakawa ba.
Dangane da irin halin da mu ka tsinci kanmu ne a yanzu abin ke daure min kai idan wani ya fito ya na babatun wai tilas sai sabon shugaban kasa ya fito daga yankin Arewa. Me zai yi mana? Wadanne manufofi da ajandodi zai aiwatar?
Na fito karara ina cewa yankin Arewa ba zai tabarbare ba idan dan Kudu ya zama shugaban kasa. Maimakon haka, har ta ma fi saukin mu tunkare shi mu ce wa kowa ne ne kan mulki mu na so a yi mana ayyuka ka za da kaza da su ka dace, kuma su ka wajaba. Babu yadda za a yi don dan Kudu ya hau mulki ya yi watsi da mu. Lallai matsawar mu ka kyautata, mu ka inganta yau, to gobenmu za ta yi kyau sosai.
Na tsaya na yi nazarin mahawarorin da ke ta yi dangane da inda ya kamata sabon shugaban kasa ya fito, idan aka ce a rika bayyana wasu ’yan takarar na Arewa, ai ko kare ba zai ci ba. Sai dai a bar kaza a cikin gashinta kawai. Sai dai kuma bayan na gama nazarin ’yan takarar da mu ke da su a yanzu, sai na ga idan mu na bukatar cigaban ’ya’yanmu, to Goodluck Jonathan ne ya cancanta. Ya yi wa Marigayi shugaba ’Yar’adua mataimaki. dabi’un da ya nu na tun bayan hawansa kujerar shugaban kasa sun nu na cewa ya fahimci inda kyakkywar aniyar Marigayi ’Yar’adua ta sa gaba. Shi ya sa yake cigaba da muhimman kudurorin da su ka fara shiryawa. Ga shi dai ya na cigaba da yasar kogin Binuwai domin tabbatar da jawo teku zuwa Arewa. Ya fara sakin kudin tallafa wa masana’antun saka atamfofi domin farfado da su yadda dubban matasan Arewa za su samu aikin yi.
Babagana ya rubuto ne daga Unguwar Hausari, Maiduguri
**{Legacy activities, comments etc counter: 1170; topic series: 6; forum: MediaHausa; associated: 6- /*}