Topic: Bayyanar mata masu neman mata a kasar Hausa
Timeline: 2010-10-05 20:18:45
Bayyanar mata masu neman mata a kasar Hausa
A Rubuce Da Rabiu Yusuf Yawale
Babu Bahaushe mai mutunci da zai yi maraba da wannan mummunar dabi’ar ta madigo da ta bulla a kasar Hausa,
ta Arewacin Najeriya, wadda mafi rinjayen al’ummar da ke zaune a cikinta Musulmi ne da addininmu ke Allah wadai da tir da madigo ko lesbialism kamar yadda ’yan boko ke kiranta. Madigo ita ce dabi’ar nan da wasu mata suke yi ta neman ’yan uwansu mata da sunan jima’i. Wannan mummunar al’ada ta shigo kasar Hausa a yau ta hanyar mata ’yan boko, musamman masu zuwa Turai ko Kudancin Najeriya da sunan karatu ko kasuwanci. Masu wannan muguwar ta’ada suna yada ta kwararo-kwararo a tsakanin mata tamkar wutar daji.
A yau a kasar Hausa wannan muguwar dabi’a ta madigo ta keta gidajen sarakuna da attajirai da ’yan siyasa da malamai da ma’aikata da gidajen matan aure har da makarantun sakandare da na gaba da su!
Kwanaki na je unguwar Brigade a nan Kano ziyarar wani abokina da daddare, sai ga wani magidanci ya rarako matarsa da kawarta daga cikin gidansa sakamakon kama su da ya yi suna aikata wannan muguwar dabi’a a dakin matarsa!
Sannan wani mai neman matan banza ya taba fada min yadda ’yan sanda a Kano suka kama karuwarsa da kawarta a cikin dakin ajiye masu laifi suna neman junansu a tsakiyar dare, kuma ya shaida min wannan farka tasa tana aikata wannan mugun aiki da wata hamshakiyar ’yar siyasa a Kano mai son fitowa takarar.Ba komai ya sanya ni tunatar da al’umma wannan al’amari ba, sai yadda wannan muguwar dabi’a ke mamayar makarantun ’yan mata da gidajen matan aure wadanda daga su ne ake fidda manyan gobe.
Baya ga fushin Allah da wannan muguwar al’ada ke saukarwa a cikin al’umma, kuma hanya ce ta yada shu’uman cututtuka a tsakaninsu.Watsi da fatali da aka yi da koyarwar addinnin Musulunci ne ya jawo shigowar wannan muguwar al’ada a kasar Hausa, domin Musulunci ya hana mata tafiya ba tare da muharraminsu ba, amma sai iyaye suka dauki dabi’ar tura ’ya’yansu mata kasashen Turai da sunan karatu ba tare da wani tsayayye a kansu ba, inda a irin wadannan kasashe madigo ya kasance burgewa da wayewa, kuma daga nan ne aka dauko mana wannan muguwar dabi’a zuwa kasar Hausa. Kuma shigowar fina-finan batsa da tauraron dan Adam da yanar gizo duk sun taimaka wajen habakar madigo wanda abin bakin ciki har kungiyoyi masu aikata wannan fitina ake da su musamman a Jihar Kano!
Ni, a fahimtata, hanyar da za a magance yaduwar wannan mummunar dabi’a a kasarHausa ita ce komawa zuwa ga koyarwar Musulunci wajen tarbiyyar iyalanmu, sannan masu aure mazaje musamman matasa wadanda suke auren mata ’yan boko da ’yan birni su kasance masu kokarin biya wa matansu bukatunsu na jima’i, ta hanyoyin da matan za su sami cikakkiyar biyan bukata. Kuma hakan ba zai samu ba sai da neman illimi, kuma illimin nan har na jima’i addininmu ya sanar da mu, amma muka yi watsi da shi muka wayi gari matanmu mun jefa su cikin damuwar da ta kai su ga fadawa waccan muguwar dabi’a saboda watsi da hakkokinsu na mu yi wanka, musa turare, mu tsabtace jikinmu da bakinmu kuma mu ba su cikakken hakkinsu wanda addininmu ya hore mu na kada mu haye musu tamkar yadda dabbobi suke yi har sai mun aiki dan aike!
Alhaji Rabiu Yusuf Yawale,No. 1118 Gama,Kano
**{Legacy activities, comments etc counter: 57821; topic series: 4; forum: MediaHausa; legacy score: 9; legacy ratings: 2; rating_ip: ***.*14.31.188; associated: 4- /*}