Topic: Hakika Najeriya ta cika shekara 50 da samun ‘yancin kai, amma...
Timeline: 2010-11-18 15:53:42
Hakika Najeriya ta cika shekara 50 da samun ‘yancin kai, amma...
A Rubuce Da Hamza Ahmad Nasidi Alfindiki
Assalamu alaikum! Jaridar Aminiya, a dade ana yi sai gaskiya j agorar jaridun kasar nan. Ina yi muku fatan alheri. EEE.....hakika Najeriya ta cika shekaru 50 da samun ‘yancin kai, amma har yanzu an kasa samun ingantacciyar hanyar cigaban kasa mai kyau, musamman a bangaren tattalin arzikin kasa,da na jama’ar da ke cikin kasa da na siyasa gaba daya.Saboda haka, na yi nazari da bincike kuma na gano cewa babu wata kasa wadda ta ci gaba a duniya sai da ta yi kwakkwaran tsari mai kyau na shirin cigabanta wato Debelopment planning,wanda da shi ne ake gano matsalolin da ke damun kasa,tare da daukar hanyar da ta fi dacewa don magancewa.
A kasar nan abin ya sha bam-ban, domin tsawon shekaru 50 da ake ikirari,an yi irin wadannan shirye-shirye da yawa. Na karshe-karshe shi ne BISION 2020 na marigayi Shugaba Umar Musa ‘Yar’adua, wanda aka gina shi a kan kawar da manyan matsaloli guda bakwai 7. Abin tambaya shi ne me ya sa shirin yake rushewa ko ake kasa aiwatar da shi yadda ya kamata ko aka tsara tun daga farko?
Dalilai ko matsalolin su ne:(1) Rashin cikakkiyar hukuma mai kula da shirin ta mai dorewa.
(2) Gina shirin bisa ra’ayoyi irin na siyasa ko wasu tsirarin mutane.
(3)Gina daukakin shirin a kan jari-hujja (capitalism) ko abin da ya shafi harkar kudi kawai.
(4)Tsoma bakin Turawan Yamma a cikin shirin (sabon salon tsarin mulkin mallaka).
(5)Saka bukatun talakawan kasa wurin tsarawa amma biyan bukatun masu ruwa da tsaki wurin aiwatarwa (yaudara).
(6) Kawo cikas da karkata salalar kudaden aiwatar da shirin zuwa wasu wuraren don samun riba daga wasu manyan jami’an masu aiwatar da shirin.
(7)Shigar da bukatu masu yawan da ba za su kammalu a kan lokaci ba.
Hanyoyin magance su su ne:(1) Samar da cikakkiyar hukuma mai zaman kanta ta dindindin wadda za ta kula da shirin. Misali EFCC, INEC da sauransu.
(2)Kawar da ra’ayoyi irin na siyasa tare da dorawa daga inda wani shugaban ya tsaya maimakon kawar da wanda aka tarar da saka bukatun talakawan kasar nan baki daya a gaba.
(3) Gina shirin bisa kishin kasa da sauran abubuwan da za su kawo cigaban kasa.
(4) Kakkabe sabon salon mulkin mallaka, na baba na daka gemu na waje ‘neo-colonialism’ ta hanyar kaurace wa Turawan Yamma da warware matsaloli a cikin gida Najeriya ba a ingila ba.
(5) Aiwatar da shirin yadda aka tsaro ba tare da an cire wani abu ba.
(6) Hukunta duk jami’in da aka samu da laifin kawo cikas ko karkata kudi ko kayan aikin zuwa wani wurin daban da zummar yin zagon kasa ga tattalin arzikin kas.
(7)kaddamar da shirin da manufar dora kasa kan hanyar ci gaba mai kyau ba kawai a yi ta yin biki ana sake wa ba. A karshe ina rokon gwamnatin tarayya da ta dubi wannan matsala ta rashin ingantaccen shirin cigaban kasa tare da maganceta don samun zaman lafiya da cigaban kasa mai ma’ana.
Hamza Ahmad Nasidi Alfindiki Kano, Tel: 08033975185, imel: hahmadnasidi@yahoo.com
Daga Hamza Ahmad Nasidi Alfindiki Kano
Assalamu alaikum! Jaridar Aminiya, a dade ana yi sai gaskiya jagorar jaridun kasar nan. Ina yi muku fatan alheri. EEE.....hakika Najeriya ta cika shekaru 50 da samun ‘yancin kai, amma har yanzu an kasa samun ingantacciyar hanyar cigaban kasa mai kyau, musamman a bangaren tattalin arzikin kasa,da na jama’ar da ke cikin kasa da na siyasa gaba daya.Saboda haka, na yi nazari da bincike kuma na gano cewa babu wata kasa wadda ta ci gaba a duniya sai da ta yi kwakkwaran tsari mai kyau na shirin cigabanta wato Debelopment planning,wanda da shi ne ake gano matsalolin da ke damun kasa,tare da daukar hanyar da ta fi dacewa don magancewa.
A kasar nan abin ya sha bam-ban, domin tsawon shekaru 50 da ake ikirari,an yi irin wadannan shirye-shirye da yawa. Na karshe-karshe shi ne BISION 2020 na marigayi Shugaba Umar Musa ‘Yar’adua, wanda aka gina shi a kan kawar da manyan matsaloli guda bakwai 7. Abin tambaya shi ne me ya sa shirin yake rushewa ko ake kasa aiwatar da shi yadda ya kamata ko aka tsara tun daga farko?
Dalilai ko matsalolin su ne:(1) Rashin cikakkiyar hukuma mai kula da shirin ta mai dorewa.
(2) Gina shirin bisa ra’ayoyi irin na siyasa ko wasu tsirarin mutane.
(3)Gina daukakin shirin a kan jari-hujja (capitalism) ko abin da ya shafi harkar kudi kawai.
(4)Tsoma bakin Turawan Yamma a cikin shirin (sabon salon tsarin mulkin mallaka).
(5)Saka bukatun talakawan kasa wurin tsarawa amma biyan bukatun masu ruwa da tsaki wurin aiwatarwa (yaudara).
(6) Kawo cikas da karkata salalar kudaden aiwatar da shirin zuwa wasu wuraren don samun riba daga wasu manyan jami’an masu aiwatar da shirin.
(7)Shigar da bukatu masu yawan da ba za su kammalu a kan lokaci ba.
Hanyoyin magance su su ne:(1) Samar da cikakkiyar hukuma mai zaman kanta ta dindindin wadda za ta kula da shirin. Misali EFCC, INEC da sauransu.
(2)Kawar da ra’ayoyi irin na siyasa tare da dorawa daga inda wani shugaban ya tsaya maimakon kawar da wanda aka tarar da saka bukatun talakawan kasar nan baki daya a gaba.
(3) Gina shirin bisa kishin kasa da sauran abubuwan da za su kawo cigaban kasa.
(4) Kakkabe sabon salon mulkin mallaka, na baba na daka gemu na waje ‘neo-colonialism’ ta hanyar kaurace wa Turawan Yamma da warware matsaloli a cikin gida Najeriya ba a ingila ba.
(5) Aiwatar da shirin yadda aka tsaro ba tare da an cire wani abu ba.
(6) Hukunta duk jami’in da aka samu da laifin kawo cikas ko karkata kudi ko kayan aikin zuwa wani wurin daban da zummar yin zagon kasa ga tattalin arzikin kas.
(7)kaddamar da shirin da manufar dora kasa kan hanyar ci gaba mai kyau ba kawai a yi ta yin biki ana sake wa ba. A karshe ina rokon gwamnatin tarayya da ta dubi wannan matsala ta rashin ingantaccen shirin cigaban kasa tare da maganceta don samun zaman lafiya da cigaban kasa mai ma’ana.
Hamza Ahmad Nasidi Alfindiki Kano, Tel: 08033975185, imel: hahmadnasidi@yahoo.com
**{Legacy activities, comments etc counter: 1192; topic series: 1; forum: MediaHausa; associated: 1- /*}