Topic: Allah ya jikan talakan kasar nan
Timeline: 2010-11-18 15:55:54
Allah ya jikan talakan kasar nan
A Rubuce Da Ishak Abdullahi Dan Rimi Bena
Anya gwamnatin kasar nan tana kaunar talakawa kuwa? Dubi yadda gwamnatin tarayya ta ware makudan kudade, wuri na gugar wuri har Naira biliyan goma don yin bikin cika shekara hamsin da samun ‘yancin mulkin kan Najeriya.
Ta bar talakawa cikin halin kaka-nika-yi.Ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi amfani da wadannan kudaden wajen inganta rayuwar al’ummarta, ba kashe su a wurin yini biki na rana daya ba. Misali akwai bukatar gwamnatin ta magance matsalar rashin aikin yi a tsakanin al’ummar kasar nan musamman ma matasa. Ga matsalar rashin tsaro da ta rashin magunguna a asibitoci, da rashin wadatacciyar wutar lantarki ga al’ummar kasa; ga karancin abinci da ya addabi al’umma saboda fatara da ta yi katutu ga ‘yan kasa duk suna da bukatar kulawa ta musamman.
Haba jama’a, a dubi wannan al’amari da idon basira. Ta yaya za a ce an ajiye duk irin wadannan matsaloli da na lissafa da wadansunsu a gefe? Idan an yi Magana sai a ce babu kudin da za a magance su, amma sai abin neman suna ya zo sannan ne za a fito da kudi. Allah Ya jikan talakan kasar nan, ba don ya mutu ba, sai don rashin kulawa da ba ya samu daga wurin gwamnati a matsayinsa na dan kasa.Idan aka yi la’akari da bikin rana daya gwamnatin Najeriya ta ware Naira biliyan goma don yin wannan bikin cikar kasar shekaru hamsin( 50) idan dai har gwamnatin da waccan niyyar ta ware wadancan kudaden to lallai ba a yi wa talaka adalci ba.
Allah Ya jikan mazan jiya, kamar su Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da Sa Abubakar Tafawa Balewa da Nnamdi Azikiwe wadanda suka yi tsaye don ganin kasar Najeriya ta samu ‘yancin kai daga Turawan Ingila. Na tabbata idan da suna nan da rai, ko su dawo su ga irin barnar da shugabannin wannan zamani ke yi da sun ci gaba da yi musu tofin Allah-tsine. Don ba haka suka yi nasu mulkin ba. Ya kamata a shiga masallatai da majami’u don yin addu’a Allah Ya ba kasar nan zaman lafiya da cigaban tattalin arziki don yin haka shi ne mafita, ba kwashe biliyoyin Naira a bikin rana daya ba.
Allah Ya jikan talakan Najeriya ba don ya mutu ba, sai don rashin kulawa da gwamnatin ke nuna masa. A yau an wayi gari an ware zunzurutun Naira biliyan 21 domin sayen jiragen sama na hawan shugaban kasa kawai duk da yake gwamnatin ta ware Naira biliyan goma domin bikin ranar samun ‘yancin kai a kasar.Shin a haka za a samu ci gaba, talaka na cikin ukuba da rashin cin yau balle na gobe? Allah Ka ba mu shugabanni masu adalci da son kaunar talaka, ba masu kaunar son ransu kawai ba. Allah Ka kara masu son talaka a zuciyarsu, ba a baki ba, amin.
ISHAK ABDULLAHI DAN RIMI BENA 07033076310.
**{Legacy activities, comments etc counter: 778; topic series: 6; forum: MediaHausa; associated: 6- /*}