Topic: Kalubalenku Sarakunan Arewa
Timeline: 2010-11-18 15:59:46
Kalubalenku Sarakunan Arewa
A Rubuce Da Bilal S. Tangaza
Hausawa ko kuma masu iya magana na cewa, idan ka ga gemun dan uwanka ya kama da wuta to ka shafa wa naka ruwa. Wannan haka yake idan aka yi la’akari da abin da yake faruwa a bangaren masarautun kasar nan.
Ya ’yan uwana talakawan Najeriya a wannan karon da yardar Allah, ina son yin tsokaci ne dangane da iyayenmu sarakunan Arewa. Ba zan taba mantawa da wani abu da ya faru ba, kimanin shekara 20 tun lokacin ina makarantar firamare wajen shekarar 1988.
Na ankara da cewa ana wulakanta sarakunan Arewa. Tun kafin a haife ni ake yi musu wulakanci. Wanda na fara sani shi ne, gwamnatin mulkin soja ta Babangida ta dankara mana Sarkin musulmi wanda ranta ke so, bayan ’yan shekaru da gwamnati marigayi Janar Abacha ta zo sai ta cire Sultan Dasuki, ta nada marigayi Maccido a shekarar 1996. Wannan ke nan.
Sarakunan Arewa sun fuskanci matsaloli da dama,tun lokacin gwamnatin NPC ta yi makamancin wannan a inda ta saukar da mai martaba San Kano Sa Muhammadu Sanusi, ta maye gurbinsa da marigayi Muhammadu Inuwa, amma an nuna ma jama’a cewa wai radin kansa ya yi murabus. A kashin gaskiya ba haka ba ne. An so a yi amfani da shi ne don cimma wani buri na daban, amma Allah Ya sa yana da kyakkyawar niyya ga al’ummar jiharsa ta Kano. Daga karshe ya bar musu kayansu cikin mutunci saboda a lokacin siyasa ta shiga cikin masarauta da sarakunan Arewa.
Haka nan kuma, an sauke sarki a Jihar Kebbi Mustapha Jakolo daga kan karagar mulki, aka maye gurbinsa. da Iliyasu Bashar. Dalilai da dama suka sa aka sauke shi daga kan karagar mulki. Kadan daga cikinsu su ne, wai ba ya biyayya ga gwamnati. Ya za a yi ya bar darajar gidan Shehu Usmanu danfodiyo ya bi ta wadanda ba su san darajar gidan ba. Sannan kuma a wannan lokacin gwamnan jihar ya kasa sarrafa shi yanda ransa ke so; ga kuma maganar su Manjo Hamza Almustapha, wanda yana daya daga cikin manyan Sarakunan Arewa da ya yi iya yinsa don ganin cewa an sako su. Wadannan dalilan da wasunsu su ne suka yi awon gaba da rawaninsa.
Haka abin yake a Jihar Adamawa, inda gwamnatin jihar ta saukar da Sarkin Bachama daga kan karagar mulki, sannan ta maye gurbinsa da wanda ranta ke so. Hambararren Sarkin aka ba shi masauki a fadar gwamnatin jihar da ke Yola, sannan kuma daga baya labari ya nuna cewa wai an sace shi, ko ina aka kai shi oho.
Idan ba a manta ba, a jihata ta Sakkwato Gwamna Wamakko ya saukar da wasu sarakuna ciki har da kanen mahaifinsa, Barade Abubakar Jabbi, inda ya maye gurbinsa da wansa Salihu Barade. Dalili shi ne wai ba ya yin jam’iyyar siyasar da gwamna yake yi. Don Allah dan uwa in banda kwadayi irin na sarakuna, me ya kai su shiga harkokin siyasa? Wanda bai kai ku matsayi ba, ya dawo yana wulakanta ku daga karshe.
Sannan kuma, a Jihar Zamfara kwanan bayan nan gwamnan Jihar ya saukar da yayan tsohon gwamnan jihar, wato Sarkin Burmin Bakura daga kan karagar mulki, a bisa zarge-zargen cewa wai al’ummar masarautar ne suka kai kukansu ga gwamnatin jihar bisa dalilin cewa Sarkin ba ya zama a yankin sai ranakun Alhamis da Jumu’a, sannan kuma ba ya girmama gwamnatin jihar, sannan ya kashe makudan kudaden tafiyar da masarautar ba bisa ka’ida ba, da sauran zarge-zarge da dama.
Duk wadannan dalilan ba su ne kashin bayan hakan ba. Dalili shi ne, muguwar gabar siyasar da ke tsakanin gwanna mai ci yanzu da tsohon mai gidansa Sanata Yarima. Wannan dalilin ne ya shafi gidan su Yarima, har aka saukar da yayansa daga kan karagar mulki..
Bayan haka wai ma don Allah mene ne dalilin da yasa ’yan siyasa suke wulakanta iyayenmu sarakuna? Musamman na Arewa. Hausawa suna cewa “idan an yi ta barawo, sai a yi ta mai bin sawunsa”, su ma Sarakunan suna da nasu laifin. Kwadayin tsiya ne da su. Don Allah mene ne ya kai sarki da hakimi ko dagaci da Maiunguwa zuwa ofisoshin gwamnati? Gaskiya ne duk mai mulkin da ya ga Sarakuna suna neman alfarma a gurinsa, ya zama dole ya juya su son ransa.
Abin kunya da bakin ciki shi ne, sarki za ka samu yana karakaina a ofishin Ciyaman na karamar hukuma, saboda mugun kwadayin da ya yi yawa, ba haka Iyayen da kakanninku suka yi ba. Don Allah mene ne ya sa kuke yin haka? Magana ta gaskiya sarakunan Arewa ba sa girmama rawaninsu, sun wulakanta kawunansu a wajen ‘yan siyasa.
karamin misali shi ne, a lokacin mulkin Obasanjo Sarakunan Arewa sun yi taro don ganin an sako su Manjo Hamza Almustapha, amma don suna ’yan jeka na yi ka, gwamnoninsu na wannan lokacin suka hana su zuwa fadar shugaban kasa domin saka baki. Gwamnoni suka yi musu barazana da cewa duk wanda ya kuskura ya je to bakin rawaninsa. A lokacin, Sarkin Gwandu kawai ya yi kokari amma daga baya ya rasa rawaninsa. Wasu ba ma rawanin ba har duniyar sun bari, da ma iyakacin duniyar ke nan, daga kin gaskiya sai bata.
A daya bangaren abin takaici da tashin hankali shi ne, Malaman Addini sun bi sahun Sarakuna. A gurin yin gogayya da masu mulki, ba za ka iya bambancewa ba tsakanin malami da kuma sarki a gurin bukukuwa da yawon neman alfarma a ofisoshin masu mulki. Sun manta da matsayin da suke da shi a cikin al’umma. Kamata ya yi a ce Sarki shi ne yake bayar da Sallah a garinsa, amma yana iya nada Liman.
Ya ’yanuwana talakawan Najeriya shin haka za mu sa idanu muna kallon Sarakunanmu suna zubar mana da mutunci a idanun duniya? Yanzu duk fadin Arewa ba wani Sarki wanda yake da kima a idon masu mulki? Sai ka ga Sarki sukutum yana neman wani abu a gurin wani dan siyasa ko mai rike da mukami a gwamnatin siyasa da sunan yana son yin tafiya wani guri. Kullum Sarakunanmu ba abin da suke kokarin yi sai dai a ba su matsayi a cikin kundin tsarin mulkin kasa. Ko ka ga Sarki mai daraja ta daya duk ranar Sallah shi zai kai gaisuwar Sallah har fadar gwamnati, maimakon gwamna ne ya kamata ya kai masa gaisuwar ban girma da kuma barka da Sallah.
Daga karshe, ina kira da babbar murya ga Iyayenmu Sarakunan Arewa cewa, don Allah su guji kwadayi su daina saka kawunansu cikin siyasa da sha’anin mulki. Saboda ku ake wulakantawa da mutuncinku da na gidajenku. Allah(SWT) Ya ba ku ikon gyarawa amin. Ni, a ganina sarki uban kowa ne a cikin kasarsa, ba daliln da zai sa a ce sai an sanya shi cikin kundin tsarin mulki don ya yi wani abu. A matsayina na sarki, ai kai zaka zo min,ba ni zan je maka ba, sai dai in ba ka lafiya, misali Allah Ya kyauta.
Bilal Bello S. Tangaza
Sakataren Kungiyar Muryar Talakawan Nijeriya Jihar Sokoto, 070’36354507
bbstangaza@yahoo.com
**{Legacy activities, comments etc counter: 2476; topic series: 4; forum: MediaHausa; legacy score: 10; legacy ratings: 2; rating_ip: ***.*14.31.188; associated: 4- /*}