Topic: Sojoji Da ’Yan Siyasa Da ’Yan Boko Sun Ci Amanarmu
Timeline: 2010-11-18 16:02:45
Sojoji Da ’Yan Siyasa Da ’Yan Boko Sun Ci Amanarmu
A Rubuce Da Ibrahim Dattijo
Sojoji da ’yan siyasa da ’yan boko sun ci amanarmu. Turawan mulkin mallaka sun mallaki kasar nan tun shekara ta 1901 har zuwa lokacin da aka hada bangarorin uku na kasar nan a shekara ta 1914. A shekara ta 1960 da aka sami ’yancin kai, mulki ya koma hannun ’yan kasa.
Talakan Najeriya ya ga mulki iri daban-daban.
Kasar ta samu shugabannin farko masu tsoron Allah da kishin kasa, ba su mayar da abin duniya komai ba. Allah Ya jikan Sa Abubakar Tafawa balewa da Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da sauran ’yan Arewa masu kishin kasa da sauran mutanen kudanci da yammaci. Dokta Nnamdi Azikiwe da Chif Obafemi Awolawo wadannan mutane sun so al’ummarsu fiye da kansu. Bayan gushewar ’yan kishin kasa, sai gwamnatin soja karkashin Janar Aguiyi Ironsi suka hambarar da gwamnatin farar hula.
Tun daga wancan lokaci aka shiga nuna bakin mulki irin na kama karya a kasar nan. Cikin wadannan shekaru, babu wani abu da za ka iya bugun kirji ka ce mun same shi. Idan ka ji mutum na cewa an ci gaba, ka tabbata shi ne ya ci gaba, ya bar kasar a baya. Duk mutum mai hankali, wanda ya san me ake nufi da cigaban kasa, sai dai ya fadi son zuciyarsa, don Najeriya ba ta cigaba ba. Idan kuwa a matsayin kasa daya ake bikin tuna ranar da kasar ta zama daya ta kai shekara hamsin, wannan mun yarda, abin tunawa ne tunda muna raye mun ga lokacin da kasarmu ta kai rabin karni,duk kuwa da irin munanan tashen-tashe hankula da aka rika samu a bangarori daban-daban na kasar nan.
Bayan wannan, sai cin hanci da ya zama jini da tsoka; ga hanyoyinmu sun zama kaburbura; asibitocinmu ba likitoci ga ba magunguna, rashin ingattaccen makamashi ya kara haifar wa matasa rashin aikin yi. Kamfanoninmu sun mutu, musamman ma a Arewacin Najeriya sannan hanyoyin sufuri sun mutu.
Harkar noma kuwa, duk shekara bayan damina ta kusa karewa ake kawo taki, ba a maganar malaman gona. Maganar tsaro shi ma abu ne da ba ka iya nuna inda yake da tsaro a kasar. A hedikwatar gwamnatin kasar, ranar murnar ’yancin kai, sai da aka samu wasu ’yan dadi-bam suka tarwatsa bama-bamai a daidai lokacin bikin, kuma suka fito suke gaya wa duniya cewa su ne suka yi.
Talakawan kasar, karatun zamani yana daf da ya fi karfin ’ya’yansu don tsadar rayuwa da rashin kudi na daukar dawainiyar ba su ilimin. Matasa kuwa sun zama ’yan-bangar siyasa da sara-suka da ’yan jari-hujja suka yi wa kasar babakere. Talaka ba shi da damar tsayawa takarar wata kujera lokacin zabe. Haka kuma ko talaka ya zabi wanda yake kyautata zaton zai yi masa aiki ba za a ba shi ba, masu mulki da masu hannu da shuni kawai ke more rayuwarsu ba ruwansu da wani ya sami sauki.
Muna fatan kafin kasar ta kai ga cimma muradun karni, za a samu canjin shugabanni masu tsoron Allah. Mu talakawa mu ji tsoran Allah mu tuna cewa za mu mutu, shugabanci dama ce ta shiga aljanna matukar aka yi shi ta yadda Allah (S W T) Ya bayyana mana ta hannun manzonSa manzon tsira Annabi Muhammad (S.A.W.) Mu cire son zuciya mu so wa ’yan uwanmu abin da muke so wa kanmu. Duniya ba madauwama ba ce. Allah Ya shirye mu Ya zaunar da kasarmu lafiya, Ya ba mu shuwagabanni masu son mu, ba wadanda muke so ba, amin.
Kwamared Ibrahim Dattijo mai nazari kan al’amuran yau da kullun, Unguwar Rimi Kaduna.-08099576675 ko 08025756675. Imel sawune2@yahoo.com 08025756675,imel,sawune2@yahoo. 08025756675,imel,sawune2@yahoo.
Jonathan da abokan hamayya akan sikelin hankali
Daga Sabo Haruna
Hausawa su kan ce wai zakaran da Allah Ya nufa da cara, ko ana muzuru ana shaho, sai ya yi. A wani karon kuma, akan ce wai, mai rabon ganin badi, ko ana dakawa a turmi sai ya gani. Hausawa ke nan da karin maganganunsu.Na yi wannan tsokaci ne domin ganin irin salon siyasar da ake takawa a Nijeriya a yau. Shin, anya akwai Allah a cikin lamarin kuwa? Da farko, ‘yan Nijeriya suna mamakin fitowa domin takarar shugaban kasa da wadansu shugabanni na da, suka yi a yanzu.
Alal misali, masu karatun jarida da dama sun yi wannan tambayar kafin ni: Shin, wai me Janar Babangida ya manta bai dauka ba ne a fadar gwamnatin Aso da ke Abuja, wadda kuma ya ke son ya koma ya dauka? Haka zalika, masu rubutu da dama su na mamakin wai, mene ne tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ke so ya ci, wanda bai ci a fadar gwamnatin Aso ba? Haba jama’a, don Allah mu fara tsoron Allahn da Ya halicce mu.
Dukkan abin da Janar Babaginda ya yi a kan karagar milki a tsakanin 1985 zuwa1993, bayyananne ne. Marubuta tarihi da masu sharhin yau-da-kullum, tuni sun yi Allah-wadai da yi wa Dimukradiyya zagon kasa da tsohon Janar din ya saka ya bar gidan gwamnati ba shiri.
A nan muna magana ne a kan zaben da ’yan Nijeriya suka yi wa Cif Moshood Abiola, amma Janar din ya rusa da gangan. Idan banda rashin akida a siyasar yau, yaya Babangida zai fito neman zaben shugaban kasar Nijeriya, bayan ya kekasa kasa, ya ki neman gafarar ’yan Nijeriya, duk da hakkin da yake kansa na zafin rana da miliyoyin ’yan Nijeriya su ka sha domin zaben Cif Abiola? Haka kuma, me Turakin Adamawa Atiku Abubakar zai ce wa ‘yan Nijeriya, ganin irin yadda aka yi ta damawa da shi, a zamanin Obasanjo, kafin su yi hannun riga da juna? Maganar gaskiya ita ce yadda Allah Yake yi wa bayinSa hisabi, tun a duniya, kafin ma a je lahira. Surorin Al’kur’ani kamar a Izazul sun nuna a karo da dama cewa abin da mutum ya shuka, shi zai girba, idan hairi, hairin, idan kuma sharri, sharrin. Wannan ayar Allah ma ta ishi dukkan shugabanni da suka shimfida mulkin zalunci, rashin adalci, rashawa da al gus. kaddara ta na daga cikin shika-shikan addinin Musulunci, kuma duk wanda bai yarda da }addarar Allah ba, to ya kuka da kansa. Tuni kuwa, siyasar }abilanci da addini ta gundiri mutane, kuma suka gane cewa siyasar koma-baya ce. Siyasa ce ta ragwage, wadanda ba su yi imani da kawunansu ba.
Koda yake mutane ba su da tawakkali ballantana hangen nesa, amma duk mai sauran tunani da imani bai dace ya yi jayayya da mulkin shugaba Goodluck Jonathan ba. Allah mahalacci ne Ya yi Musulmi, kuma Ya yi kirista. Shi ne kuma Yake da ran kowa a hannunSa. Sha’awata ga shugaba Goodluck Jonathan ta wanzu ne daga irin bishara, da misalin da Sarki Allah ya nuna game da shi.
Da farko, wannan dan taliki mataimakin gwamna ne, amma Allah Ya canza lamarinJiharsa ta Bayelsa, yadda ya kasance gwamna mai gafaka, ba tare da ya tsaya a zabe kamar kowa ba. Dadin dadawa, haka ma ya kasance mataimakin shugaban kasa, kuma Allah Ya yi ikonsa, yayin da ya kasance cikakken shugaban kasa, bayan rasuwar shugaba ’Yar’Adua.
Idan aka bi salsala, da yadda Goodluck yake kara samin karbuwa, nasara da bunkasa, to lallai mai zurfin tunani zai gane cewa mai yiwuwa Allah ne Yake son Ya kara koyar da mu darasin kaddara ta riga fata. Haka zalika, zakaran da Allah Ya nufa da cara, ko ana muzuru, ana shaho, sai ya yi.
Sabo Haruna ya rubuto daga Anguwar Sarki, Kaduna
**{Legacy activities, comments etc counter: 3367; topic series: 1; forum: MediaHausa; legacy score: 4; legacy ratings: 1; rating_ip: ***.*14.6.229; associated: 1- /*}