Topic: Abin Da Ya Kamata A Yi Kafin Gudanar Da Zabe: Me ya sa Arewa ke neman mantawa da Atiku?
Timeline: 2010-11-18 16:07:30
]Abin Da Ya Kamata A Yi Kafin Gudanar Da Zabe: Me ya sa Arewa ke neman mantawa da Atiku?
A Rubuce Da Alhaji Abdulkarim Dayyabu
Daga Jamhuriyya ta Biyu zuwa yanzu ba abin da ake yi in ban da cin zarafin kasa da raina wayon jama’arta. Wadansu ’yan kalilan suna tafka mummunar almundahana da sace dukiyar kasa. Wannan ya sa ake ta ci gaba da tafka irin wannan barna saboda gaza samun sauyi irin na Rawlings na Ghana a Najeriya. kokarin da Buhari ya yi na kawo gyara ya hadu da cikas din miyagun kasa wadanda suka kame ragamar mulki bayan sun kawar da shi.
Wannan ya jefa kasar nan a halin ni-’yasu. kasar ta zama daular beraye da gafiyoyi ba tare da an sami wani yunkuri na kawo gyara ba. Duk da gagarumar sata da almundahanar da ake tafkawa, ba wanda aka hukunta. kokarin da Nuhu Ribadu ya yi na firgitarwa da hukunta barayin Najeriya ya hadu da cikas. Yau an yi shiru ba wani motsi na dakile wannan muguwar harka. Sai dai abin tambaya shi ne haka za mu ci gaba da tafiya?
Zarge-zargen da ake yi kan batutuwan almundahana ya wajaba a bincike su saboda muhimmancin da suke da shi.
i) Kowa ya san ba dukkan tsare-tsaren gwamnati ake aiwatarwa ba, ba ya ga wadanda za su amfani wani rukunin mutanen kasa da suke amfani da fada-a-ji ko dukiyarsu ko mukamansu. A lokuta da dama sukan yi kafar ungulu ga ayyukan da za su amfani jama’ar kasa.
ii) A kafa wata hukuma ta musamman da za ta kwato dukiyar da aka sace kamar yadda aka kafa hukumar Kula da Rarar Man Fetur (PTF), wadda za ta sarrafa wannan dukiya da aka kwato wajen farfado da cibiyoyi da hukumomin gwamnati da suka durkushe, kamar Kamfanin Jiragen Sama na Najeriya da Kamfanin Jiragen kasa na Najeriya da Kamfanin Sadarwa na Najeriya da sauransu.
iii) Matsalar Mista James Ibori abin misali ne na irin abin da wadancan daidaikun mutane mahandama za su iya yi. Sun mayar da kansu gwamnati. Kuma saboda wadannan dalilai muke bayar da shawarar a kafa wata hukuma ta musamman (ba ’yan sanda da EFCC ba), ta binciki abubuwa masu zuwa domin cimma wannan manufa.
Sassan da za a bincika su ne:
i) Wani marubuci Ba’amurke mai suna Jeffrey Robinson a cikin littafinsa mai suna The Sink, ya ce: “Daga cikin Dala biliyan 120 da miyagun ’yan siyasa (ko shugabanni) suka sace daga baitumalin Najeriya zuwa kasashen Turai, ana zargin Dala biliyan 20 sun tafi asusun Janar Ibrahim Babangida ne da ya yi mulki tsakanin 1985 zuwa 1993. Sannan duniya da wasu majiyoyi na kasa da kasa sun bayyana cewa ya yi rub-da-ciki kan jimillar Dala biliyan 35 na al’ummar Najeriya. Akwai bukatar a yi cikakken bincike kan wannan zargi, kuma a kwato dukkan kudaden, idan zargin ya tabbata gaskiya, idan kuma ba gaskiya ba ne, mu huta da jin wannan labari mai bakanta rai.
ii) A binciki batun rarar man fetur na Dala biliyan 12 da Dala miliyan 200.
iii) A bincki zargin almundahanar da ke yi wa marigayi Janar Abacha.
ib) A binciki kudaden ajiyar waje da ake zargin Janar Abdulsalami ya wawure.
b) A binciki badakalar Halliburton.
bi) A binciki zurmuken kwangilar gyara hanyoyi na baya-bayan nan, musamman na Abuja.
bii) A binciki muna-munar da ake zargin Majalisar kasa da ita, inda ake zargin ’yan majalisar da tsara wa kansu albashin da ya shallake hankali da mahaukatan alawus-alawus da kirkiro ayyuka don amfanin kawunansu. Idan aka gudanar da wannan bincike akalla ’yan Najeriya za su san an kama hanyar gyara kasa. Amma a yi shiru al’amura suna tafiya ba daidai ba, abu ne da ke dada jefa kasar nan a ramin halaka.
A kafa gwamnatin rikon kwarya.
Bayan wadannan al’amura da muka ambata sun samu, a fili yake cewa a yanzu kasar nan tana tsaka mai wuya tare da fuskantar matsalolin barazana ga lafiyarta. Najeriya yanzu kamar mutum marar lafiya take, tana bukatar a kula da lafiyarta kafin a yi batun komai.
Don haka muna kira da babbar murya ga shugaban kasa da dukkan hukumomin da suka wajaba, su tsara wani kuduri na kiran taron kasa da zai yanke shawara kan abubuwa masu zuwa:
a. dage zabubbukan shekarar 2011.
b. A kara wa’adin gwamnati mai ci da shekara daya, ta yadda za a gudanar da shawarwarin da muka bayar a sama.
c. A kafa gwamnatin rikon kwarya da za ta shirya zabe ingantacce, kuma a tabbatar duk wanda zai tsaya takara ya sauka daga mukaminsa akalla wata uku ko shida kafin zabe, tun daga kan shugaban kasa zuwa gwamnoni da ’yan majalisa da shugabannin kananan hukumomi da makamantansu. Idan haka ta samu akwai kyakkyawan zaton za a iya gudanar da karbabben zabe marar magudi a zabe mai zuwa.
Amma yadda al’amura suke tafiya a yanzu, da yadda wadanda suke kan gadon mulki suke kokarin sake komawa ta kowane hali, alama ce da ke nuna ba za a sami zabe na kwarai a badi ba.
kasar nan tana kan siradi a yanzu, kuma akwai bukatar shugabanni da al’ummar kasa su tuna kasar tana gaba da kowa. Don haka wajibi ne kowa da kowa ya yi abin da ya wajaba domin kare bukatun kasar da jama’arta fiye da bukatu na kashin kai. Idan kuma muka ki, muka fifita bukatunmu na kashin kai, a kan bukatun kasa, ina ji mana tsoron yadda kasar nan za ta kasance a nan gaba.
Kada a jefa kasar nan a cikin rikicin da zai kara wa talaka da ba ya morar wani abin kirki daga kasar nan a cikin wani kangin wahala. Kada a jefa kasar nan a cikin rikicin da zai wargaza ta saboda son zuciyar wadansu kalilan din ’ya’yanta! Kada a jefa makomar ’ya’ya da jikokinmu a cikin wani kunci baya ga kuncin da muke ciki a yanzu. Allah ba Zai yafe mana ba, idan muka kara sanya jama’ar kasar nan a cikin wata wahala.
Muna fata idan kunne ya ji, jiki ya tsira.
Abdulkarim dayyabu
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya,
Lamba 11 Beirut Road,
Kano.
08023106666, 08060116666, 064983333.
Imel: jdaiyabu@yahoo.com
Me ya sa Arewa ke neman mantawa da Atiku?
Daga Bashir Garba Na’ibawa
Na kasance mai karanta jaridun Hausa. Lokuta da dama na kan yi tsallaken karantawa, tun daga rikita-rikitar harkar siyasar “Tazarce” da Obasanjo ya nemi ya yi, ban sake bari jaridun suna wuce ni ba. Kirdadon da na yi na fahimci cewa kafafu ko tayoyin taragon jirgin dimokuradiyyar Najeriya sun fara karkacewa, tun bayan amanar tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ci a zamanin da su ke kan mulki.
Zan iya tunawa a watan Nuwambar shekara ta 1999 zawa 2000, gwamnonin Arewa da daukacin shugabannin kananan Hukumominsu da sauran masu ruwa da tsakin siyasa musamman na PDP, sun shirya wani gangami a Kaduna, a fakaice taron ya na nufin wani gangami ne na yi wa Atiku mubayi’a a matsayinsa na jigo, jagora kuma jagaba a daukacin tafiyar siyasar Arewacin kasar nan.
Haka siyasar Arewa ta tafi a lokacin ana yi wa Atiku kallon wani bangon jingina ga ‘yan siyasar Arewa. Ko ba komai a lokacin shi ne dan Arewa mai rike da mafi girman mukami a kasa. Ko shakka babu kowa ya san kashin bayan Turakin Adamawa ya yi kwarin goya duk wani nauyin da za a jibga masa.
An wayi gari, ba a maganar kowa a Arewa sai Atiku. Daga ’yan siyasa, manyan ’yan kasuwa, manyan ma’aikata, kai hatta Sarakunan gargajiya kowa tagomashin Atiku ya ke nema. Yadda sunansa ya yi nisa a ko’ina haka alherinsa da tagomashinsa ya mamaye dukkan Arewacin kasar nan. Yadda ’yan bokon Arewa suka ci gajiyar kwangiloli a karkashin hukumar tara rarar kudin man fetur ta PTDF, haka a zamanin mulkin Janar Abacha, ’yan siyasa suka rika jingina a gadon bayan Atiku,
Zubin gwamnonin farko da na biyu na mulkin Obasanjo wadanda Obasanjo ya rika yi wa barazanar warware musu rawanin sarauta, su ne su ka fara juya wa Atiku baya don su na tsoron Obasanjo, akokarin bi ta kan gwamnonin don dakushe kaifin makaman siyasar Atiku da ya ga sun yi, ganin yadda ya yi kememe ya ki yarda da shirin shedancin Obasanjo na tazarce.
A nan sai mu dawo mu tambayi gwamnonin wancan lokacin, ina karyar kishin Arewar da su ke yi da kishin Atiku jagoransu a lokacin? Har su ka bari Obasanjo ya maida shi saniyar ware saboda ya ki amincewa da tazarce? Idan Atiku ya ki yarda da tazarce don kamar yadda ake cewa don ya na kwadayin kujerar Obasanjo ne, shin a nan wa ya fi cancanta a Arewa ya gaji Obasanjo a loakcin idan har dan Arewa ne za a tsaida takara? Ko laifi ne idan mataimakin shugaban kasa ya nemi kujerar shugaban kasa? Me ya sa Arewa ba ta botsare wa Obasanjo ba yayin da ya rika kuntata wa Atiku? Me ya hana algunguman gwamnati yi wa Obasanjo tawaye ganin yadda ya kashe Arewa kuma ya ke neman kashe wa Arewar Atikun ta?
Arewa ta yi sake ta na neman rasa jan-gwarzo wanda zai iya rike mata tutar siyasar zamantakewar kasa. Na yarda da manufofin Atiku don ya nuna a fili cewa shi jan-gwarzo ne. Dubi yadda ya rika tandara Obasanjo da kasa a kotu har sau shida, duk da cewa Obasanjon na kan kujerar mulki, shi kadai ya rika yaki da Obasanjo. Da taimakon harzikin jami’in yada labaransa, Malam Garba Shehu, lokacin da aka uzura wa Atiku ya fita daga gidansa na fadar shugaban kasa. Malam Garba ya yi ta fuskantar barazarana da kuntatawa daga hannun jami’an tsaro.
Jimiri da jajircewar Atiku ta kai shi ga kwatar jihohi biyu a zaben gwamnoni na shekara ta 2007, da kuma ’yar manuniya ta nuna cewa shi ne ya ci jihar Ekiti bayan wadancan jihohin Legas da Edo. Bayan wannan, kowa ya ga yadda shari’ar zaben shugaban kasa ta kaya inda wasu alkalan kotun koli ba su yarda da cewa PDP ta yi rinjaye a zaben ba, don an yi amfnai da la’ananniyar hukumar zaben lokacin ta hana Atiku fara kamfen har sai da wuri ya kure. Wannan kuwa ba ya cikin adalcin dimokuradiyya kwata-kwata. Kuma ya saba wa ka’idojin tsayawa takara, don an hana Atiku shiga lungunan kasar nan kamar yadda dan takarar PDP wanda Obasanjo ya dora, marigayi Umaru ’Yar’Aduwa ya karade ko’ina.
Kada mu kai ta da nisa, jan hankalin da na ke so na nuna a nan shi ne, duk wata rikita-rikita da tagumin da Arewa ke yi a siyasar yanzu, ya samo asali ne daga butulcin da aka yi wa Akitu. kiri-kiri aka yi masa kora da hali, ya fice daga PDP duk da su ne su ka raine ta har aka jawo Obasanjo ciki. Aka kware wa Atiku baya, aka zura wa Obasanjo ido ya dauko wanda ransa ke so, ba tare da ya shawarci kowa ba, ya tsaida shi takara. ’Yan Arewa na gani, su ka ki cewa komai saboda idonsu ya rufe.
Ga shi yanzu an bar su da neman mafita. To me zai hana yanzu tunda Atiku ya koma PDP, ’yan Arewar da ke adawa da Jonathan su je su ba shi hakuri, su ba shi tikitin tsaya wa jam’iyyar takarar shugabancin kasa.
Na tabbata idan aka yi haka, Atiku ya zama dan takarar da ya cancanta ya kutsa Kudancin kasar nan a karbe shi hannu bibiyu, don tasirinsa ba a Arewa kadai ba ne. Shi cikakken dan Nijeriya ne.
Na yi nazarin kudirorin Atiku wadanda ke cikin daftarin da ya buga, babu fannin da bai tabo ba,ilimi da shari’a da samar da ayyuka da farfado da masana’antu, bin ka’ida samar da rowan sha da wutar lantarki da inganta hanyoyin sufuri da tattalin arzikin kasa zai farfado duk Atiku ya yi bayanin su dalla-dalla. Yadda Atiku ke da haushin lalata Arewa da Obasanjo ya yi, shi ne ya kamata mu sa a gaba don ya farfado da kasar baki daya. Zabi biyu ne mu ke da shi ko Atiku ko mu sake fadawa ’yar gidan jiya.
Bashir Garba ya rubuto ne daga Unguwar Na’ibawa, Jihar Kano
**{Legacy activities, comments etc counter: 695; topic series: 3; forum: MediaHausa; associated: 3- /*}