Topic: Bijirewar Ganin Wata: Babbar Barazana Ga Hadin Kan Musulmin Najeriya
Timeline: 2012-03-27 18:14:09
Bijirewar Ganin Wata: Babbar Barazana Ga Hadin Kan Musulmin Najeriya
A Rubuce Da Muhammad Sani Isa
Kamar yadda aka saba, Azumin watan Ramadan, kowace shekara, yakan zo da gardamar wace rana ta kamata a tashi da azumi? Shin a yarda da ranar da Mai Alfarma Sarkin Musumi ya tsayar; ko za a yi watsi da ita, a riga shi dauka, ko a ki farawa a ranar da ya sanar, a dauka kashegari ko ma bayan kwana 2 ko 3?
Bana an samu cewa, kusan kama azumi ya rabu gida biyu ne kawai a madadin gida 4 ko 5 da aka saba. A bangare daya, akwai ‘Yan Izala bangaren Jos, wadanda suka yi watsi da sanarwar Sarki Musulmi, suka yi riga-malam-masallaci, suka fara ranar Lahadi, 31 ga watan Yuli, 2011; haka nan wani bangaren kasar Gwandu ma sun ki bin umurnin Sarkin Musulmi. A daya gefen kuma, akwai mafiya yawan al’ummar musulmi, ’yan sami’ina-wa-ada’ana, masu bin umurni, sun fara ranar da Sarkin Musuli ya sanar, ranar 1 ga watan Agusta, 2011.
Dangane da wani bangaren kasar Gwadu, wadanda su ma suka bi sahun Izalar Jos, suka fara azumi da kwana daya kafin ranar da Sarkin Musulmi ya tsayar, hujjarsu ita ce: wadanda suka ce sun ga watan, sun rantse da Alkur’ani cewa sun gani. Don haka tilas a gaskata su, kuma tilas a yi aiki da ganinsu. Sun mance cewa rantsuwa da Alkur’ani ba ta mayar da karya gaskiya, musamman a halin da aka tabbatar da cewa, abin da aka rantse a kansa kwata-kwata ba zai yiwu ba, kuma karya ne. Misali da’awar ganin wata a halin da aka san ba a riga an haifi watan ba, ko kuma jim kadan bayan haihuwarsa; yana dan mitsitsi.
Ana watsi ko kin karbar rantsuwar ganin wata a ranar da wata ya fadi kafin faduwar rana; ko a ranar da ba zai taba yiwuwa a ga wata ba, domin ba a riga an haife shi ba; ko domin wani dalilin da zai hana a ga watan. Yin watsi da irin wannan rantsuwar, ba ya nufin watsi da fadar Manzo (SAW) cewa: ‘ku dauki azumi in an gan shi, ku sha in an gan shi’, domin a hakikanin gaskiya, ba watan aka gani ba.
Mafiya yawan al’umma, wadanda suka dauki azumi ranar Litinin, 1 ga Agusta 2011, mabiya umurnin Sarkin Musulmi, sun dauka ne domin, a ka’idar Shari’a, ana daukar azumi ne kawai a ranar da shugaba ya tabbatar kuma ya ayyana, gami da cewa, ranar daukar azumi ta hakika, ita ce ranar da mafiya jama’a suka dauka bisa umurnin shugaba, kamar yadda ya zo a Hadisan Annabi SAW. Domin a zamanin Manzo SAW, duk lokacin da aka ga wata, sai an zo an sanar da Annabi SAW, bayan ya tantance, ya tabbatar, sannan sai ya ba da umurnin daukar azumi ko ajiyewa.
Daga cikin irin wadannan hadisai, akwai hadisin Ibnu Umar, ya ce, “mutane sun yi kokarin ganin wata turu, sai na gaya wa Annabi SAW cewa, ‘ni ma na gan shi’. Sai (Annabi SAW) ya dauki azumi, ya sa jama’a su dauka”. Abu Dawud, Hakim, Ibnu Hibban suka rawaito. Hakim da Ibnu Hibban sun inganta hadisin. Baihakiy, Darukutniy da Darimiy ma sun rawaito shi. Kuma Ibnu Hazmin ya inganta hadisin.
Ikrima ya ji Ibnu Abbas yana cewa, wani Balaraben kauye ya zo wajen Annabi SAW ya sanar da shi cewa ya ga wata, sai Annabi SAW ya ce, “ka yi imani babu abin bauta wa bisa cancanta sai Allah?’’ Ya ce ‘e’. Sannan sai Annabi SAW ya ce, “ka yi imani Muhammadu manzon Allah ne?’’ Ya ce ‘e’, sai Annabi SAW, ya ce, “Ya Bilal, ka sanar da jama’a cewa su tashi da azumi daga gobe.’’ Malamai 5 suka rawaito shi, banda Ahmad. Haka nan Ibnu Hibban, Darimiy, Darukutniy, Hakim da Baihakiy ma sun rawaito shi.
Daga Rib’iy Bin Harash, daga daya daga cikin sahabban Annabi SAW ya ce, an samu sabanin ko ranar ce karshen Ramadan ko ba ita ce ba, sai wani Balaraben kauye ya zo ya rantse a gaban Annabi SAW cewa ya ga wata a wannan maraicen, sai Annabi SAW ya umurci jama’a su sha ruwa kuma su fito Sallar Idi kashegari.
Daga A’ishah RA, ta ce, Manzo SAW ya ce, ‘‘ranar daukar azumi ta hakika, ita ce ranar da (shugabanni da mafiya al’umma) suka dauki azumi; ranar saukewa, ita ce ranar da suka sauke.’’ Tirmidhiy ya rawaito, kuma ya inganta shi kuma ya ce, malamai sun fassara cewa, wannan hadisi yana nufin jama’a suna daukar azumi tare; su sauke tare, bisa umurnin Sarki ko shugaba.
Khattabiy ya ce, hadisin yana nufin cewa, an yafe kuskuren da aka yi gaba daya tare; idan mutane sun yi iya kokarinsu. Idan mutane suka yi iyakar dubawa ba su ga wata ba, suka yi azumi 30, idan daga baya aka gano watan kwana 29 ya yi, azuminsu karbabbe ne. Haka nan kurakuran da aka yi wajen tsaida ranar aikin Hajji, idi da sauran ranakun ibada masu tsarki. Haka nan hadisin yana nufin idan wani mutum ya ga wata shi kadai, sannan sai shugabanni suka ki karbar shaidarsa, ba shi da ikon ya dauki azumi shi kadai.
Muhammad Binul Hassan Al Shaibaniy ya ce, idan mutum ya ga wata kuma aka yi watsi da shaidar ganinsa, ba shi da ikon daukar azumi shi kadai; ko da tabbas ya ga watan. Haka ‘Ata’a da Al Hassan ma suka fassara wannan hadisi.
Daga Abi Bakarata, Annabi SAW ya ce, ‘ranakun idi guda biyu ba sa tawaya; Ramadan da Dhul Hijjah.’ Bukhari, Muslim da Abu Dawud suka rawaito. Mafi kyau daga cikin fassarorin da malamai suka yi wa wannan hadisi shi ne cewa, kurakuran da shugabanni suka yi wajen tsayar da ranakun azumi da aikin Hajji da makamantansu ba za su tauye samun cikakkar ladar ibadun da aka yi a bisa wadannan ranaku da aka yi kuskure ba.
Wadannan Hadisai, sun nuna cewa, ranar da shugaba ya tsayar, ko da bisa kuskure ne, shari’a ta amince da wannan hukuncin da shugaba ya yanke bisa kuskure kuma ibadar da aka aiwatar bisa wannan kuskuren rana, karbabbiya ce mai cikakkar lada.
Muhammad Sani Isa ya rubuto ne daga:
AB 29, Umar Suleiman Rd, BUK Old Site, Kano
Tel 080 3408 3456; e-mail: saniisa2191@yahoo.com
**{Legacy activities, comments etc counter: 915; topic series: 6; forum: MediaHausa; associated: 6- /*}