Topic: Wani abu kan watan Sha’aban (1)
Timeline: 2012-03-27 18:14:35
Wani abu kan watan Sha’aban (1)
A Rubuce Da Salihu Makera
Godiya ta tabbata ga Allah Makadaici. Allah Wanda ake nufi da bukata. Bai haifa ba, ba a haife Shi ba. Kuma babu wani tamka a gare Shi. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabi Muhammad, wanda bai bar komai da zai kusanta mu da Aljanna ya nesanta mu da wuta ba face ya sanar da mu. Ya Allah Ka kara tsira da aminci a gare shi da alayensa da sahabbansa da wadanda suka biyo su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, ga mu nan tsamo-tsamo a cikin watan Sha’aban watan jajiberan azumin Ramadan Mai girma.
Yawaita azumin Manzon Allah (SAW) a Sha’aban
Watan Sha’aban wata ne da Manzon Allah (SAW) yake yawaita azumin tadawwa’i a cikinsa fiye da kowane wata a bayan Ramadan. Kamar yadda Uwar Muminai A’isha (Allah Ya yarda da ita da mahaifinta) ta ruwaito cewa “Manzon Allah (SAW) ya kasance yana azumi har mu ce ba ya shan ruwa, kuma in yana sha ruwa har mukan ce ba ya azumi. Amma ban ga Manzon Allah (SAW) ya cika wata yana azumi ba, sai na watan Ramadan, kuma ban gan shi yana yawaita azumi ba kamar yadda yake yi a watan Sha’aban.” (Buhari da Muslim). Ibn Hajar ya ce, “Wannan Hadisi dalili ne kan falalar azumin Sha’aban.” (Fathul Bari Mujalladi na 4 shafi na 253). A cikin Lada’iful Ma’arif shafi na 247 Ibn Rajab ya ce “Amma azumin Manzon Allah (SAW) a mafi shaharar Sunnah ya ksance yana azumtar Sha’aban fiye da kowane wata.” Yayin da San’ani ya ce “A cikinsa (Hadisin) akwai dalilin cewa ya kebance Sha’aban da yin azumi fiye da waninsa.” (Subulus Salam, Mujalladi na 2 shafi na 342). Kuma A’isha (RA) ta ce “Watan da Manzon Allah (SAW) ya fi so ya azumnta a cikin watanni shi ne Sha’aban, sannan ya sadar da shi da Ramadan.” Ahmad ya ruwaito shi a Musnad, kuma Abu Dawuda da Nisa’i sun ruwaito shi, kuma Hakim ya ce Sahihi ne a bisa sharadin Buhari da Muslim, yayin da Albani ya inganta shi a cikin Abu Dawud. Hadisi na 2124.
Akwai ruwayoyi da dama kan falalar yawaita azumi a watan Sha’aban, kuma malamai sun karfafa haka tare da yin maganganu a kai.
Hikimar Yawaita azumtar Sha’aban
An karbo daga Usama Bin Zaid (RA) ya ce “Na ce Ya Manzon Allah ban gan ka kana azumi a wani wata daga cikin watanni ba, kamar yadda kake azumtar Sha’aban Sai ya ce “Wannan wata ne da mutane suke gafala daga gare shi a tsakanin Rajab da Ramadan. Shi ne watan da ake daukaka ayyukan bayin Allah zuwa ga Ubangijin talikai, don haka nake son a daukaka aikina ina azumi.” Ahmad da Nisa’i suka ruwaito kuma Albani ya inganta shi a cikin Attargib, Hadisi na 1022.
Bayan wannan ma’ana da Manzon Allah (SAW) ya bayar, malamai sun yi karin haske kansa. Ibn Rajab ya ce, “Kuma an ce a cikin azumin watan Sha’aban, akwai wata ma’ana ta daban, cewa azumtarsa kamar jarrabawar share fage ce ga azumin Ramadan, domin kada mutum ya shiga azumin Ramadan a cikin wahala, ta yadda mutum zai shiga cikin watan ya saba da azumin kuma ya goge da shi. Azumin Sha’aban a gabaninsa ya zame masa dandano, ta yadda zai fara azumin Ramadan da karfin jiki da nishadi.” (Lada’iful Ma’arif shafi na 251).
Daren Nisfu Sha’aban da kebance shi da tsayuwar dare
Wani sashi na malamai suna dogara da wasu ayoyi biyu da suke cikin Suratu Ad-Dukhan don nuna cewa a cikin daren rabin Sha’aban (Nisfu Sha’aban) ake kasafin ayyukan shekara don haka suka bullo da bidi’ar kebe daren da tsayuwar dare da wasu ayyukan ibada.
Ayoyin biyu suna cewa “Lallai Mun saukar da shi (Alkur’ani) a cikin wani dare mai albarka, kuma Mun kasance Masu gargadi. A cikinsa ake rarrabe (kasafta) kowane al’amari mai hikima.” (k Dukhan 3-4).
Akwai maganganun malamai kan ma wane dare ne ake nufi da wannan dare.
Kashi na farko wanda kuma shi ne mafi rinjaye sun tafi a kan daren Lailatul kadari ne da yake cikin watan Ramadan. Kuma shi ne fassarar Ibn Abbas da Hasanul Basri da Mujahid da Abu Abdurrahman As-Sulami da Ikrimata da Abu Jauza’i da Abu Nadrata da kattadah da Umar Maula Gafrata.
Daga Abdullahi Ibn Abbas (RA) ya ce game da fadinSa Madaukaki “A cikinsa ake rarrabe kowane al’amari mai hikima.” Cewa ana rubutawa a cikin Uwar Littafi a daren Lailatun kadari abin da zai kasance a cikin shekara na daga arziki da mutuwa da rayuwa da ruwan sama, har ana rubuta alhajin da zai yi hajji (ko wani da zai bukaci taimako daga wani).” Muhammad Bn Nadri da Ibn Munzir da Ibn Abu Hatim sun fitar da shi kamar yadda yake a Dururrul Mansur Mujalladi na 7 shafi na 399. Kuma ya sake cewa “Za ka ga mutum yana tafiya a kasuwanni, alhali sunansa ya fada cikin matattu. Sannan ya karanta “Lallai Mun saukar da shi a cikin dare mai albarka, kuma lallai Mun kasance Masu gargadi. A cikinsa ake rarrabe kowane al’amari mai hikima.” (Dukhan 3-4), ya ce “yana nufin dare Lailatul kadari, domin a ckin wannan dare ne ake rarrabe (kasafta) al’amuran duniya zuwa misalin shekara mai zuwa na daga mutuwa ko rayuwa ko arziki, kowane al’amarin duniya ana kasafta shi a wannan dare ne gwargwadon misalin shekara mai zuwa.” Hakim ya fitar da shi a Almstadrik Mujalladi na 2 shafi na 487, sannan Baihaki ya inganta shi a Shu’ubul Imani, Mujalladi na 3 shafi na 321, Abdu Bn Hamid da Ibn Munzir da Ibn Abu Hatim sun fitar da shi kamar yadda yake a cikin Ad-Dururl Mansur Mujalladi na 7 shafi na 400.
Daga Rabi’ata Ibn Khulsum ya ce “Na kasance a wurin Alhasan, sai wani mutum ya ce, “Ya Babban Sa’id, shin ana samun Lailatun kadari ne a kowane Ramadan” sai ya ce “Eh wallahi, lallai ana samunsa a kowane Ramadan. Shi ne daren da ake rarrabe (kasafta) kowane al’amari mai hikima a cikinsa. A cikinsa Allah Yake yanke kowane ajali da buri da arziki zuwa misalinsa.” Jarir ya ruwaito shi a tafsirinsa Mujalladi na 22 shafi na 9, haka ma Sa’id da Abdu Bn Hamid da Ibn Munzir kamar yadda ya zo a Dururul Mansur Mujalladi na 7 shafi na 399.
Daga Mujahid Bin Jabbar Al-Makkiy kan fadinSa Madaukaki “A cikinsa ake rarrabe kowane al’amari mai hikima.” Sai ya ce Daren Lailatun kadri ne, kowane abin da zai auku a shekara zuwa shekara na daga mutuwa da rayuwa, a cikinsa ake kaddara gwargwadon abin rayuwa da musibu dukkansu.” (4)
Daga Mansur ya ce “Na tambayi Mujahid na ce masa “Kana ganin ya dace dayanmu ya yi addu’a ya ce “Ya Ubangiji idan sunana ya kasnce a cikin mutane nagari Ka tabbatar da shi a cikinsu. Kuma idan sunana yana cikin shakiyyai, Ka shafe shi daga ciki, Ka sanya shi a cikin mutane nagari” sai ya ce “Da kyau.” Sannan bayan shekara na hadu da shi na sake tambayarsa kan wannan addu’a, sai ya ce “Lallai Mun saukar da shi a cikin dare mai albarka, kuma Mun kasance masu gargadi. A cikinsa ake rarrabe kowane al’amari mai hikima.” (Dukhan 3-4), ya ce “A cikin Dare Lailatul kadari Allah Yake yanke abin da zai kasance a shekara na daga arziki ko musiba. Sannan Ya gabatar da abin da Ya so, Ya jinkintar da abin da Ya so. Amma littafin masu rabo da shakiyyai shi tabbatacce ne ba ya sauyawa.” Ibn Jarir ya fitar da shi a cikin tafsirinsa Mujalladi na 22 shafi na 10.
Za mu cigaba insha Allah
**{Legacy activities, comments etc counter: 705; topic series: 1; forum: MediaHausa; associated: 1- /*}