Topic: Wani abu kan watan Sha’aban (2)
Timeline: 2012-03-27 18:18:43
Wani abu kan watan Sha’aban (2)
Haka dai masu wannan fahimta suka yi ta kawo hujjojinsu.
Magana ta biyu kuma ita ce, wannan dare yana nufin daren Nusfu Sha’aban ne. Kuma ita ce maganar Adda’u da kuma wata magana ta Ikrimata.
An karbo daga Muhammad Bin Sukah daga Ikrimata kan fadin Allah Madaukaki: “A cikinsa ake rarrabe kowane al’amari mai hikima.” Ya ce, “A cikin daren rabin Sha’aban ake tsara al’amarin shekara da shafe matattu daga rayayyu da rubuta mahajjatta, ba za a kara a cikinsu ba, ba za a rage wani daga cikinsu ba.” (Ibn Jarir ya fitar da shi a cikin tafsirinsa Mujalladinna 22 shafi na 10, sai Ibn Munzir da Ibn Abu Hatim kamar yadda yake a Durur Mujalladi na 7 shafi na 401 da Ibn Ad-Baisiy a Jaza: Lailatu Nisfu Min Sha’aban wa Fadluha shafi na 128-129. Wanda ya tabbatar da littafin Amru Bn Abdulmun’im Bn Sulaim ya raunata isnadinsa).
Daga Adda’u Bin Yassar ya ce: “Idan daren rabin Sha’aban ya kasance, sai a mika wa Mala’ikan Mutuwa wata takarda, a ce da shi: “Ka karbo ran wanda ke cikin wannan takarda.” Kuma lallai wani mutum zai shisshimfida shimfidu ya auri mata, ya yi gine-ginen gidaje alhali an sanya sunansa a cikin matattu.” (Ibn Abud Duniya ya fitar da shi kamar yadda yake cikin Durur Mujalladi na bakwai shafi na 402).
Maganar da ta fi karfi daga cikin biyun:
Maganar da ta fi karfi game da manufar daren da ake rarrabe ayyuka ita ce Daren Lailatul kadari ba daren rabin Sha’aban ba. Kuma dalilai a kan haka su ne:
1. Lamirin da ke cikin fadinSa Madaukaki: “A cikinsa” yana komawa ne kan dare mai albarka wanda aka saukar da Alkur’ani a cikinsa. Kuma dare mai albarka da aka saukar da Alkur’ani a cikinsa bisa magana ingantaciyya shi ne daren Lailatul kadari.
kattadah ya ce: “A cikin dare mai albarka”: shi ne Lailatul kadari.” (Jami’ul Bayan Mujalladi na 22 shafi na 7)
Ibn Zaid kuma ya ce: “Wannan dare shi ne daren Lailatun kadari. Allah Ya saukar da Alkur’ani daga Uwar Littafi a Lailatul kadari ne.” (Jami’ul Bayan Mujalladi na 22 shafi na 7). Ibn Jarir ya ce: “abin da ya fi zama daidai daga cikin maganganun shi ne maganar wanda ya ce ana nufin Lailatul kadari ne.” (Jami’ul Bayan Mujalladi na 22 shafi na 7).
2. Fadinsa Madaukaki: “Lallai mun saukar da shi a cikin Lailatul kadari.” Da kuma fadinSa: “Lallai Mun saukar da shi a dare mai albarka. Suna wajabta ya kasance wannan dare mai albarka shi ake kira da Lailatul kadari domin kada a samu warwara (a ayoyin biyu).” (Jami’ul Bayan, Mujalladi na 22 shafi na 8).
Akwai cewa Allah Madaukaki Ya fadi game da siffar Lailatul kadar: “ Mala’iku suna sauka tare da Ruhu a cikinsa da izinin Ubangijinsu daga kowane al’amari.” A nan kuma sai Ya ce: “A cikinsa (daren) ake rarrabe kowane al’amari mai hikima.” A nan akwai alaka tsakaninsa da “Mala’iku suna sauka a cikinsa tare da Ruhu.” Sannan akwai alaka tsakanin fadinSa “Umarni daga gare Mu…” da a cikin Saratul kadari da Ya ce: “Da izinin Ubangijinsu daga kowane al’amari (umarni). Idan siffofi suka kusanci juna ya wajabta a ce lallai daya daga cikin dararen nan biyu shi ne dayan. (Tafsirul Kabir, Mujalladi na 27 shafi na 238)
Sannan ma’anar fadinSa Madaukaki: “Lallai Mun saukar da shi a cikin daren Lailatul kadar.” Yana nufin daren kasafta abubuwa gwargwado al’amuran shekara ce na daga arziki da mutuwa da rayuwa da haihuwa da cuta da lafiya da annoba da fari da sauransu na al’amuran shekara. Kuma a bisa wannan tafsiri ingantacce na Lailatul kadar yake, kuma gwargadonta al’amura da aka ambata a hakika shi ne ake nufi da fadinSa Madaukaki: “A cikinsa ake rarrabe kowane al’amari mai hikima.” (Adwa’ul Bayan, Mujalladi na 7 shafi na 321, kuma a duba Alhawadis wal Bid’ah shafi na 265).
Ibn Jauziy ya ce: “A bisa abin da aka ruwaito daga Ikrimata cewa lallai wannan na faruwa ne a daren Nusfu Sha’aban, wannan ruwaya daga gare tana raurawa, kuma hakika maruwaicinta ya saba mata, domin an kuma ruwaito daga Ikirimata cewa ya ce: “A daren Lailatul kadari, kuma a kan haka masu tafsiri suka tafi.” (Zadul Musayyir, Mujalladi na 7 shafi na 112).
Ibn Al-Arabiy ya ce, “Jamhurun Malamai ya tafi a kan daren Lailatul kadar ne. Daga cikinsu akwai wanda ya ce daren Nusfu Sha’aban ne, wannan (ra’ayi) batacce ne, domin Allah Madaukaki Ya fada a LittafinSa yanke cewa: “Watan Ramadan wanda aka saukar da Alkur’ani a cikinsa.” Ya yi nassi a kan lokacin saukarsa a cikin Ramadan ne, sannan Ya nuna lokacin saukar a cikin dare ne cikin fadinSa: “Lallai Mun saukar da shi a cikin dare mai albarka.” Don haka duk wanda ya zaci a cikin waninsa ne hakika ya yi wa Allah karya. Babu wani Hadisi da za a iya dogaro da shi wajen cewa a cikin daren Nusfu Sha’aban ne. Babu a cikin fafalarsa ko a cikin amsar ajali a cikinsa, kada ka saurari irin wannan magana.” (Ahkamul kur’an, Mujalladi na 4 shafi na 1690).
Shi kuma Shaukani cewa ya yi: “Abin da yake gaskiya shi ne abin da Jamhurun Malamai suka tafi a kai cewa dare mai albarka shi ne daren Lailatul kadar ba daren Nusfu Sha’aban ba. Domin Allah Madaukaki Ya kawata shi Ya kuma bayyana shi a cikin Surar Bakara cikin fadinSa: “Watan Ramadan wanda aka saukar da Alkur’ani a cikinsa.” Da fadinSa a Sarar kadar: “Lallai Mun saukar da shi a cikin daren Lailatul kadar.” Don haka a bayan wannan bayani gamsasshe babu abin da zai sa a samu sabani, kuma bai kamata a ce akwai wani rudu ba.” (Fahul kadir Mujalladi na 4 shafi na 811).
Nan ma Malamai sun yi maganganu sosai kan wannan mas’ala.
Har wa yau malamai sun rabu biyu kan kebe daren Nusfu Sha’aban da tasyuwar dare da tahajjud da zikiri da addu’o’i, inda har mustahabbantar da yin wata Sallah da ake kira Salatul Alfiyya da ake karanta kulhuwallahu sau dubu a cikin raka’a 100. Wadansu malaman kuma suka mustahabbantar da raya daren Nusfu Sha’aban din da yin sallolin tahajjud cikin jama’a. Yayin da na uku suka ce a raya daren a daidaikun mutane. A cikin masu wannan ra’ayi akwai Imam Auza’iy. Kuma wannan ne mazhabar Abu Hanifa da zahirin maganar Shafi’iy da ruwayar Ahmad, wadanda suka dogara da hadisan da aka ruwaito kan falalar daren Nusfu Sha’aban, duk da cewa hadisan masu rauni ne, suna ganin ana aiki da Hadisi mai rauni a ayyukan falala (mustahabbai).
bangare na biyu kuma suna ganin babu halaccin kebe daren Nusfu Sha’aban da tsayuwar dare ko addu’o’i, suna ganin hakan bidi’a ce. Wannan shi ne ra’ayin mafi rinjayen malaman Hijaz kamar Adda’u da Ibn Abu Mulaika kuma shi ne maganar Malik da sauransu, inda suka ce: “Wannan duk bidi’a ce.” (Lada’iful Ma’arif shafi na 263).
Abdurrahman Bin Zaid Bin Aslam ya ce: “Ban riski wani daga cikin malamanmu da fakihanmu suna yin wani abu kan daren Nusfu Sha’aban ba. Kuma ban riski waninsu yana ambaton hadisin Makhul ba, ko yana ganin daren yana da wata falala a kan sauran darare ba. *****aha’u bas u yin haka. (Ibn Waddah ya yi isnadinda a cikin Albid’u wan Nahyu anha shafi na 92). Kuma daga cikin wadanda suka zabi wannan magana akwai Asshadabi (Al’I’tisam mujalladi na 1 shafi na 46) da Ibn Baz (Attahzir Minal Bid’i).
Kuma hujjarsu kan haka, shi ne hakan bai tabbata daga Annabi (SAW) ko Sahabbansa ko Tabi’ai da Tabi’ina da suka rayu a karni uku da Annabi (SAW) ya yaba.
Ibn Rajab ya ce: “Babu wani abu da ya tabbata kan tsayuwar dare a daren Nusfu Sha’aban daga Annabi (SAW) ko sahabbansa.” (Lada’iful Ma’arif shafi na 263).
Kuma Abul Khidab Ibn Dahiya ya ce: “Masana ilimin Hadisi (Ahlul Ta’adil wat tajrih) sun ce cikin Hadisan Nusfu Sha’aban babu ko Hadisi daya da ya inganta.” (Alba’is ala Inkarin Bidi’i wal Hawadis shaifi na 52 da Tahzir Minal Bid’a shafi na 16 ).
Haka dai malamai suka yi ta kawo hujjoji kan rashin ingancin kebe daren Nusfu Sha’aban da tsayuwar dare ko kebe ranarsa da azumi da sauran ibadojin da mutane suke yi.
Sai dai karancin lokaci ba zai ba mu dama mu tsawaita magana kan wanan batu ba, amma masu son kara bincike kan wannan batu suna iya zuwa su duba littattafan da muka ciro wadannan maganganu daga cikinsu da wadansu da ba mu ambata ba.
Allah Ya datar da mu ga bin abin da Ya yarda da shi, kamar yadda ManzonSa (SAW) ya koyar, kuma mu yi shi domin neman yardarm Allah.
Wasallallahu ala Nabiyyil karim wa alihi wasallim.
**{Legacy activities, comments etc counter: 2806; topic series: 1; forum: MediaHausa; associated: 1- /*}