Topic: Darussan da ke cikin azumin watan Ramadan (1)
Timeline: 2012-03-27 18:26:09
Darussan da ke cikin azumin watan Ramadan (1)
A Rubuce Da Salihu I.I. Makera
Bayan mun nazarci ayoyin da suka yi magana kan azumin watan Ramadan muna ganin yana da kyau mu nazarci wasu darussa da za mu iya dauka daga azumin watan Ramadan din. Wannan domin mu dada fahimtar hikimar da ke cikin wannan wata mai daraja ne.
Daga cikin darussan da za mu iya dauka a cikin azumin watan Ramadan akwai cewa:
1.Ramadan watan hakuri ne:
Assabru, wanda ke nufin hakuri da Hausa, shi ne kamewa. Arragib ya ce: “Hakuri shi ne kamewa a lokacin tsanani.” Kuma ya ce: “Ana kiran azumi da hakuri saboda kasancewarsa kamar nau’insa ne.” (Almufradat, shafi na 474). Dalili Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma ku nemi taimako da yin hakuri, da Sallah:…” (k:2:45). Ibn Jarir ya ce: “An ce ma’anar hakuri a nan na nufin azumi ne. Domin azumi wata ma’ana ce daga cikin ma’anonin hakuri a wurinmu.” (Tafsirin dabari, Mujalladi na 1 shafi na 259).
Ramadan da hakuri:
An karbko daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Watan hakuri da kwanaki uku a kowane wata azumin shekara ne.” Nisa’i ya ruwaito. Suyudi ya ce: “Watan hakuri shi ne watan Ramadan. Asalin hakuri kamewa ne, sai aka kira azumi da hakuri saboda abin da ke cikinsa na kame rai daga ci da sha da aure. (jima’i). (Sarhin Sunnani Nisa’i).
Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce ga wanda ya zo yana neman ya rika azumi kullum cewa: “Ka azumci watan hakuri da akalla rana daya a kowane wata….” Abu Dawuda da Ibn Majah suka ruwaito.
Ramadan makarantar koyon hakuri ne:
Don haka Ramadan makarantar koyon hakuri ne kamar yadda Ibn Rajab Alhambaliyyu ya ce: “Mafi falalar nau’o’in hakuri shi ne azumi. Domin ya tara hakuri kan abubuwa uku; shi hakuri ne wajen yin da’a ga Allah Madaukaki da hakuri wajen barin sabkon Allah. Saboda bawa yakan bar sha’awoyinsa saboda Allah alhali ransa yana jayayya da shi kan haka. Don haka ne Hadisi ingantacce ya zo cewa lallai Allah Madaukaki Yana cewa: “Kowane aiki na dan Adam nasa ne ban da azumi. Shi kan nawa ne, Ni zan saka a kai. Domin ya bar sha’awarsa da abincinsa da abin shansa saboda Ni.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
Kuma a cikinsa har wa yau akwai hakuri kan kaddara mai wahala da za su iya shafar mai azumi na daga yunwa da kishin ruwa. Manzon Allah (SAW) ya kasance yana kiran watan azumi watan hakuri. (Jami’ul Ulumi wal Hikami, Mujalladi na 1 shafi na 26).
Nau’o’in hakuri:
Ibn kayyim ya ce: “Hakuri bisa lura da abin da yake da alaka da shi ya kasu kashi uku: hakuri a kan bin umarce-umarcen Allah da ayyukan da’a har sai an aikata su. Da hakuri daga abubuwan da aka hana da sabko har a tabbatar ba a auka musu ba. Da hakuri kan kaddarori da abin da aka hukunta wa mutum har ya zamo bai fusata Allah a kansu ba.” (Mudarijus Salikina, Mujalladi na 2 shafi na 165).
2. Ramadan watan kyauta da kyautatawa da da’a da sadar da zumunta ne:
An karbko daga Ibn Abbas (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya kasance mafi kyauta a tsakanin mutane, amma kyautarrsa ta fi yawaita a watan Ramadan lokacin da Jibrilu yake ganawa da shi, kuma yana ganawa da shi ne a kowane dare na Ramadan yana yi masa darasun Alkur’ani. Manzon Allah (SAW) ya fi iskar sarfa yawan alheri.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
Ibn Hajrin ya ce: “A cikinsa (Hadisin) akwai nuni cewa yawan darasu (karanta) Alkur’ani yana sabunta alkawari da karuwar wadatar zucci, kuma wadatar zucci sababi ce na yin kyauta. Kuma kyauta a shari’a, shi ne bayar da abin da ya dace ga wanda ya dace, ita ta fi sadaka. Har wa yau Ramadan lokacin bikin alherai ne, domin ni’imar Allah a kan bayinSa a cikinsa tana karuwa fiye da waninsa. Don haka Manzon Allah (SAW) ya kasance yana tasirantuwa da bibiyar Sunnar Allah a cikin bayinSa. Duk abubuwan da aka ambata na lokaci da abin da ake saukar da shi da mai saukarwa da muzakkira, suna kara yin kyauta da ilimi a wurin Allah.” (Fathul Bari, Mujalladi na 1 shafi na 31).
**{Legacy activities, comments etc counter: 1136; topic series: 4; forum: MediaHausa; legacy score: 9; legacy ratings: 2; rating_ip: ***.*14.31.188; associated: 4- /*}