Topic: I’itikafi da hukunce-hukuncensa
Timeline: 2012-03-27 18:29:38
I’itikafi da hukunce-hukuncensa
A Rubuce Da Nata’ala Sambo Babi (Nasaba)
MA’ANAR I’itikafi a harshen Larabci ita ce tsayawa a kan abu, daga nan kuma sai aka yi amfani da kalmar ga wanda ya lazimci masallaci, domin tsayar da ibada a cikinsa, aka kira shi Mu’utakifun, ko Akifun, wato mai I’itikafi.
Ya zo a cikin Buhari daga Nana A’isha(RA), cewa Annabi (S.A.W) ya kasance yana I’itikafi a cikin kwanaki goma na karshen Ramadan har Allah Ya karbe shi, kuma matansa sun yi I’itikafi a bayansa. Annabi (S.A.W), ya ce “wanda ya yi I’itikafi na kwana daya don neman yardar Allah, Allah zai sanya ramuka uku a tsakaninsa da wuta, kowane rami zurfinsa ya fi nisan da ke tsakanin sama da kasa.” dabarani ne ya ruwaito.
Kuma ya tabbata cewa, Annabi (S.A.W) ya yi I’itikafi a karshen goman Shawwal. Buhari da Muslim suka ruwaito.
Allah Madaukaki Ya ce:“kuma kada ku rungume su alhali kuna masu I’itikafi a cikin masalattai, wadancan iyakokin Allah ne: don haka kada ku kusance su. (Bakara: 187).
Kuma Amirul Muminina Umar Bin Khaddabi (RA) ya ce da Annabi (S.A.W) ya Rasulallahi ni na yi bakance, a zamanin jahiliyya cewa zan yi I’itikafi na dare daya a Masallaci Mai alfarma? Sai ya ce ka cika bakancenka (ka yi I’itikafi na dare daya.) Buhari ya ruwaito.
I’itikafi shi ne mutum ya zauna a cikin masallaci domin yin zikiri da Sallah da karatun Alkur’ani, yana mai yin azumi, kuma mai kamewa daga yin jima’i da magabatan jima’i har kwana daya ko fiye da niyyar yin ibada.
Hukuncin I’itikafi
Hukuncin yin I’itikafi mustahabi ne mai lada da yawa, wajibi ne I’itikafi ya zamo a cikin masallaci. Mai yin sa yazamo yana yin azumi, ko na farilla ko na tadawwu’i da sharadin kwanakin yinsu a jere ba a yanke ba, Akallar I’itikafi kwana daya, mafi yawansa kuwa kwana goma, kuma an ce akallarsa kwana goma, mafi yawansa wata daya. Mafi girma I’itikafi shi ne na cikin watan azumin Ramadan, saboda Hadisin Abu Huraira (RA) cewa Annabi (S.A.W) ya kasance yana yin I’itikafi a goman karshe na Ramadan, da shekarar da zai yi wafati ta zo, sai ya yi na kwana ashirin.
Kuma Buhari ya ruwaito cewa Annabi (S.A.W) ya kasance yana yin I’itikafi a goman karshe na Ramadan har Allah, Ya karbi ransa.
Idan mutum zai fara I’itikafin da ya dauki alkawarin zai yi, zai shiga masallaci ne, gabanin faduwar rana, idan kuma ya kare zai bar masallaci ya tafi gida bayan sallar Magariba, wajibi ne mutum ya cika adadin kwanakin da ya dauki alkawarin yin I’itikafi, bai hallata ya rage su ba.
Mai yin I’itikafi zai fita wajen masallaci,domin lalurar dan Adam kamar fita cin abinci ko fitsari ko bahaya ko wanka ko alwala, kuma idan ya fita domin dayan wadannan abubuwa ba zai shige wuri mafi kusa ga inda zai biya bukatarsa ba, idan ya je wuri mafi nisa, I’itikafinsa ya baci, sai ya daura niyyar sabo.
Amma idan rashin lafiya ya kama mutum, ko kuwa jinin haila ko na biki ya zo ga mace tana I’itikafi, to za ta fita ta tafi gida, amma da zarar uzurin ya gushe sai ta dawo cikin masallaci da sauri ta ci gaba da I’itikafinta, watau za ta yi lissafi da kwanakin baya, kuma a lokacin zamanta a gida domin uzurin duk yana cikin hakkin I’itikafi, na barin jima’i da magabatansa.
Shiga I’itikafi
Idan mai I’itikafi ya ci abinci da rana da gangan, ko ya yi jima’i da rana ko da dare da gangan ko da mantuwa, I’itikafinsa ya baci, sai ya fara sabo tun daga farko.
Mai I’itikafi ba zai fita daga masallaci domin duba marar lafiya ba, sai idan dayan mahaifansa ne, kuma ba zai fita don Sallar Jana’iza ko yin ciniki ba.
Masallacin Idi daga can sai ya nufi gida.
I’itikafin mace da ziyartar mijinta a masallaci
Ya hallata mace ta ziyarci mijinta a wajen I’itikafinsa, shi kuma ya halatta ya taka mata har zuwa kofar masallaci. Safiyyah, (R.A) ta ce “Annabi (S.A.W.) ya kasance yana yin I’itikafi a goman karshe na Ramadan, sai na kai masa ziyara da daddare na tarar da shi da matansa sai suka tafi, na yi hira da shi zuwa wani lokaci, sannan na tashi zan koma, sai ya ce kada ki yi gaggawar tafiya, bari na taka miki. Sai ya tashi a lokacin kuwa mazaunina yana kusa da kofar gidan Usamatu Ibn Zaid, sai da ya kawo kofar masallacin da take kusa da kofar gidan Ummu Salamah, sai wadansu mutum biyu daga Ansar suka gilma da suka ga Annabi (S.A.W)sai suka kama sauri, sai Annabi(S.A.W) ya ce ku dakata, ba wani abin gudu ba ne, Safiyyah ce ’yar Huyayyu. Sai suka ce “subhanallah, ya Rasulullahi! Mu kuwa me zai sa mu zaci wani abu?” Sai ya ce “Ai kun san Shaidan yana bin jikin mutum ne, kamar yadda jini yake gudana a jikinsa, saboda haka na ji tsoron kada ya jefa wani sharri a zukatanku, ko kuma cewa ya yi (wani abu).”
Buhari da Muslim da Abu Dawud ne suka ruwaito shi.
Ya hallata mace ta yi I’itikafi ita kadai ko da mijinta, saboda fadin Nana A’isha (RA) cewa “Annabi (S.A.W) ya kasance yana yin itikafi a goman karshe na Ramadan, har Allah Ya karbi ransa, sa’annan matansa suka yi bayansa.” Buhari da Muslim da Abu Dawud ne suka ruwaito.
Ya halatta ga mai I’itikafi da waninsa ya yi alwala a masallaci. Kuma ya halatta ga mai I’itikafi ya kafa wani karamin tanti a karshen farfajiyar masallacin da zai yi I’itikafi a cikinsa, domin Nana A’isha (RA) ta kasance tana kafa wa Annabi (S.A.W) tanti idan yana I’itikafi, wannan kuwa yana kasancewa ne da umurninsa, kamar yadda ya zo a Sahihul Buhari da Sahihul Muslim.
Kuma ya halatta ga mai yin I’itikafi ya sanya shimfidarsa ko gadonsa a cikin tantin, saboda abin da Ibn Umar (RA) ya ruwaito daga Annabi (S.A.W) cewa shi idan ya tashi yin I’itikafi sai a yi masa shimfida, ko a sanya masa gado a bayan Al’amudin Tauba. Ibn Majah da Buhari ne suka ruwaito shi.
Ya halatta ga mai I’itikafi ya fita saboda wata bukata tasa ta dan Adam, kamar yadda bayani ya gabata, haka ma ya halatta gare shi ya fito da kansa daga masallaci don a wanke masa gashi ko a aske, Nana A’isha (RA) ta ce Annabi (S.A.W) ya kasance yana shigo min da kansa alhali yana I’itikafi a masallaci, ni kuma ina cikin dakina, sai na wanke masa shi kuma tsakanina da shi babu wani abu sai dandamalin kofa alhali ina haila, kuma ya kasance idan yana I’itikafi ba ya shigowa gida sai don wata lalura ta dan Adam. Buhari da Muslim da Ahmad da Ibn Abi Shaiba ne suka ruwaito shi.
Nata’ala Nasaba
Ya aiko da wannan rubutu ne daga Sakkwato
nasabaman@yahoo.com
08096967800
**{Legacy activities, comments etc counter: 881; topic series: 2; forum: MediaHausa; legacy score: 9; legacy ratings: 2; rating_ip: ***.*14.31.188; associated: 2- /*}