Topic: Tuba da istigfari
Timeline: 2012-03-27 18:34:17
Tuba da istigfari
A Rubuce Da Salihu Is’hak Makera
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mai gamammiyar kyauta a nan duniya, Mai kebantacciyar kyauta a Lahira. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halitta, Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da masu bin su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, assalamu alaikum ’yan uwa a cikin Musulunci.
Muna rokon Allah Ya amsa mana kyawawan ayyukan da muka gabatar a watan Ramadan, kuma Ya yafe gazawa da kura-kurai da laifuf*****an da muka yi a cikinsa. Allah Ya maimaita mana muna cikin Musulunci muna da imani.
Bayan haka, a yayin da muke ban kwana da watan azumin Ramadan, zai yi kyau mu waiwaya baya, mu dauki biyu daga cikin abubuwan da muka koya kuma ake so mu yawaita yi a cikinsa wato tuba da istigfari, ta yadda za mu nazarce su tare da fatar su zame mana jiki yau da kullum bai sai a cikin Ramadan kadai ba.
Tabbas idan muka riki wadannan abubuwa biyu rayuwarmu za ta inganta sakamakon yadda za mu kaurace wa aikata zunubai da miyagun ayyuka. Bismillah!
Ma’anar Tuba da bayani kanta:
Tuba (taubatun) a lugga: Ibn Manzur ya ce: “Ita ce juyawa daga (ko barin aikata) zunubi. Haka ma ma’anar taubu yake.”
Al-Akhfash kuma ya ce: “Attaubu, jam’in taubatun ne, kamar azmatun da azmun. Kan haka ne ake cewa: “Wa taba ilallahi ya tubu tawwaban wa mataba.” Ma’ana: Ya bari kuma ya juya wa sabo baya zuwa ga aikin da’a.”
Almubarrid ya tafi kan cewa kalmar taubu masdari ce, kamar kalmar kaulu, ko kuma jam’u ne na taubatun kamar kalmar lauzatun da lauzun, sai ya kafa hujja da fadin Allah Madaukaki: “Gafiriz zanbi, wa kabilu taubi”: Ma’ana “Mai gafarta zunubi kuma Mai karbar tuba” (k: 39: 3). (Tartibu Lisanil Arab, Mujalladi na 2 shafi na 61)
Abu Mansur ya ce: “Asalin taba (tuba) na nufin komawa zuwa ga Allah da dawowa zuwa ga yi maSa da’a. Daga cikinsa akwai fadinsa (SAW): “Ya Ubangiji! Ka karbi tubata, kuma Ka wanke dautata.” Tirmizi ya ruwaito, kuma ya ce Hadisi ne mai kyau. Idan aka ce “Taballahu alaihi” yana nufin Allah Ya karbi tubarsa. (Tahzibul Luggah, Mujalladi na 14 shafi na 332 da Almisbahul Munbar fi Garibi Sharhil Kabir, shafi na 78 da Almufradat na Ar-Ragib Al-Asfahani, shafi na 72 da Mu’ujamu Makayisl Luggah na Ibn Faris, Mujalladi na na 1 shafi na 357 da kuma Asasul Balagah shafi na 40).
Ubangiji Madaukaki da bawa suna yin tarayya a kalmar tauba. Idan aka jinginata ga bawa tana nufin ya koma ga Ubangijinsa daga barin sabo, idan aka siffanta ta ga Ubangiji Madaukaki tana nufin Ubangiji Yana juyowa zuwa ga bawa da rahamarSa da falalarSa.
Amma siffanta Allah da Tawwabu da sigar mubalaga. Yana nufin kaiwa karshe wajen aiki da yawan karbarsa, ko kuma saboda yawan masu tuba ga Allah Madaukaki, ko kuma Shi Mai jinkirta wa bayinSa da yawa ne don su tuba.” (Tafsirin Imam Razi, Mujalladi na 3 shafi na 22 da Jami’u Li Ahkamil kur’an, Mujalladi na 1 shafi 325 da Ruhul Ma’ani, Mujalladi na 1 shafi na 237-238 da kuma Tafsirin At-Tahrir Wat-Tanwir, Mujalladi na 1 shafi na 439).
Alhalimiy yana cewa game da tafsirin Tawwabu: “Cewa Shi Mai mayar da rahama da falala ne ga bawanSa a duk lokacin da ya koma ga yi maSa da’a, ya yi nadama a kan sabo. Ba zai bata abin da (bawa) ya gabatar na alheri ba, ba kuma zai haramta masa abin da Ya yi alkawari ga mai yi masa da’a ba na kyautatawa.
Alkhaddabi ya ce: “Attawwabu: shi ne wanda Yake sake karbar bawa a duk lokacin ya bar zunubi ya tuba.” (Fathul Bari Sharh Sahihul Buhari, Mujalladi na 11 shafi na 107).
Amma siffanta bawa da tawwabu yana nufin yawan komawa zuwa ga da’a, domin Allah Madaukaki Yana cewa: “Lallai Allah Yana son masu yawan tuba, kuma Yana son masu yawan tsarkakewa.” (k:2:222)
Ma’anar tuba a shari’a
A shari’a tuba tana da ma’anoni da dama kamar yadda malamai suka fassara ta. Daga ciki akwai:
Ibn Jarir Addabari ya ce: “Ma’anar tuba daga bawa zuwa ga Ubangijinsa ita ce: “Komawa zuwa ga yi wa Allah da’a da bin abin da Ya yarda da shi ta hanyar barin abin da Yake fusata shi na daga al’amuran da Ubangiji Yake ki.” (Tafsirin Ibn Jarir Ad-dabari, Mujalladi na 1 shafi na 283).
2. Khurdabi ya fassara tuba da cewa: “Ita ce yin nadama a zuciya da barin sabo nan take, da niyyar bawa ba zai koma ga aikata irinsa ba, kuma hakan ya kasance don jin kunyar Allah.” (Aljami’u Li-Ahkamil kur’an, Mujalladi na 5 shafi na 91).
Imam Khurdabi ya tara manyan sharuddan tuba, sai dai ba dukkansu ba ne, amma ya hada da muhimmin al’amari, wato shi ne ya kasance tuba ta kasance saboda Allah domin jin kunyarSa, ba don jin tsoron rasa mukami ko wani abin duniya ba.
3. Ar-Ragib Al-Isfahani ya fassara ta da cewa: “Tuba ita ce barin zunubi saboda kinsa da yin nadama a bisa saken da bawa ya yi da niyyar kin sake komawa ga sabon da kokarin aikawata abubuwan da suka kubuce masa gwargwadon irin ayyukan da zai iya yi. A duk lokacin da wadannan abubuwa hudu suka hadu, to hakika sharuddan tuba sun kammala.” (Al-Mufradat, shafi na 72).
Ibn Hajrin Al-Askalani ya kara kan ma’anar da Ar-Ragib ya ba tuba inda ya ce: “Da kuma mayar da kayan zalunci ga masu shi, ko samun yafewa daga gare su.” (Fathul Bari, Mujalladi na 11 shafi na 103).
4. Ibn Kasir ya ciro fassarar tuba daga sashin wadansu malamai, inda ya ce: “Tuba ta gaskiya ita ce bawa ya ciru daga zunubi nan take, kuma ya yi nadama bisa laifin da ya gabata, kuma ya yi niyyar ba zai sake aikata wannan laifi a gaba ba. Sannan idan ya kasance hakki ne na dan Adam, to ya mayar masa ta hanyar da ta dace.” (Tafsirin Ibn Kasir, Mujalladi na 4 shafi na 392, don karin bayani a duba At-Ta’arifat na Jurjani shafi na 95).
Nazari kan ma’anonin da suka gabata
Daga cikin abin da ya gabata za mu fahimci cewa lallai tuba ita ce bawa ya san munin zunubi da cutarwarsa a kansa, ya ciru daga gare shi yana mai tsarkake niyya ga Allah wajen ciruwarsa daga zunubi. Yana mai nadama a bisa abin da ya aikata na sabo a baya da niyya ko bisa jahilci, yana mai niyya niyya mai karfi na rashin komawa ga zunubin a nan gaba. Sai tsayuwa da aikata da’a da kyawawan ayyuka yana mai mayar da hakkokin mutane gare su, ko ya nemi gafararsu. (At-Tauba fi Dau’il kur’anil Karim na Dokta Amal Nusair shafi na 21).
’Yan uwa masu karatu idan muka lura za mu ga cewa tuba ba abu ne da ya tsaya ga furuci da baki kawai ba, a’a abu ne da ya hada da aiki da gabbai. Idan mutum ya ce ya tuba da fatar baki, to wajibi ne gabban da suke aikata sabo su hanu daga ci gaba da aikata wannan sabo. Misali idan mutum ya ce ya tuba daga karya, to wajibi ne ya daina karyar a nan take tare da niyyar ba zai sake yin karyar a rayuwarsa ba. Idan mutum ya ce ya tuba daga sata ko zina ko zamba cikin aminci, to wajibi ne hannunsa da farjinsa su kame daga aikata sata da zamba da zina. Zai zama isgili mutum ya ce ya tuba da fatar baki, amma gabban da suke aikata sabon ba su hanu ba. Don haka a yayin da muke ban kwana da Ramadan akwai wajibcin mu ci gaba da dabbaka darrusan da muka dauka a wannan wata mai albarka.
A mako mai zuwa cikin yardar Allah za mu duba ma’anar Istigfari da bayanan da malamai suka yi a kansa.
Wassalamu alaikum
**{Legacy activities, comments etc counter: 3123; topic series: 3; forum: MediaHausa; legacy score: 9; legacy ratings: 2; rating_ip: ***.*14.31.188; associated: 3- /*}