Topic: Layya da hukunce-hukuncenta (2)
Timeline: 2012-03-27 18:45:59
Layya da hukunce-hukuncenta (2)
A Rubuce Da Muntasir Umar Fagge Lokacin yanka layya
Lokacin yankan layya yana farawa ne daga lokacin da Liman ko Shugaban Musulmi ya yanka tasa dabbar layyar. Shi kuwa Liman zai yanka dabbar layyarsa ne bayan ya sallame Sallar Idi, bayan gama hudubarsa. Idan kuma Liman ba shi da abin da zai yi layya, in ya gama Sallah da huduba sai ya umarci jama’a kowa ya je gida ya yanka abin layyarsa.
Wadanda ba su kusa da masallaci kuma sai su kintaci daidai lokacin da ya isa a ce Liman ya gama yanka layyarsa, in da a ce zai yi layyar, sai su ma su yanka. Lokacin yin yankan yana zarcewa har zuwa faduwar ranar kwana ta uku daga kwanakin yanka. Dalili kuwa shi ne Hadisin da Bara’u (RA) ya ruwaito ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya yi yanka bayan an yi Sallah ya cika yankansa, kuma ya dace da Sunnah” (Buhari ya ruwaito), sai kuma wanda Jundubi bin Sufyan al-Bajli ya ruwaito cewa: “Na kasance tare da Annabi (SAW) a ranar yanka, sai yake cewa: “Wanda duk ya yanka kafin a yi Sallah, to, ya yanka wata a madadinta, wanda kuwa bai yanka ba, to, ya yanka.” (Buhari ya ruwaito).
Kuma wanda lokacin yankan da aka ambata a sama ya kubuce masa, ba zai yi ramuwar yankan a wani lokaci ba. Idan Liman ba tare da wani uzuri ba, ya yi jinkirin yanka layyarsa, sai a dan saurara gwargwadon lokacin da zai isa a yi yankan bayan gama Sallah, sai kowa ya yanka layyarsa. Idan kuwa akwai uzurin da ya sa ya jinkirta yanka layyar tasa, sai jama’a su saurare shi har zuwa kusa da zawali, ta yadda gwargwadon yankan ne kawai zai saura ga zawali, sai kowa ya yanka layyarsa.
Idan ba a yin Sallar Idi a gari, sai mutanen garin su kintaci gama Sallah da hudubar gari mafi kusa da su. Sannan kuma babu wani laifi a tare da su, koda ta bayyana cewa sun riga limamin wancan gari da suka kintata don yin layyar.
Abin so ga mai yin layya
1. Ya jinkirta aske duk wani gashi daga jikinsa da kuma jinkirta yin yankan farce har zuwa bayan goma ga Zul-hajji, daga zarar wata ya kama har sai ya yi layya. Duk daya ne ko shi ne zai yi layyar ko za a saka shi cikin ladanta ne. Saboda Hadisin da Ummu Salma (RA) ta ruwaito cewa Annabi (SAW) ya ce: “Idan goma (ta watan Zulhijja) ta fara, alhali kuma dayanku yana da niyar yin layya, kada ya shafi wani abu daga gashin jikinsa.” (Muslim ya ruwaito)
2. Ya yanka abin layyarsa da kansa. Wannan kuma duk daya ne ko mai yin layyar namiji ne ko mace ko yaro, saboda yin koyi da Annabi (SAW). An karbo daga Anas (RA) cewa “Manzon Allah (SAW) ya yanka taguwoyi guda bakwai da hannuwansa a tsaye” (Abu Dauda ya ruwaito). Abin ki ne mutum ya wakilta wani ya yanka masa, matukar dai zai iya yankawa da kansa.
3. Ya hallata mutum ya ci, ko ya yi sadaka, ya kuma yi kyauta da naman layyarsa, ba tare da iyakancewa ba.
4. Ya yanka dan dabbar layyar tasa, idan ya fito daga gare ta kafin ya yanka ta. Amma idan dan ya fito bayan an yanka uwarsa, wannan hukuncinsu daya da ita.
5. An so magaji ya aiwatar da layyar wanda ya gada, matukar dai ya nuna ta kafin mutuwarsa.
Abubuwn da ba a so mai yin layya ya yi
1. Aske gashin dabbar layyar kafin a yanka ta. Saboda yin hakan zai rage wa dabbar kyau.
2. Sayar da wannan gashi da aka ce kada a aske daga jikin dabba idan har an riga an aske din.
3. Shan nonon dabbar layyar ta tasa.
4. Ciyar da kafiri daga naman layyar.
5. Abin ki ne a yi wa mamaci layya. Sai dai idan tun kafin ya mutu ya nuna dabbar layyar tasa.
6. Abin ki ne a musanya dabbar layyar da wadda ba ta kai ta girma ko lafiya ba.
Allah Ya sa mu dace, Ya kuma karbi ibadunmu.
Muntasir Umar Fagge,
Kano
08037747019
**{Legacy activities, comments etc counter: 693; topic series: 6; forum: MediaHausa; associated: /*}