Topic: Tuba da istigfari (4)
Timeline: 2012-03-27 18:47:50
Tuba da istigfari (4)
A Rubuce Da Salihu Is’hak Makera
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mai gamammiyar kyauta a nan duniya, Mai kebantacciyar kyauta a Lahira. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halitta, Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da masu bin su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka yau za mu ci gaba da darasinmu kan wannan maudu’i mai girma kamar haka:
Imam Annawawi (Allah Ya lullube shi da rahamarSa) yana cewa cikin sharhinsa kan Hadisin kudusin nan mai cewa: “Ina inda bawaNa yake zatoNa.” Buhari Hadisi na 7405, sai Muslim Hadisi na 2675, cewa tuba wajiba ce daga dukkan sabo. Kuma wajibi ne a gaggauta ta, ba ya halatta a jinkirta ta, ya alla sabon karami ne ko babba. Kuma tuba tana daga cikin muhimman abubuwan Musulunci, kuma turakunsa masu karfi, wajibcinta a wurin Ahlus Sunnah bisa shari’a ne.” (Sharhu Sahihul Muslim, Mujalladi na 17 shafi na 59).
Shi kuwa Imam Algazali ya yi ta’aliki kan wajibcin tuba daga dukkan zunubai ne da cewa: “Amma bayanin wajibcin tuba a koyaushe kuma a kowane lokaci shi ne cewa kowane mutum ba ya kubuta daga aikata sabo da gabbansa, inda Annabawa ma ba su kubuta daga haka ba, kamar yadda ya zo a cikin Alkur’ani da kuma labaran kura-kuran Annabawa da tubarsu da kukansu kan kura-kuransu. Kuma idan mutum ya kubuta daga sabon gabbai a wasu halaye ba zai kubuta daga himmar zuciya ta aikata zunubi ba, idan kuma ya kubuta daga himmar zuciya a wasu halayen, ba zai kubuta daga wasi-wasin Shaidan ta hanyoyin sanya shi tunani iri-iri ba. Kuma idan ya kubuta daga gare shi ba zai kubuta daga gafala da gazawa wajen sanin Allah da siffofinSa da ayyukanSa ba. Dukkan wadannan nakasu ne kuma yana da sabubba, kuma barin sabubban ta hanyar shagalta da kishiyoyinsu komawa ce daga wata hanya zuwa kishiyarta.” (tsakure daga Ihya’u Ulumid Din, Mujalladi na 4 shafi na 10).
Sharuddan karbar tuba:
kofar tuba a bude take kullum ga dukkan wanda yake son shiga cikinta, bayan zuciyarsa ta farka, azamarsa ta yi karfi wajen kaurace wa sabo da zunubai.
Sayyid kutub ya ce: “kofar tuba a bude take a kowane lokaci, duk wanda ransa ya farka kuma ya yi nufin komowa ga Allah, babu mai wata manufa da zai iya hana shi, kuma ba a rufe fuskar mai tuba, duk yadda yake, kuma duk yadda ya kai ga yawan zunubi.” (Fi Zilalil kur’an, Mujalladi na 1 shafi na 258).
Don haka a bisa abin da muka ambata na ma’anar tuba muna iya rarraba sharuddan karbar tuba zuwa gida biyu:
Na farko, sharuddan da suka shafi barin tuba.
Na biyu, sharuddan da suka shafi lokacin karbar tubar.
Sharuddan da suka shafi barin zunubi:
Sahardi na daya: Musulunci.
Tuba ba ta inganta sai daga Musulmi. Amma kafiri tubarsa tana nufin shigarsa Musulunci. Imam kurdabi ya ce: “Ka sani lallai ita tuba, takan kasance ne daga kafirci ko zunubi. Tubar kafiri karbabbiya ce yanke, babu wata jayayya kan haka, amma tubar mai zunubi karbabbiya ce bisa wa’adi gasakantacce.” (Almufham bi Sharhi Mukhtasar Sahihul Muslim, Mujalladi na 7 shafi na 717).
Allah Madaukaki Ya ce: “Ba tuba ba ce ga wadanda suke aikatawar munanan ayyuka har idan mutuwa ta halarci dayansu ya ce: “Lallai ni, na tuba yanzu.” Kuma ba tuba ba ce ga wadanda suke mutuwa alhali kuwa suna kafirai. Wadannan Mun yi musu tattalin wata azaba mai radadi.” (k:4:18)
Abin da ayar take nufi shi ne, kore aukuwar tuba daga mushirikai da kafairai, domin ba ya cikin sha’aninta ta zamo gare su. Kuma fadinSa “Kuma ba tuba ba ce ga wadanda suke mutuwa alhali kuwa suna kafirai.” Yana nufin babu tuba ga wadancan, kamar yadda babu tuba ga wadannan.” (Tafsirul Mannar, Mujalladi na 4 shafi na 448 da Mujalladi na 4 shafi na 450).
Kuma Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai ne, Allah ba Ya gafarta a yi shirki da Shi, kuma Yana gafarta abin da yake bayan wannan, ga wanda Yake so. Kuma wanda ya yi shirki da Allah, to, lallai shi ya bace bata mai nisa.” (k:4:116)
Sayyid kutub ya ce: “Ba a gafarta laifin shirka idan ma’abucinsa ya mutu a kansa. Alhali kuwa kofar tuba tana bude ga kowane zunubi koma bayansa, a inda Allah Ya so. Kuma dalilin kaurara laifin shirka da fitar da shi daga da’irar gafara, shi ne duk wanda ya yi wa Allah shirka yana fita ne daga iyakokin alheri da hali nagari gaba daya, kuma fidirarsa tana baci gaba daya ta yadda ba ta inganta har abada.” (Fi Zilalil kur’an, Mujalladi na 2 shafi na 760).
Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma idan suka tuba, kuma suka tsayar da Sallah, kuma suka bayar da Zakkah, to, ’yan uwanku ne a cikin addini, kuma Muna rarrabe ayoyi daki-daki, ga mutane wadanda suke sani.” (k:9: 11)
Sharadi na biyu: Ikhlasi:
Lallai mai tuba daga sabo, tubarsa ba ta inganta, sai da ikhlasi (tsarkake niyya da yin abu don Allah kawai). Duk wanda ya bar aikata zunubi daga cikin zunubai don wanin Allah, kamar tsoron kada a fallasa shi, ko kada mutane su rika zolayarsa da yi masa ba’a, ko kuma saboda ya gaza aikata zunubin, ko ya ji tsoron rasa wani abin duniya ko mukami, hakan ya sanya shi ya gaza ci gaba da aikata wannan sabo, misalin hakan shi ne, mutum ya ki karbar rashawa ba don tsoron Allah da tsoron la’anarSa ba, a’a sai don samun wani matsayi da ba zai samu ba matukar aka san yana karbar rashawar, to irin wannan tuba da tubar da ta gabata, takan kasance abar mayarwa bisa ittifakin ma’abuta ilimi.” (Fathul Bari, Mujalladi na 11 shafi na 103).
Allah Madaukaki Ya ce: “Saboda haka wanda ya kasance yana fatar haduwa da Ubangijinsa, to, sai ya yi aiki na kwarai. Kuma kada ya hada kowa ga bauta wa Ubangijinsa.” (k:18:110)
Game da fadinSa “Kuma kada ya hada kowa ga bauta wa Ubangijinsa.” Sheikh Asshankidi yana cewa: “Ta game kowane hani da ya wuce riya kawai, ma’ana kada ya bauta wa Ubangijinsa don riya da jiyarwa, kada ya sarrafa komai daga cikin hakkokin Mahaliccinsa zuwa ga wani daga cikin halittunSa, domin Allah Yana cewa: “Lallai ne, Allah ba Ya gafarta a yi shirki da Shi.” (k:4:116) da sauran ayoyi irin wannan. Za a fahimta daga saba wa wannan aya cewa, lallai wanda yake hada wani da Ubangijinsa wajen bauta, kuma ba ya aikata aikin kwarai, to wannan ba ya fatar haduwa da Ubangijinsa, kuma wanda ba ya fatar haduwa da Ubangijinsa ba ya da wani alheri a wurin Allah.” (Adwa’ul Bayan fi Idahil kur’an bil kur’an, Mujalladi na 4 shafi na 199).
Tuba tana daga cikin ayyukan kwarai da ya wajaba a samu ikhlasi a cikinta don ta samu karbuwa a wurin Allah Madaukaki, kamar dai sauran ibadoji da ayyukan neman kusantar Allah. Ayoyi da Hadisai a kan wannan batu sanannu ne kuma mashahurai ne.
Sharadi na uku: Ikirari da zunubi
Lallai tuba ba ta kasancewa sai akwai zunubi, wannan yana nufin mai tuba ya san cewa yana da zunubi, jahiltar mai tuba game da zunubinsa yana kore shiriya. Don haka tuba ba ta inganta sai tare da sanin zunubin mutum da ikirari ko furtawa da bakinsa, tare da neman kubuta daga cutarwar zunubin da mugun karshensa.
Sai mako na gaba insha-Allah za mu dora.
Wassalamu alaikum
**{Legacy activities, comments etc counter: 1984; topic series: 3; forum: MediaHausa; associated: 3- /*}