Topic: Matsayin gemu a Musulunci (5)
Timeline: 2012-03-27 19:28:10
Matsayin gemu a Musulunci (5)
A Rubuce Da Ahmad Muhammad
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin halittu, Muhammadu dan Abdullahi, sallallahu alaihi wasallam, tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsu har zuwa ranar karshe.
Ga ci gaban tsokaci kan matsayin gemu:
“Attirmiziy ya ruwaito hadisi cewa Manzon Allah, sallallaahu alaihi wasallam, ya ce, “Ba ya cikinmu, wanda ya kwaikwayi (ya kamantu) wadansu mutane, ba mu ba; kada ku kwaikwayi Yahudawa da Nasara.” Wani rahoton kuma ya yi nunin cewa: “Duk wanda ya kwaikwayi (ya yi kama da) wasu mutane, yana cikinsu.” Imam Ahmad ne ya ruwaito shi. Kuma Umar dan Khaddaab ya ki karbar shaidar wani da ya cire wani abu daga gemunsa.
“Imamu dan Abdul Barru ya fada a cikin littafin al-Tamheed cewa: “Haram ne a aske gemu, kuma ba wanda yake yin haka sai wanda yake da dabi’ar mata-maza (wato mai kwaikwayar mata). Ma’aikin Allah, sallallaahu alaihi wasallam, yana da gemu mai kauri, kamar yadda Muslim ya ruwaito daga Jaabir, Allah Ya yarda da shi; da kuma a cikin wadansu ruwayoyi. Bai halatta a cire wani abu daga gemu, saboda fassarar bai-daya (gamammiya) da take nuna haka a cikin dukan hujjojin hadisan da ke bayani a kan tsayar da gemu.” [karshen bayanin Ibn Taimiyya].
An tambayi Shaykh Ibn Baz (Allah Ya rahamshe shi) ko mene ne hukuncin wanda ya daidaita gefunan gemunsa, sai ya ce, “Abin da ake bukata dai shi ne a kyale gemu ya tohu, kada a taba shi (a yi masa kwaskwarima), saboda abin da aka tabbatar daga Manzon Allah, sallallaahu alaihi wasallam, inda ya ce a rage gashin baki a yalwata gemu; kuma a yi bamban da mushrikai – saheeh-muttafakun alaih. – Bukhaariy daga Ibn Umar, Allah Ya yarda da su. Muslim shi kuma daga Abu Hurairah, Allah Ya yarda da shi, Manzon Allah, sallallaahu alaihi wasallam, ya ce, a datse gashin baki a kyale gemu; a yi bamban da majusawa.
Dukan wadannan hadisai suna nuni da cewa wajibi ne a kyale gemu (kada a taba shi), amma a rage ko a datse gashin baki. Wannan shi ne tsarinMusulunci, kuma shi ne farilla, kamar yadda Ma’aiki, sallallaahu alaihi wasallam, ya koyar kuma ya yi kira zuwa gare shi. Kuma yin hakan shi ne bin dabi’ar Manzon Allah, sallallaahu alaihi wasallam, da sahabbansa, Allah Ya yarda da su gaba daya, wanda yake saba wa mushrikai da kuma kauce wa yin kamanci da su da kuma mata.
Dangane da hadisin da al-Tirmiziy (Allah Ya yi masa rahama) ya ruwaito kuwa, wanda ke cewa Manzon Allah, sallallaahu alaihi wasallam yakan rage tsawo da fadin gemunsa, wannan hadisin karya ne, kamar yadda masana suka bayyana; kuma ba ingantacce ba ne daga Manzon Allah, sallallaahu alaihi wasallam. Wadansu mutane sun doge wajen amfani da wannan hadisi a matsayin hujja (ta rage gemu, ba aske shi ba), alhali bai inganta ba, saboda a cikin isnadinsa akwai Umar ibn Haarun al-Balkhi, wanda aka zarge shi da karya.
Saboda haka bai halatta ba, ga wanda ya yi imani, ya bi wannan hadisi, ko kuma ya yi amfani da shi wajen dogaro (hujjar rage gemu, ba aske shi ba fa!) kamar yadda wadansu malamai kan fada, alhali an wajabta mana bin sunna dukanmu. Allah Yana cewa, “Duk wanda ya bi Manzo (Muhammad, sallallaahu alaihi wasallam), hakika ya bi Allah.” [al-Nisaa’ 4:80]
“Ka ce, “Ku yi da’a ga Allah, kuma ku yi da’a ga Manzo. To idan kun juya (baya – kun ki) kuma (shi) a kansa akwai abin da aka aza masa kawai (na iyar da sakon Allah), kuma a kanku akwai abin da aka aza muku kawai (na bin sakon). Kuma idan kun yi masa da’a za ku shiryu. Kuma babu abin da yake a kan Manzo face iyarwa bayyananna.” [al-Nuur 24:54]
“Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi da’a ga Allah, kuma ku yi da’a ga ManzonSa, da ma’abuta al’amari daga cikinku. Idan kun yi jayayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa, idan kun kasance kuna imani da Allah da Ranar Lahira. Wannan ne mafi alheri, kuma mafi kyau ga fassara.” [al-Nisaa’ 4:59]
Kuma Allah Shi ne Mataimaki. [Wannan shi ne karshen bayanin da aka cirato daga Majmuu’ Fataawa al-Shaykh ibn Baaz (4/443].
Na biyu: Bai halatta ba shugabanka (a wajen aikinka) ya umurci ka rage gemunka, domin wannan umurni ne na ka yi laifi, kuma kai bai halatta ka yi masa biyayya ba. Abin da ya kamata ka yi shi ne ka yi masa bayanin abin da shari’a ta ce, cikin natsuwa da ladabi da biyayya. Idan ya dage a kan bukatarsa, alhalin kai kuma za ka rasa aikinka, in ka ki rage gemun naka, al’amari ya danganta da irin halin da kake ciki. In kana iya samun wani aikin, sai ka bar wannan, alhalin kana mai neman yardar Allah. Idan kuma ba ka iya samun wani aikin, muna fatar Allah Ya gafarta maka wannan laifi na rage gemu, musamman saboda abin da malamai – magabata – suka nuna cewa mutum ya samu ya aikata haram a yayin da wani tsanani ya same shi alhalin ba yadda ya iya, - matukar dai ka takaita wajen rage gemun naka wajen yardar da shugaban naka. Allah Ya ce, “Sai ku bi Allah da takawa gwargwadon abin da kuka sami iko…” [al-Taghaabun 64:16].
Allah Shi ne mafi sani. [karshen bayanin kundin Fatawowin Musulunci – na Turanci – da aka fitar daga yanar sadarwa ta www.islam-ka.com – a watan Yuni 2009].
Tambaya: Mene ne hukuncin bin (sallar?) wanda yake aske gemu kuma har yakan zolayi (yin izgili ga) wadanda suke barin gemu, har yana umurtar su aske gemun?
Amsa: Dukkan yabo da godiya na Allah ne, kuma tsira da amincin Allah su tabbata ga Ma’aikinSa, iyalan gidansa da sahabbansa.
Ba ya halatta a yi wasa dangane da tsayar da gemun mutum, saboda tsayar da gemu bin umurnin Manzon Allah, sallallaahu alaihi wasallam, ne. A yi wa mai zolaya nasiha, a bayyana masa cewa yin ba’a kan tsayar da gemu, yana iya wuce matsayin babban zunubi ya kai ga kafirci (domin ba a wasa da hukuncin yi ko bari a Musulunci wai don raha kawai – wal’iyaazubillaah!). Allah, Mai girma da daukaka Ya ce, “…Ka ce: “Shin da Allah, da kuma ayoyinSa da ManzonSa kuka kasance kuna izgili?” Kada ku kawo wani uzuri, hakika, kun kafirta a bayan imaninku…” [Taubah 9:65, 66].
Kuma Allah Shi ne Mai bayar da cin nasara. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu Muhammad, da alayensa da sahabbansa. [Kwamitin dindindin na fatawa – wato Fataawa al-Lajnah al-Daa’imah].
Daga abin da ya gabata na bayanai, duk mai hankali da lura dangane da al’amarin addini, zai yi karatun ta-natsu, ya fahimci al’amarin gemu ba wasa ba ne. Kodayake, kamar yadda na fada tun a farkon wannan mukala, akwai jahilci a tare da mutane game da da yawa na hukunce-hukuncen addinin nan, amma wannan ba hujja ba ce da za ta sa mutum ya zauna yana biye wa al’ada ko kuma dabi’un wadanda ba musulmi ba – wai yana takamar ya “ci gaba.” Allah Ya tsare, Ya nuna mana gaskiya, Ya ba mu ikon bin ta, kuma Ya nuna mana karya, Ya ba mu ikon guje mata. Amin.
Nan zan gutsure wannan mukala tare da yin manuniya ga littattafan da aka tara fatawowin Musulunci da ake kira Fataawaa Islamiyyah (kodayake ’yan wadanda nake da su na Turanci ne – wato Islamic berdicts bugun farko na shekarar 2002) a mujalladi na farko daga shafi na 379; da kuma mujalladi na Takwas daga shafi na 233 – duk za a ga karin bayanai game da gemu.
Wasallallaahu alaa man laa nabiyya ba’adah, wa ala aalihi wa sahbihi wasallam.
**{Legacy activities, comments etc counter: 3738; topic series: 6; forum: MediaHausa; associated: 6- /*}