Topic: Macen Da Allah Ya Tsine Mata
Timeline: 2012-05-01 05:19:33
Macen Da Allah Ya Tsine Mata
A Rubuce Da Salihu Is’hak Makera
Daga Abu Ja’afar bin Ibrahim Nadabo kankara Godiya ta tabbata ga Allah muna gode maSa kuma muna neman taimakonSa. Lallai wanda Allah Ya shiryar babu mai batar da shi, wanda Ya batar babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma ina shaidwa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne.
Bayan haka ya ku ’yan uwa Musulmi kun san ko wace mace ce Allah Ya tsine mata?
Ita ce macen da ke fita ba tare da sanya tufafin Musulunci ba, ita ce take yin kwalliya ta shafa turare a jikinta ta fita titi tana sayar da naman jikinta. To wannan matar ta fada cikin tsinuwar Allah. Annabi Muhammad (SAW) ya ce akwai wasu siffofi na ’yan wuta amma ban gan su ba, wadansu mutane ne tare da su akwai bulali kamar bindin shanu suna dukan mutane da su da kuma wadansu mata suna sanye da tufafi amma tsirara suke yawo. Karkatattu masu karkatarwa gashin kansu kamar tozon rakumi wanda ya karkace. Ba su shiga Aljanna kuma ba za su ji kanshinta ba, kuma kanshinta ana jinsa daga tafiyar kaza zuwa kaza. Muslim ya ruwaito.
Ya ku bayin Allah! Macen da take fita ba tare da tufafin da Musulunci ya tsara ba, mujirima ce game da hakkin mijinta. Domin tana yin ado ga waninsa, wanda kuwa wajibi ne ta yi ado gare shi shi kadai. Macen da ke fita babu tuffain Musulunci mujrima ce ga mutanen da ke rayuwa da ita. Mace idan ta shafa turare ta yi kwalliya ta fita sai ta fitini maza da samarin da babu addini tare da su. Idan irin wannan matar ta fito ga maza sai ta ba su sha’awa idan ta ba su sha’awa sai su neme ta, idan suka neme ta sai alfashar zina ta bazu a tsakanin al’umma. Allah Ya ce: Lallai wadanda suke son yada alfasha ga wadanda suka yi imani, to suna da azaba mai radadi a duniya da Lahira kuma Allah Shi ne Masani, alhali ku ba ku sani ba (Nur: 19).
’Yan uwa Musulmi! Wajibi ne ga mace mai yawo ba da suturar Musulunci ba ta ji tsoron Allah a kan kanta, ta yi gaggawar tuba zuwa ga Allah. Allah Madaukaki Ya ce: “Ku tuba zuwa ga Allah gaba daya ya ku muminai! Tsammaninku ku samu babban rabo.” (Nur: 31).
Sannan ’yan uwana Musulmi mu sani addu’a ibada ce, saboda haka ya zama wajibi mu kiyaye wadannan ka’idoji lokacin addu’a. Wadannan ka’idoji su ne:
1. Tsarkake niyya zuwa ga Allah. 2. Farawa da godiya ga Allah da yabo gare Shi da yi wa Annabi (SAW) salati. 3. Halarto da Ubangiji a cikin zuciya al okacin addu’a. 4. Addu’a lokacin da mutum yake cikin jin dadi da lokacin da yake cikin tsanani. 5. Kada mai addu’a ya roki kowa sai Allah Shi kadai. 6. Rashin yin mummunar addu’a ga iyali da ’ya’ya da dukiya da kansa. 7. Yin kasa-kasa da murya lokacin addu’a, wato tsakanin boyewa da bayyanawa. 8. Yin furuci da zunubi da neman gafara kansa. Da yin furuci da ni’ima da yin godiya ga Allah a kanta. 9. Mayar da abin da aka zalunta da yin tuba. 10. kankan da kai da nuna tsoron Allah da kwadayi da tsoro.
Abu Ja’afar bin Ibrahim Nadabo kankara
070 68353836
Imel: nanaaishanadabo@yahoo.com
**{Legacy activities, comments etc counter: 3056; topic series: 1; forum: MediaHausa; legacy score: 9; legacy ratings: 2; rating_ip: ***.*14.6.229; associated: 1- /*}