Topic: Me Ka Sani Gameda Annabi Muhammad (SAW)?: Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin (AI)
Timeline: 2012-05-13 06:16:27
Mai fassara: Muazu Abba Jabir
Me Ka Sani Gameda Annabi Muhammad (SAW)?: Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin (AI)
Yabo da Godiya su tabbata ga Allah ma]aukakin sarki wanda ya nuna mana hanyar shiriya, ya kuma kare mu daga fa]awa hanyar ~ata. Tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayye kuma za~a~~en manzonsa(Muhammadr), wanda aka aiko shi don ya zamo rahama ga dukkan talikai, kuma abin kowi ga masu bin hanyar
warai, tsira da aminci su tabbata ga alayensa da sahabbansa da duk wanda ya shiriya da shiriyarsu ar zuwa ranar
iyama. Bayan haka ;
Ya yan’uwa musulmai, ha{i}
a mafificin abin da za’a bashi lokaci da kulawa ta musamman shine karantar tarihi da rayuwar Annabir tsaftacacciya, domin ta kan sanya musulmi yaji tamkar cewa tare dashi akayi wannan rayuwar , takan kuma sanya shi yaji cewa shi ma ]aya daga cikin ma]aukaka kuma barrantattu(Sahabbai) wa]anda su ne }ashin-bayan kafuwan musulunci da samun ]aukakarsa. Kuma dai ta hanyar karantar tarihin ne musulmi zai san dayawa daga cikin siffofin Annabir da hanyoyin da yabi wajen }ira i zuwa ga musulunci alokacin zaman lafiya da kuma lokacin ya
i. Kamar yadda ta hanyar karantar tarihi ne musulmi zai gane lokuta da guraren da musulmai suke samun }arfi ko kuma rauni,da kuma abubuwan da suke kawo cin nasara ko kuma rashinsa, da kuma hanyoyin da za a bi wajen warware matsaloli idan suka faru komin girmansu.
Bugu da }ari, ta hanyar karantar tarihin Annabir ne musulmai zasu dawo da martabarsu da suke da ita ,ta hanyar sanin da tabbatar da cewa Allah yana tare dasu kuma zai taimakesu matu}ar suna bauta masa bauta ta gaskiya kuma suna mi}a wuya ga shari’arsa. Allah ma]aukakin sarki yace :
“إن تنصر الله ينصركم ويثبت أقدامكم. سورة محمد: 7 « In kuka taimaki Allah to zai taimake ku, kuma zai tabbatar da dugaduganku ». kuma yace:
“إنا لننصر رسلنا والذين ءامنوا في الحياة الدنيا ويوم يقوم الأشهاد” سورة غافر:51 « lallai hakika muna taimakon mazanninmu da wa]anda suka yi imani a rayuwar duniya da ranar da shaidu ke tsayawa(Kiyama). ». kuma yace :
ولينصرن الله من ينصره إن الله لقوي عزيز”.سورة الحج:40
«Ba shakka kuma Allah zai taimaki mai taimakonSa. Hakika Allah mai Karfi ne mabuwayi ».
‘Yan uwa Musulmai, ha}i}a abubuwan da za’a fa]a cikin wa]annan shafuf*****a, abubuwa ne ka]an game da tarihin Annabir, ta yadda zai zamo kamar shimfi]a ne da share fage ga duk mai bu}atar fa]a]a karatu da bincike kan tarihin Annabir. Allah ma]aukakin sarki yace :
“محمد رسول الله“ سورة الفتح:29
“ Muhammad manzon Allah ne”.
Muhimman abubuwa game da tarihin Annabir sune kamar haka:
DANGANTAKAR ANNABIr:
Shine (Baban Alqasim), Muhammad ]an Abdullah ]an Abdulmu]allib [an Hashim ]an Abdumanaf]an
usaiyi ]an Kilab ]an Murrah ]an Ka’ab ]an Lu’a’iyi ]an Galib ]an Fihri ]an Malik ]an Nadri ]an Kinanah ]an Khuzaimah ]an Mudrakah ]an Iliyas ]an Mudar ]an Nazar ]an Ma’add ]an Adnan. Wannan itace dangantakarsa wacce babu sa~ani akai, kamar yadda kuma ba’a yi sa~ani ba wajen cewa “Adnan” ]aya ne daga cikin zurriyar Annabi Isma’ilu.(wato kenan dangartakan Annabir ta ha]u da ta Annabi Isma’I ]an Annabi Ibrahimu).
2. SUNAYEN ANNABIr:
An kar~o hadisi daga Jubair ibn Mu]’im, Annabir ya ce :”Ha}i}a Ina da sunaye masu yawa;Ni ne Muhammad ,Ni ne Ahmad ,Ni ne Almahi (wato wanda Allah zai share kafirci da shi).Ni ne Al-hashir (wanda za’a fara tayar da shi ranar {iyama). Ni ne Al’a}ibu (wanda babu Annabi bayansa).[ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi].
An kar~o Hadisi daga Abu-musal’Ash‘ari yace :”Annabir ya kasance yana fa]a mana wasu daga cikin sunayensa sai ya ce : “Ni ne Muhammad, Ni ne Ahmad, Ni ne Mu}affi(wato na }arshen Annabawa), Ni ne Alhashir, Ni ne Nabiyyut-Taubah, Ni ne Nabiyyur- Rahmah”. [Muslim ne ya ruwaito shi].
3. TSARKAKAR DANGANTAKAR ANNABIr:
Ya ‘yan’uwa musulmai; ku sani cewa Annabinmu Muhammadr wanda shi ne fiyayyen halitta ; Allah ya kiyaye mahaifinsa(Abdullah) daga fa]awa cikin zina. Don haka an haifi Annabir ne ta hanyar aure irin wadda aka sani bata mummunar hanya ba.
An kar~o hadisi daga Wasilah ibn Asqa’I yace: Annabir ya ce: ‘Ha}i}a Allah ya fifita Annabi Isma’il daga cikin ‘ya’yan Annabi Ibrahimu, ya kuma fifita Kinana daga cikin ‘ya’yan gidan Isma’ilu, ya kuma fifita {uraishawa daga cikin ‘ya’yan gidan kinana, ya kuma fifita ‘ya’yan gidan Hashim daga cikin {uraishawa, Ni kuma ya fifita ni daga cikin ‘ya’yan gidan Hashim ». [Muslim ne ya ruwaito shi].
Haka kuma lokacin da (Hira}al) sarkin }asar Rum ya tambayi Abu-sufyan(]aya daga cikin masu nuna }iyayya ga Annabir kafin ya musulunta) game da dangantakar Annabir sai yace:” Lallai dangantakarsa mai kyau ce a cikin mu, sai Hira}al yace: Ha}i}a haka ne ma dukkan sauran Annabawa ake aiko su daga mafi kyawun dangartakar mutanensu. [Bukhari ne ya ruwaito shi].
4. HAIHUWAR ANNABIr:
An haifi Annabir ne ranar litinin a watan Rabi’ul Awwal, malamai sun }ara wa juna sani game da kwanan watan da aka haife shi; wasu suka ce: biyu(2) ga wata, wasu kuma: takwas(8) ga wata, wasu kuma: goma(10) ga wata, wasu kuma suka ce:Sha biyu(12) ga wata. Babban malamin Tafsirin nan (Ibn Kasir) yace: « Maganar da babu sa~ani akai ita ce cewa :An haife shi ne shekarar da ake }ira (shekarar Giwaye) kamar yadda Ibrahim ibnul -muzir Alhuzami (malamin Bukhari) da Khalifatu ibn Khayya] da sauransu suka fa]a.
Masana Tarihi suka ce: lokacin da mahaifiyar Annabir (Aminatu) ta ]auki cikinsa ta ce : « Ban ji nauyinsa ba kamar yadda sauran mata suke ji, lokacin dana haife shi kuwa ; sai wani haske ya fito tare da shi wanda ya haskaka gabar da yamma.
An kar~o hadisi daga Irbad ibn Sariya yace: “ Na ji Annabir yana cewa: Lallai ha}i}a tabbas haka Allah ya rubuta a cikin Lauhul-mahfuz cewa nine cikamakin Annabawa, haka kuma al’amarin ya ke agurinSa tun kafin a halicci Annabi Adamu, abubuwan da su ke nuna haka kuwa sune; Addu’ar mahaifina Annabi Ibrahimu (lokacin da ya ro}i Allah a aiko da wani manzo cikin larabawa), da kuma albishirin da Annabi Isau yayi wa mutanensa(cewa wani Annabi zai zo bayansa), da kuma hasken da mahaifiyata ta gani lokacin da ta haife ni, wanda ya haskaka }asar Sham (siriya).
Mahaifin Annabir ya rasu ne kafin a haife shi.Wasu malamai suka ce : ya rasu ne bayan haihuwarsa da wata ]aya ko kuma shekara ]aya.Amma maganar da tafi shahara ita ce ta farko.
5. SHAYAR DA ANNABIr:
Suwaibah ce ta shayar da shi zuwa ]an wani lokaci, sannan aka nema masa wajen shayarwa a }abilar (Bani-Sa’ad), sai Halimatus Sa’adiyya ta cigaba da shayar da shi, ya kuma zauna tare da ita tsawon shekara hu]u a gurin da }abilar Banu-Sa’ad ]in suke, a can ne ma aka tsaga }irjinsa aka tsaftace shi daga munanan halaye da rabon shai]an, ganin haka, Halimatus Sa’adiyya sai ta tsorata tayi gaggawar mayar da shi wajen mahaifiyarsa.
Mahaifiyarsa ta rasu ne a hanyar dawowanta zuwa Makka a wani guri da ake }ira (Abwa’i), a lokacin yana da shekara shida. Saboda haka ne ma lokacin da Annabir ya zo wucewa ta wannan gurin zai nufi garin Makka shekarar da akayi (Fathu Makka) sai ya tsaya a gurin ya nemi izinin Ubangijinsa don ya ziyarci kabarinta, Allah yayi masa izini, sai ya tsaya yayi kuka har yasa wa]anda suke tare da shi kuka.kuma yace: “ku ziyarci {aburbura domin tana tunatar da mutuwa.” [Muslim ne ya ruwaito shi].
Ummu-aiman (baiwar da ya ci gadanta a gurin babansa.) ita ta cigaba da rainonsa bayan rasuwar Mahaifiyarsa, sai kakansa Abdulmu]allib ya cigaba da kula dashi. Lokacin da Annabir ya kai shekara takwas, kakansa sai ya rasu, amma kafin rasuwarsa, sai ya bada wasiccin ri}on Annabir wa Baffansa(wato Abu-[alib) sai ya cigaba da kula dashi, ya kuma bashi cikakkiyar kulawa da taimako da kuma goyon baya musamman ma lokacin da aka bashi manzanci, duk da cewa shi bai musulunta ba. Saboda haka ne ma ranar {iyama Allah zai sassauta masa azaba kamar yadda ya tabbata a ingantaccen hadisi.
KIYAYEWAR DA ALLAH YA YI MASAr DAGA {AZANTAR JAHILIYYA:
Allah ma]aukakin sarki ya kiyaye annabinSa tun yana }arami daga }azantar jahiliyya da ma kowace irin aibi, ya kuma }awata shi da halaye masu kyau, har ya zamo sunan da ya yafi shahara dashi a cikin mutanensa shi ne; Al-‘ameen (wato amintacce), lura da abubuwan da suka bayyana musu na tsarkakansa da gaskiyarsa da ri}on amanarsa. Saboda haka ne ma lokacin da {uraishawa suka yi nufin sa ke gina ]akin {a’aba, a lokacin yana da shekara Talatin da biyar, bayan sun gama ginawa sai suka yi sa~ani wajen mayar da Hajrul-Aswad(Ba}in dutse) gurbinsa, kowace {abila tana cewa ita zata mayar don ta samu wannan falalar, daga }arshe sai suka daidaita kan cewa; gaba ]ayansu sun amince duk wanda ya fara shigowa masallacin to shi zai mai da dutsen gurbinsa, sai ko akayi dace wanda ya fara shigowa masallacin shine Annabir, sai suka ce Al-‘ameen ya zo kuma suka amince cewa shi zai mai da dutsen. Sai Annabir ya shimfi]a mayafinsa a }asa, ya ]auki dutsen da hannunsa ya ]aura a tsakiyar mayafin, (kasancewar da ma manya-manyan {abilun su hu]u ne); Annabir sai ya umarci wakilin kowace {abilar da ya ri}e gefen mayafin sannan su ]aga shi zuwa gurin da za’a mayar da da dutsen, Annabir sai ya ]auka da hannunsa ya mai dashi gurbinsa. [Ahmad da Hakim ne suka ruwaito shi].
7. AUREN ANNABIr:
Annbir ya auri Khadija ce lokacin yana da shekara Ashirin da biyar(25). Dalilin auren kuwa shine : Annabir ya fita fatauci wa khadija zuwa }asar sham(siriya) tare da yaron gidanta Maisarah. Bayan dawowarsu daga fataucin, sai maisarah ya ba wa khadija labarin abubuwan mamaki da ya gani game da Annabir da kuma irin gaskiyarsa da ri}on amanarsa, daga nan sai khadija ta nemi Annabir da ya aure ta. Annabir bai }ara aure ba har zuwa rasuwar khadija (ta rasu ne kafin a yi hijira zuwa Madinah da shekara uku). Bayan rasuwarta sai Annabir ya auri Saudah ‘yar Zam’an, sannan ya auri A’ishah ‘yar Abubakar, (ita ka]ai ce Annabir ya aure ta tana budurwa). Sannan ya auri Hafsah ‘yar Umar, sai Zainab ‘yar Khuzaimah, sai Ummu-salma(asalin sunanta Hindu ‘yar Umaiya). Sannan ya auri Zainab ‘yar Jahsh, sai Juwairiyya ‘yar Haris, sai Ummu-habiba(asalin sunanta Ramlah ko Hindu ‘yar Abu-sufyan). Sannan sai ya auri Safiyya ‘yar Huyayyi lokacin da akayi ya}in Khaibar , sai ya auri Maimunah ‘yar Haris wacce ita ce mace ta }arshe da Annabi r ya aura(Allah ya }ara musu yarda).
8. ‘YA’YAYEN ANNABIr:
Dukkanin ‘ya’yayen Annabir maza da mata in banda Ibrahim ; Khadija ce ta haifa masa su. Mahaifiyar Ibrahim ita ce Mariyatul Kib]iyya wacce Mu}au}is ya ba da ita kyauta wa Annabir.
‘ya’yayensa maza sune :
Al-}asim (da shi ne ake yi wa Annabir alkunya, kuma bai jima ba a duniya ya rasu). Sai A]-]ahir da A]-]ayyib.Wasu malamai suka ce : ]ansa Abdullahi shi ne ake masa la}abi da A]-]ahir da A]-]ayyib domin an haife shi ne a cikin musulunci. An haifi Ibrahim ne a Madinah, ya rayu tsawon watanni Ashirin da biyu, ya riga Annabir rasuwa da wata uku.
‘ya’yayensa mata sune :
Zainab : ita ce babbarsu, ]an goggonta (Abul-Ass) ne ya aure ta.
Ru}aiyah: mijinta shi ne Usman bn Affan.
Fa]imah: mijinta shine Aliyyu bn Abi-[alib, ta haifa masa Al-hasan da Al-husain (shuwagabanin matasan Aljannah).
Ummu-kulsum: Usman bn Affan ne ya aure ta bayan rasuwar Ru}aiyah ( Allah ya }ara musu yarda).
Imam Nawawi yace: « Babu sa~ani kan cewa ‘ya’yayen Annabir mata su hu]u ne, maza kuwa su uku ne a bisa ingantacciyar magana ».
9. AIKO ANNABIr DA MANZANCI :
An aiko Annabir da manzanci ne lokacin da ya cika shekara Arba’in a rayuwarsa.
Mala’ika Jibril ya fara zuwa masa ne ranar Litinin goma sha bakwai (17) ga watan Ramadhan a lokacin yana kogon Hira. Kuma ya kasance a duk lokacin da wahayi ya zo masa, ya kan shiga mawuyacin hali, fuskarsa takan canza, kuma Goshinsa yayi zufa.
Lokacin da Mala’ikan ya zo masa a karo na farko, yace da shi: ka yi karatu !. sai Annabir ya ce : Ni ban iya karatu ba !!. Sai Mala’ikan ya dam}e shi da }arfi har sanda Annabir ya shiga mawuyacin hali sannan ya sake shi, ya sake ce masa : ka yi karatu !!. Annabir ya ce : Ni ban iya karatu ba !!!. haka aka yi har sau uku, ana ukun sai Mala’ikan ya ce da shi : « Kayi karatu da sunan Ubangijinka wanda yayi halitta.* Ya halitta mutum daga gudan jini.* Ka yi karatu, kuma Ubangijinka shi ne mafi karimci.* Wanda ya sanar (da mutum) game da alkalami.* Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.* ». [ suratul Alaq, Aya :(1-5) ].
Sai manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya dawo gurin Khadija a firgice yana ~ari, ya bata labarin abubuwan da suka faru da shi. Khadija (Allah ya }ara mata yarda) sai ta kwantar masa da hankali ta ce : « Albishirinka !! ha}i}a nasan Allah ba zai tozartar da kai ba har abada, domin kuwa kana sadar da zumunci !, kana fa]in gaskiya !, kana ]aukan nauyin marar galihu !, kuma kana taimakon wa]anda masifu suka afka musu.
Daga nan sai wahayi ya yanke, Annabir ya zauna tsawon lokaci wahayi baya zuwa masa. Ana nan a haka wata rana Annabir yana tafiya cikin garin Makka, sai mala’ikan da ya zo masa a karo na farko ya bayyana masa a sama da shi, yana mai kwantar masa da hankali da kuma masa albishirin cewa ha}i}a shi ]an aiken Allah ne zuwa ga mutane. Lokacin da Annabir ya ganshi sai ya firgita ya juya ya koma gida wajen Khadija(R.A) yana cewa : ku lullu~e ni ! ku lullu~e ni !!. Sai Allah ya sau}ar masa da wahayi cewa : « Ya wanda ya lullu~a da mayafi.* Ka tashi domin kayi garga]i wa mutane.* Kuma ka girmama Ubangijinka.* Kuma ka tsarkake tufafinka”. [ suratul Muddassir, Aya:(1-4) ].
Wa]annan ayoyi sun }unshi umarni ne ga Annabir daya tashi yayi garga]i wa mutanensa ga barin shirka ya kuma }ira su i zuwa ga bautar Allah shi ka]ai. Daga nan ne fa Annabir yayi ]amara ya zage damtse ba dare ba rana ya fara }irar yara da manya, maza da mata, ‘ya’yaye da bayi, ba}i da fari kan azo a bauta wa Allah ma]aukakain sarki.Sai aka samu cikin kowace {abila wa]anda Allah ya nufe su da shiriya da samun rabo duniya da lahira suka amsa }irarsa,suka musulunta. Kafiran Makka sai suka fara cutar dasu suna gana musu ba}ar azaba, amma Annabir Allah ya kare shi ne daga cutarwarsu ta hanyar baffansa Abu-[alib, domin ya kasance mutum ne mai daraja da fa]a-aji a cikinsu, don haka baza su iya cutar da Annabir da komai ba saboda sun san irin son da yake yi masa.
Imam Ibnul Jauzi yace : Annabir ya zauna a Makka tsawon shekaru uku yana Da’awarsa a ~oye, bayan sau}an fa]in Allah ta’ala : « sai ka tsage gaskiya game da abin da aka umarceka dashi, ka kuma kau da kai daga masu shirka ». [ suratul Hijri,Aya :(94)],sai Annabir ya fara Da’awarsa a bayyane. Lokacin da fa]in Allah ta’ala ya sau}a : « kuma kayi garga]i ga danginka mafiya kusanci ».[ suratu Ashshu’ara’I, Aya:(214)]. Sai Annabir ya fito ya hau dutsen Safa yayi kira da }arfi yace : Ya ku mutane na !! sai mutane suka ce wa ye yake }ira ?!sai akace : ai Muhammadu ne, sai suka zo suka tattaru, Annabir yace dasu : Ya ‘ya’yan gidan wane da wane………, Ya ‘ya’yan gidan Abdu manaf, ya ‘ya’yan gidan Abdul-mu]allib………..yanzu zaku gaskatani in nace muku wani doki zai fito ta }ar}ashin wannan dutsen ?! sai suka ce : }warai da gaske, domin kuwa baka ta~a mana }arya ba, sai yace dasu : to ha}i}a ni mai garga]i ne agare ku kafin zuwan azaba mai tsanani(ga wanda ya}i yin Imani). Sai baffansa Abu-lahab yace : « tir da kai yanzu da ma don wannan kawai ka taramu »,sai ya tashi ya tafi, sai Allah ta’ala ya sau}ar da suratul Masad cewa : « Hannaye biyu na Abu- lahab sun halaka kuma ya halaka……. » har zuwa }arshen surar. [Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi].
JURIYAR ANNABIr KAN CUTARWAR DA AKE MASA:
Annabir ya kasance mai ha}uri ne da neman lada kan duk abubuwan da yake fuskanta daga mutanensa na wahalhalu da tsanani. Har ma ya kai ga cewa ya umarcin sahabbansa da suyi hijira zuwa }asar habasha(Eutopia) don guje wa zalunci da }as}ancin da suke fuskanta, sai suka aikata hakan.
Babban malamin tarihin nan (Ibn- Ishaq) yace: lokacin da baffan Annabir ( Abu-[alib) ya rasu, sai {uraishawa suka fara cutar da Annabir cutarwa mai tsanani wadda basu ta~a tsammanin zasu iya masa irinsa ba lokacin baffansa yana da rai. Abu-Nu’aim ya ruwaito hadisi daga Abu-Huraira(R.A) yace: lokacin da Abu-[alib ya rasu sai {uraishawa suka }untata wa Annabir, har Annabir ya ke cewa: Ya baffana!! Ban ji da]in rashinka da nayi ba.!!
Hadisi ya zo cikin Bukhari da Muslim cewa: wata rana Annabir yana sallah a masallacin {a’aba, sai Uqbah ]an Abi-mu’ai] ya ]auko mahaifar Ra}umi ya zuba a bayan Annabir, Annabir bai ]ago daga sujjada ba har sanda ‘yarsa Fa]imah tazo ta ]auke, sai Annabir a lokacin yace: “Ya Allah ka dam}i wane da wane cikin {uraishawan nan”. Hadisi ya zo cikin Bukhari cewa:”wata rana Uqbah ]an Abi –mu’ai] yazo ta bayan Annabir sai ya sha}e shi sha}a mai tsanani, har sanda Abubakar(R.A) ya zo ya ture shi yace: don me zaku kashe mutum(Annabir) haka kawai don ya ce ubangijinsa shine Allah?!!”.
11. RAHAMAR ANNABIr DA TAUSAYINSA GA MUTANENSA:
Lokacin da cutarwa ya tsananta ga Annabir bayan rasuwar Abu-[alib da Khadija(R.A) ; Annabir sai ya fita daga Makka ya nufi garin [a’if, anan ne ya }ira }abilar Sa}iif i zuwa ga musulunci, saidai kash !ha}o bai cimma ruwa ba, domin kuwa basu tari Annabir da komai ba in banda cutarwa mai tsanana da izgilanci da tsaurin kai, har ya kai ga cewa sun jejjefe shi da duwatsu suka ji masa rauni a }afafuwarsa, daga }arshe Annabir sai ya yanke shawarar dawowa garin Makka. Annabir yace : « Na kamo hanyar dawowa daga [a’if ina cike da ba}in ciki, ban fa]aka ba har sanda na zo gurin da ake }ira {arnus-sa’alib (mi}atin mutanen Najd), ina ]aga kaina sai ga wani girgije yamin inuwa, dana duba sai naga ashe mala’ika Jibril ne a ciki, sai ya }ira ni yace : ha}i}a Allah yaji abin da muta nenka suka gaya maka, da kuma martanin da sukayi maka, yanzu haka Allah ya aiko maka da mala’ikan dake ri}e da duwatsu ne don ka umarce shi da duk abin da kaso ayi dasu. Sannan sai mala’ikan dake ri}e da duwatsu ya }ira ni ya min sallama yace : Ya Muhammad ! ha}i}a Allah yaji maganar da mutanenka suka maka, kuma nine mala’ikan dake ri}e da duwatsu, Allah ya turoni ne don ka umarce ni da duk abin da kaso, in kaso yanzu sai in kifar da wa]annan manyan duwatsun a kansu ? sai Annabir yace :a’a kada ayi musu haka, saidai ina fatar Allah zai fitar daga tsatsonsu wa]anda zasu bauta wa Allah shi ka]ai kuma bazasu masa tarayya da komai ba ». [ Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi].
Kuma Annabir ya kasance yana fita a mausimi(duk lokacin da za’ayi wani taro na musamman) don ya bijirar da da’awarsa ga {abilun larabawa yana cewa :Waye zai bani mafaka ?. Waye zai taimake ni ?, domin {uraishawa sun hana ni isar da sa}on ubangijina ! ».
A lokacin mausimi, Annabir sai ya ha]u da mutane shida daga cikin mutanen Madinah a gurin da ake }ira Aqabah, ya }ira su izuwa ga musulunci sai suka musulunta, sai suka koma Madinah suka cigaba da }ira, har musulunci ya watsu a garin Madinah. Sannan akayi mubaya’ar Aqaba ta farko da ta biyu dukkansu a ~oye, lokacin da aka umarci Annabir da wa]anda suke tare dashi dayin hijira zuwa Madinah,sai suka fita ]aya-bayan-]aya.
12. HIJIRAR ANNABIr ZUWA MADINAH :
Sai Annabir da Abubakar(R.A) suka nufi kogon Saur suna masu hijira zuwa Madinah, suka zauna cikin kogon tsawon kwanaki uku, don haka labarinsu sai ya ~ace wa {uraishawa. Lokacin da Annabir da Abubakar suka shiga Madinah, sai mutanen garin suka kar~e su hannu bibbiyu, sai Annabir ya gina masallacinsa da masau}insa.
13. YA}U}UWAN DA ANNABIr YAYI A RAYUWARSA:
An kar~o hadisi daga Ibn Abbas(Allah ya }ara masa yarda) yace: ”lokacin da Annabir ya fita daga garin Makka yana mai hijira, sai Abubakar(R.A) yace: wa]annan mutane ({uraishawa) sun shiga uku sun lalace!! Ta yaya za’ayi su fitar da Annabinsu daga garinsa!! Sai Allah ma]aukakin sarki ya sau}ar da fa]insa : « An yi izini ga wa]anda ake yakarsu da cewa lalle an zalunce su, kuma lallai hakika Allah mai iko ne kan taimakonsu ».[suratul Hajji, Aya :(39)]. Itace aya ta farko data sau}a tana umarni da ya}i. Ya}u}unan da Annabir yayi a rayuwarsa guda Ashirin da bakwai(27) ne, wa]anda ya}i ya faru a cikinsu guda tara(9) ne, gasu kamar haka :
1.Badr. 2.Uhud. 3.Muraisi’i. 4.Khandaq. 5.Bani-{uraiza. 6. Khaibar. 7. Fathu-Makka. 8. Hunain. 9. A]]a’if.
Kuma ya aika Sariyyah(rundunan ya}i }ar}ashin jagorancin wani sahabi) guda hamsin da shida(56).
14. HAJJIN ANNABIr DA UMARARSA :
Annabir bai yi hajji ba bayan hijirarsa zuwa Madinah sai hajji guda ]aya wadda shine ake }ira Hajjatul-wada’i(wato hajin ban-kwana). Annabir yayi umara ne sau hu]u (4) a rayuwarsa, dukkaninsu cikin watan Zul-{a’ada ne banda wacce yayi tare da hajinsa, gasu kamar haka :
1.Umarar Hudaibiyya(wacce kafurai suka hana shi shiga garin Makka). 2. Umarar {ada’i. 3. Umarar Ju’uranah. 4. Umarar da yayi tare da hajinsa.
15. SIFFOFIN ANNABIr :
Annabir ya kasance mutum ne madaidaici, kuma ya kasance fari ne mai ha]e da ja, yana da gashi mai yawa, mai tsananin ba}in ido ne, kuma ya kasance ba yi da gashin da ya lullu~e gaba ]aya kan }irjinsa da cikinsa, yana da gashi a tsakiyar }irjinsa da cikinsa.
16. HALAYEN ANNABIr :
Annabir shi yafi kowa kyauta, da fa]in gaskiya, da taushin hali, da iya zamantakewa, Allah ma]aukakin sarki yace: “ kuma lallai hakika kana kan halayen kirki ma]aukaka”.[suratul {alam, Aya:(4)]. Kuma Annabir yafi kowa jarunta da kamewa da }an}an-da-kai, kuma ya kasance mai matu}ar kunya ne fiye da budurwa a tarbukanta, ya kan kar~i kyauta kuma yayi sakamako akai, amma baya kar~ar sadaqa kuma baya ci, kuma ya kasance ya kanyi fushi idan an keta ha}}in Allah ma]aukakin sarki, amma baya fushi idan an keta ha}}insa, kuma ya kasance yakan ci gwargwadon abinda ya samu, baya }i ko mayar da abinda Allah ya bashi, kuma baya }wa}}wafi da bi-biyan abinda bai bashi ba, kuma ya kasance baya cin abinci a kishingi]e ko akan teburi, kuma ya kasance watanni uku sukan shu]e a gidansa ba a ]aura tukunya akan murhu ba don girka abinci, kuma ya kasance yana zama da talakawa da miskinai, yana kuma ziyartan marasa lafiya, kuma ana zuwa ma}abarta dashi.
Annabir ya kasance ya kanyi raha amma baya fa]in }arya cikinsa, kuma baya }yal}yalewa wajen dariyarsa( wato murmushi yake yi), kuma ya kasance mai hidima ne ga iyalensa, yace: “ mafi alkhairin cikinku shine wanda yafi ku kyautata wa iyalensa, nine kuwa nafi ku kyautata wa iyalaina”.[Tirmizi ne ya ruwaito shi, Albani kuma ya ingantashi]. Anas bn Malik(R.A) yace: “ nayi yaron gida wa Annabir tsawon shekara goma(10), amma bai ta~a zargi na ba kan wani abu dana aikata kan cewa; don me na aikata kaza? Ko kuma kan wani abu da ban aikata ba cewa; don me baka aikata kaza ba?!!.
Annabir bai gushe ba yana tausasa wa dukkanin halitta, yana kuma nuna musu ayoyi da abubuwan gagara-koyo da suke nuni akan manzancinsa,daga ciki akwai kamar: tsagewar wata (lokacin da {uraishawa suka nemi shi da yayi addu’a hakan ya faru), ~u~~ugar ruwa daga tsakankanun yatsunsa, nusantawar da kututture yayi masa(lokacin da Annabir ya bar tsayuwa akansa don hu]uba), kawo kukan da Ra}umi yayi gurinsa, bugu da }ari kuma; ya bada labarin abubuwan gaibu da zasu faru sai suka faru kamar yadda ya fa]a, d.ss.
17. FALALAR ANNABIr:
An kar~o hadisi daga Jabir ]an Abdullah(R.A) cewa Annabir ya ce: an bani wasu abubuwa guda biyar wa]anda ba a ba dasu ba ga wani Annabiu da yazo gabanina: (1). an taimake ni da tsorata abokan gaba wa]anda tsakanina dasu akwai nisar tafiyar wata guda. (2). an sanya min }asa ta zamo tsarkakakkiya (wajen yin taimama) kuma gurin sallah, don haka; duk wanda sallah ta riske shi a hanya sai ya tsaya yayi. (3). kuma an halattamin cin ganima wacce bata halttaba ga wani Annabi daya zo gabanina. (4). an bani damar yin ceto( a farfajiyar {iyama). (5). Annabawan da suka zo gabani na sun kasance ana aikosu ne zuwa ga mutanensu kawai; ni kuwa an aiko ni ne zuwa ga mutane baki ]aya”. [Bukari da Muslim ne suka ruwaito shi].
Ya zo a cikin sahihu-Muslim a hadisin Anas(R.A) cewa Annabir yace: “Ni ne farkon wanda zai fara yin ceto ranar {iyama, kuma nafi dukkan Annabawa samun mabiya ranar {iyama, nine kuma zan fara }wan}wasa }ofar Aljanna don a bu]e”. Ya zo a hadisin Abu-huraira (R.A) cewa Annabir yace: “Ni ne shugaban ‘yan-Adam ranar {iyama, kuma ni ne farkon wanda zai fara fitowa daga kabari ranar {iyama, ni ne kuma farkon wanda zaiyi ceto,kuma farkon wanda za’a bashi damar yin ceto”.
18. IBADAR ANNABIr DA SALON RAYUWARSA:
A’ishah (Allah ya }ara mata yarda) tace : Annabir ya kasance yakan yi sallar dare har }afafuwansa su kumbura su tsatstsage, sai aka ce masa ; Annabir don me kake haka bayan kuwa an gafarta maka zunubanka?!! Sai yace : to ai ya dace in zamo bawa mai godiya(kan ni’imomin da akamin).[Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi]. Ta cigaba da cewa : kuma shimfi]ar Annabir da yake barci akai fata ne wadda akayi masa cushe da tankan dabino. Ya zo a hadisin Ibn Umar(R.A) yace : ha}i}a naga Annabir yana kai-kawo bai samu abinda zai sa a ma}oshinsa ba, duk abinda ya rasa baya damunsa matu}ar na duniya ne, duk da cewa shine shugaban duniya gaba ]aya.
Muna godiya ga Allah ta’ala daya sanya mu cikin al’ummarsa, kuma yayi mana gam-da-katar dayi masa biyayya, kuma muna ro}on Allah ya tasar damu ranar {iyama cikin masu bin littafinsa da sunnarsa. Amin summa Amin.
MUHIMMAN ABUBUWAN DA SUKA
FARU A RAYUWARSAr:
ü Isra’I da Mi’iraji(tafiyar da akayi dashi zuwa masallacin {udus da hawa da akayi dashi zuwa sama) : ya faru ne kafin ayi hijira zuwa Madinah da shekara uku, a lokacin ne aka farlanta salloli.
ü Shekarar farko bayan hijira: hijira zuwa Madinah, gina masallacinsa, fara }o}arin kafa daular musulunci, farlanta Zakka.
ü Shekara ta biyu: Ya}in Badr babba,(a cikinsa ne Allah ya ]aukaka muminai ya kuma ]orasu akan abokan gabansu).
ü Shekara ta uku: Ya}in Uhud ; a wannan ya}in ne musulmai suka samu rauni saboda sa~awar da wasu daga cikinsu sukayi wa karantarwan Annabir da shagaltuwa wajen ]iban ganima.
ü Shekara ta hu]u : ya}in Banin-Nadiir; a wannan ya}in ne Annabir ya fitar da yahudawan Banin-Nadiir daga Madinah saboda warware al}awari da sukayi.
ü shekara ta biyar: ya}in Banil- Mus]alaq, ya}in Ahzab, ya}in Bani- }uraiza.
ü shekara ta shida: sulhun-Hudaibiyya, kuma a wannan shekarar ne aka haramta giya har abada.
ü shekara ta bakwai: ya}in Khaibar, a wannan shekarar ne Annabir da musulmai suka shiga garin Makka sukayi umara, kuma a shekarar ne ya auri Safiyyah ‘yar Huyayyi.
ü shekara ta takwas: ya}in Mu’uta(tsakanin musulmai da Rumawa), fathu- Makka, ya}in Hunain(tsakanin musulmai da {abilun Hawaz da sa}iif).
ü shekara ta tara: ya}in Tabuk; wannan shine ya}i na }arshe da Annabir yayi a rayuwarsa, kuma a wannan shekaran ne mutane suka zo gurin Annabir suka shiga musulunci }ungiya-}ungiya, shi yasa ake }irar wannan shekarar “shekarar wufudi”.
ü shekara ta goma: hajin ban-kwana, a shekarar ne Annabir yayi haji tare da musulmai sama da dubu ]ari.
ü shekara ta goma sha ]aya: a farkon wannan shekarar ne Annabir ya rasu, ya rasu ne ranar litinin cikin watan Rabi’ul- Awwal duk da cewa anyi sa~ani wajen }ididdige kwanan watan. Annabir ya rasu ne yana da shekara sittin da uku (63) a rayuwarsa, Arba’in (40) daga ciki kafin ya zamo Annabi, ashirin da uku(23) kuwa yana annabi kuma manzo, shekara goma sha uku (13) daga ciki yayi su ne a Makka, sauran goman (10) kuma a Madinah (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da alayensa da sahabbansa).
Ya ‘yan’uwa musulmai!! Ku duba irin wannan rayuwa ta Annabir !Shin haka rayuwarmu take?!!Ko dai bamu sakankance bane cewa wannan annabi shine annabin da aka aiko mana ?!! ku tuna da fa]in Allah ma]aukakin sarki da yake cewa : « Hakika kuna da abin koyi mai kyau game da manzon Allahr…… ». [suratul Ahzab, Aya :(21)]([1])
* * *
BAYANIN WURAREN DA AKA CIRO
MAGANGANU:
“Tahzibulasma’Iwallugaat” na Imam Nawawi.
“Attabsiratu-walhada’iq” na Imam Ibnul Jauzii.
“Zadul-Ma’aad” na Imam Ibnul {ayyim.
« Assiratun-nabawiyya » na Imam Azzahabi.
“Jawami’is-siratin-nabawiyya” na Imam Ibn Hazm.
“Alfusul fi siratir-rasul” na Imam (Ibn Kasiir).
“Sahihus-siratin-nabawiyya” na Ibrahimul- Alii.
Mai fassara: Muazu Abba Jabir
(1) baya daga cikin maganar mawallafin.
**{Legacy activities, comments etc counter: 3265; topic series: 8; forum: MediaHausa; legacy score: 8; legacy ratings: 2; rating_ip: ***.*14.31.188; associated: 8- /*}