Topic: Ilimin Falaki da kamawar watan Ramadan na bana
Timeline: 2010-10-05 19:52:56
Ilimin Falaki da kamawar watan Ramadan na bana
A Rubuce Da Muhammad Sani Isa
Kasancewar watan Ramadan ya kusato, ga kuma jayayyar da sanarwar ganin wata ke haifarwa, ya sa muke gabatar da wannan dan bincike don nuna cewa, ilimin falaki zai iya taimakawa a samu saukin wannan takkaddama.Shi lissafin falaki ilimin kimiyya ne wanda yake tabbas wanda za a iya sanin wuri da hali da kuma matsayin da wata da sauran duniyoyin samaniya suke ciki a kodayaushe. Za a iya tantance rana da lokacin da za a haifi jinjirin wata. Haka nan za a iya tantance yiwuwar ganinsa da awanninsa da haihuwarsa a lokacin magariba da lokacin da wata zai fadi da tazara tsakanin faduwar rana da faduwar wata da sauran bayanai. Bisa wadannan tarin bayanai, za a iya magancen kuskure da kuma karyar ganin wata. Hasali da ma can, tsarin ganin wata a matsayin hanyar sanin kamawar watannin musulunci an shar’anta shi ne saboda rashin rashin samuwar ilimin lissafin falaki a cikin al’umma a zamanin Annabi (SAW). Domin a hadisin da Bukhari da Muslim suka rawaito, Annabi (SAW) ya ce, “Mu al’umma ce wacce ba ta iya karatu da rubuta da Iissafin falaki ba, don haka, ku dauki azumi idan an gan shi, ku ajiye idan an gan shi. Idan an lullube muku shi, ku cika adadin Sha’aban kwana 30.”
Wannan hadisi ya nuna cewa da akwai masu ilimin lissafin falaki a zamanin Annabi (SAW) da maganar aiki da ganin wata ba ta taso ba, kuma ganin wata rahusa ne sakamakon rashin masu ilimin falaki a cikin al’umma. Lokacin da ilimin falaki ya samu a wannan al’umma, ya kamata wannan rahusa ta daina aiki. Kamar rahusa ne yin taimama sakamakon rashin ruwa da zarar an samu ruwa, damar yin taimama ta kau. Rahusa tana gushewa ne da gushewar hujjar da ta jawo aiki da wannan rahusa. Ya kamata mu yi la’akari da cewa, ba ana aiki ne da tsarin ganin wata a karan kansa ba, makasudi shi ne sanin kamawa da mutuwar watannin Musuluci. Idan za a cimma wannan manufa ta wata hanyar da shari’a ta yarda da ita, ya kamata a rungume ta.
Bugu da kari, a hadisin da Muslim ya rawaito daga Nawwas Bin Sam’an game da Dujal, Annabi (SAW) ya ce, lokacin da Dujal ya bayyana zai yi kwana 40 a duniya; ranar farko tsawon shekara guda, rana ta biyu tsawon wata guda, rana ta uku tsawon mako guda, sauran kwanakin kamar sauran kwanaki. Da suka tambayi Annabi (SAW), shin sallar kwana guda ta wadatar a rana mai tsawon shekara? Sai ya ce, Sallah biyar ba za su wadatar ba, ku kiyasta lokacin kowace Sallah. Wannan ya nuna cewa, al’umma za ta samu ilimin falaki daga baya, kuma wajibi ne su yi aiki da shia lokacin.
Idan mun dawo kan watan Ramadan na bana, lissafin falaki ya tabbatar da cewa, iktiranin wata wanda rana da wata da duniya sukan jeru wannan bisa wannan, wata na tsakanin rana da duniya; daidai wannan lokaci ne ake haihuwar sabon wata, zai faru ne a ranar 10/08/2010 da karfe 4 da minti 8 na asuba. Ran nan rana za ta fadi da karfe 6 da minti 48 na yamma, wanda ya nuna cewa, wata yana da awa 14 da minti 20 da haihuwa, don haka yayi kankanta ba zai ganu da ido ba a ko ina a Najeriya ba. Jinjirin wata yana bukatar akalla awa 17 zuwa 20 da haihuwa kafin ya ganu da ido. Koda yake za a iya ganinsa da na’urar hangen nesa a Kudancin Najeriya, amma ba zai ganu a Arewa ba ko da na’urar ce.
**{Legacy activities, comments etc counter: 2118; topic series: 3; forum: MediaHausa; associated: 3- /*}