Topic: Da Takarar Wani Gara Buhun Karara
Timeline: 2010-11-18 15:51:25
Da Takarar Wani Gara Buhun Karara
A Rubuce Da Saratu Muhammad Kurna Babban Lay
Haka Allah Yake al’amarinsa. Iskar bazarar siyasa ta fara kadawa da karfinta, wani lokaci ta huro zafi wani lokaci kuma ta huro sanyi, har wuta take kunnowa. Idanuwan jama’a da yawa sun rufe, musamman wadanda aka fi sani da ‘yan siyasa. Da yawa daga cikin ‘yan siyasa ba sa gani a wannan lokaci, don ba abin da suke so a yanzu sai dai ka gaya musu kana son su, ko da kuwa karya ne sai su dauko abin sayan kashin miya su ba ka.
Domin sun san cewa idan suka ba ka, kai kuma sai ka ba su kuri’arka. Idan kuwa har suka samu damar dare wannan wawakekiyar kujerar, a hankali za su fanshe abin da su ka ba ka, har ma su ninka ninkin baninki. Kuma ko ka ki ,ko ka so, ba ruwansu da kai.
‘Yan takara da yawa sun fito, kowannensu yana ta kokarin ya ga ya sami jama’a daga kowane bangare na al’umma. Wadanda suka hada maza da mata da ma’aikata da matasa da ‘yan mata da dalibai da kowa da kowa. Abin mamaki, wasu daga cikin masu fitowa takara kowa ya san su, shahararrun ‘yan damfara ne, macuta kuma azzalumai. ‘Yan handuma da babakere da katon wuya, ko bera nan ya gansu ya kyale. Amma su ne za su fito cikin mutane ko kunya ba sa ji, su zo su ce a zabe su. Mu kuma da yake ruwa ya ciyo mu ga yunwa, mutum ya gama kashe mu sai mu zo mu ba shi damar ya mulke mu. Daga nan, ko kabari mai kyau ba za mu samu ba, yawancinsu haka suke mugaye, kuraye ne da fatun awaki. Kai, sun ma fi kuraye, domin ita kura ba ta cin kai, amma su ta kan su ke farawa. Don haka ya kamata mu yi hattara da su. Kamata ya yi idan sun fito a yi musu ihu, a gaya musu ba su isa ba, amma abin mamaki idonsu ya rufe, mu kuma idon mu da hankalin mu ya gushe.
Ba duka aka taru aka zama daya ba, daga cikin dubu, za a iya samun goma masu kirki. Idan ma mutum ya ce duka ba su da kirki, to bai yi wa kansa adalci ba. Domin halayyarmu ce ka ji wani ya na cewa, “ai yanzu duk mutane ba su da mutunci”, to duk mai fadar haka shi ne babban mara mutunci. Domin kuma ko addininmu bai yadda da wancan wawan zancen ba. Saboda haka dai a cikin ‘yan takara za a iya samun nagari, wadanda ba don kudi, ko don holewa da fantamawa su ka fito ba.
Daga cikin takarar da ta dauki hankalina ita ce, takarar wani dan boko, wanda ya fito takarar gwamnatin jihar Kano a karkashin sabuwar jam’iyyar CPC, wato Dokta Auwal Anwar. Wannan dan takara ya bayyana cewa shi fa a gaskiya ba wani ne ya ce ya fito takara ba. Sabanin yadda wasu mahandama suke yi, sai su turo wani dan korensu kafafen yada labarai ya zo ya ce wai talakawa ne suke son wane ya fito, alhalin karya ne talakawa ba su ma san shi ba. Don haka, shi dai Dokta ya fada a fili cewa shi dai shi ya ga dama ya fito, ya fito ne don ya yi bakin kokarinsa wajen kawo abubuwan ci gaba ga al’umma.
Wannan dan takara ban san shi ba, amma dai na taba halattar wani taro da aka gabatar a Jami’ar Bayero a dakin taro mai kujeru dubu, wanda ni a wannan lokaci ba don shi na je ba, na je ne don in saurari laccar malamin da na sani malami ta Dokta Salisu Shehu. Sai aka yi gamon katar na tsaya na saurara. Tun wancan lokaci na kwallafa rai na wajen ganin na sami laccar da Dokta Auwal, amma da kyar da jibin goshi na samu a wajen wani babban farfesa.
Dokta Auwal Anwar, a gani na da irin yadda na ga yanayinsa ina yi masa zaton alheri. Duk da ban san shi ba, amma Hausawa suna cewa Juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta. Lallai mutum ne haziki idan mutum ya ji maganganunsa, kuma mutum ne da ya karantu domin ya dade yana koyarwa a jami’ar Maiduguri, sannan kuma ya koma Abuja inda a can ma ya rike mukamai da dama.
Akwai masu ra’ayin cewa, su malaman jami’a da suke son shiga harkar siyasa, ai da ma can a yunwace suke, dama kadai suke nema su je su ci gaba da turanci suna sace dukiyar al’umma. Wannan hasashe ne kawai, domin idan mai ilimi ya yi zalunci ya san ya yi, amma jahili kuwa zai zalunce ka ne, kuma ya yi dariya. A karshe ma ya sauya unguwa ya koma Abuja ko Nasarawa ya barka a nan inda kake ka na hamma.
Har ila yau, idan mutum ya tsaya tsai, tsayuwar tsayin daka, zai gane cewa hatta irin yadda ake kamfe, na yada manufar wannan bawan Allah, hanya ce ta ilimi. Kai ko alluna da ake yi a like hotunansa ma kawai idan ka duba, za ka ga ana amfani da ilimi wajen sanin gurbin da ya kamata a manna ko a kafa su. Ba kawai kai tsaye ake zuwa a dankara su a ko’ina ba, yadda za su bata gari kuma su dami mutane.
Wani kalubale da ke gaban wannan Dokta shi ne, shi da kansa yana fada a wajen kamfe dinsa cewa, aikin da ya yi a jihar Kano ba zai wuce na shekara daya kawai ba, to hakan ba zai zame masa illa ba, ta wajen rashin sanin hakikanin matsalolin da ke damun Kanawa. Gwamnatocin Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da Dokta Shekarau duk sun yi kokari irin nasu don kawo walwala da ci gaba ga jama’a, to amma dai har inda muke yau akwai kalubale mai yawa ga al’ummar jihar Kano.
Kadan daga cikin sun hadar da rashin ruwa, rashin wuta rashin ingantaccen tsaro, rashin isassun makarantu da malamai da rashin isassun asibitoci, da likitoci, ga mutuwar ma’aikatu, ga cin hanci da rashawa, ga rashin aikin yi, ga shaye-shayen miyagun kwayoyi, ga barna da dukiyar al’umma, ga dan kasuwancin da ake tutiya da shi, shi ma sai kara baya-baya yake yi, ga wulakantar da harkar noma da kiwo, ga zaluncin shugabannin al’umma, tun daga kan manyan jami’an gwamnati, da ‘yan majalisu da ciyamomi da kansiloli. Wasunsu ma tamkar ba su san aikinsu ba, kawai su karbi albashi ko kwangila, su yi shashanci, ba ruwansu da harkar al’umma.
Fatanmu dai, Allah ya zaba mana na gari, domin za ka iya ganin wani a matsayinsa na mai mutunci, amma daga zarar ya dare kujera, sai kansa ya guntule na jaki ya hau. Amma dai duk da haka idan mutum yana da kyakkyawar manufa, bai kamata a yi masa mummunan zato ba, kamata ya yi a karfafe shi da addu’a da maganganu masu kyau, har Allah ya kai mu ga gaci. Wannan dan takara Dokta Anwar ga alama ya yi!
Don haka mu yi addu’ar Allah ya sa yana da alheri. Domin kamar yadda ya fada da bakinsa, idan ya fito ne domin ya zalunci talakawa, ya Allah Ya hana shi, idan kuma ya fito ne don ya taimaki talaka, ya Allah Ka ba shi, Ka taimake shi amin.
Saratumuhammad@gmail.com
**{Legacy activities, comments etc counter: 839; topic series: 4; forum: MediaHausa; associated: 4- /*}