Topic: Bijirewar Ganin Wata: Babbar Barzana Ga Hadin Kan Musulmin Najeriya (2)
Timeline: 2012-03-27 18:16:10
Bijirewar Ganin Wata: Babbar Barzana Ga Hadin Kan Musulmin Najeriya (2)
A Rubuce Da Muhammad Sani Isa, Kano
Bugu da kari kan cewa, tun daga zamanin Shehu Usman dan Fodio; Sarkin musulmi ne jagoran musulmin Daular Usmaniyya. A taron da malamai da aka yi a Kaduna a zamanin Firimiyan Jihar Arewa, Alhaji Sa Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, Allah Ya gafarta masa, an dora wa Sarkin Musulmi nauyin tantancewa da sanar da kamawar wata da ranakun daukar azumi da ajewa da idi da makamantansu. Da aka kafa majalisar koli ta kula da harkokin Musulunci ta Najeriya (Nigerian Supreme Council for Islamic Affairs), kasancewar Sarkin Musulmi ne shugaban wannan majalisa, aikinsa ya hade dukkan musulmin Najeriya.
Dangane da haka ne, bisa dogaro da rahotannin da Sarkin Musulmi ya samu daga sauran Sarakuna, kuma kamar yadda Shari’ar Musulunci ta tsara, sai ya ba da shelar cewa, an tabbatar an ga wata, don haka rana kaza ce 1 ga wata.
Kasancewar ana samun sabanin ranakun dauka da ajiye azumin Ramadan duk shekara, gami da cewa, wannan sabani gagarumar illa ce ga hadin kan musulmi, shin akwai wata hanyar da za a iya inganta hanyar tantance tsayuwar watanni ta yadda za a magance wannan sabani da rarrabuwar kai? Shin akwai hanyar da za a gano kuskure ko daidai din ranakun da Sarkin Musulmi yake tsayarwa? Bisa wace hujja ake bijire wa umurnin Sarkin Musulmi da yin tawaye game da ganin wata? Shin Shari’ar Musulunci ta ba wani mutum ko wata kungiya damar yin gaban kanta wajen dauka da ajiye azumi da yin idi da layya?
Hanya mafi inganci ta tantancewa da kuma hasashen kamawa da mutuwar farin wata, ita ce ta hanyar amfani da Ilmin Falaki, wanda ya ginu ne a kan Kitabu (Alkur’ani) da Sunnah (Hadisi). Ilmin falaki yana bin diddigi da kididdigar lissafin tafiyar rana da wata da sauran duniyoyin sama jannati da kuma dangantakarsu da juna a kodayaushe; kasancewar tafiyar rana da wata da duniyoyi an tsara su a kan ilmin lissafi kamar yadda Ayoyin Alkur’ani Mai Girma suka nuna. Wadannan ayoyi sun hada da: Suratur Rahaman Aya ta 5; Suratu Ibrahim Aya ta 55; Suratu Ya Sin Ayoyi na 39 da 40; Suratu ‘An’am Aya ta 96; Suratu Yunus Aya ta 5 da makamantansu.
Don haka, ilmin falaki ilmi ne na lissafin sanin wuraren da rana da wata da taurari suke, da matsayin da suke ciki, lokacin hudowarsu da faduwarsu, lokacin kamawarsu da mutuwarsu da sauran bayanai na dabi’unsu. Kasancewar ba sa kaucewa daga wannan tsari da Allah Ta’ala ya aza su a kai, za a iya, ta hanyar lissafi, sanin dukkan bayanai game da wadannan halittu. Ta wannan hanya ake sanin lokutan sallah ba tare da an dubi rana ba.
Haka nan wata, za a iya lissafin ranar da za a haife shi, da ranar da zai ganu da ranar da ba za a iya ganinsa ba. Haka nan ana iya sanin lokacin hudowarsa da faduwarsa ko da ba zai ganu da ido ba.
Rana da wata suna tafiya a bisa lissafi da tsarin da Allah Ta’ala Ya dora su a kai, ba su da ikon sabawa, kamar yadda ayoyi suka yi bayani. Wannan ilmi ake amfani da shi wajen aika taurarin dan Adam zuwa duniyar wata da sauran duniyoyin sama, domin an san gudunsu da hanyar da suke bi, don haka idan an harba kumbo, sai kumbon su yi magami da duniyar da wannan kumbo ya nufa.
Dangane da watan Ramadan na 2011, Ilmin Falaki ya tabbatar da rashin yiwuwar kamawar watan ranar Lahadi (31/07/2011), domin, a wannan ranar, ba a haifi watan ba; kuma tsohon watan Sha’aban bai mutu ba; kuma ranar Asabar na daga cikin kwanakin boyon watan Sha’aban. Allah SWT Ya tsara cewar, kowane karshen wata, wata zai yi boyon kwana daya ko biyu kafin sabon wata ya kama. Watan da zai cika kwana 30, zai yi boyon kwana biyu; watan da zai yi kwana 29, zai buya kwana daya. Larabawa da malaman Musulunci suna kiran kwanakin boyon wata; Ayyamul Mihak, ko Ayyamus Su’al ko Ayyamul Istitar.
Malamai a wajen tafsirin ayoyin da suka yi magana game da tsarin tafiyar wata, kamar su Abdullahin Gwandu sun ce, wata yana da manzilai ko masaukai ko matakai 28, wata yana kwana daya a kowane manzili, daga nan sai ya buya kwana daya ko biyu, kafin ya mutu sabon wata ya kama. Duba tafsirin Suratu Ya Sin, Aya ta 39, da Suratul ‘An’am Aya ta 96 da kuma Aya ta 5 ta Suratu Yunus.
Misali, a cikin littafinsa na tafsiri mai suna Diya’ut Ta’awil, Abdullahi Bin Fodiyo ya ce, wata yana da manzilai 28 wadanda yake bi a cikin kwanaki 28 a kowane wata, daga nan sai ya buya dare 2; idan watan mai kwana 30 ne, ko kwana 1; in watan mai kwana 29 ne.
A cikin Majmu’ul Fatawa, Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, ya ce, Iktirani yana faruwa ne bayan boyon tsohon wata kafin bayyanar (haihuwar) sabon wata; domin wata yana tafiya ne a tsakanin manzilai 28 wanda Allah Ya tsara shi a kai. Bayan ya gama zagaya wadannan manzilai, sai wata ya je kusa kusa da rana, sai ya bace kwana 1 ko 2 saboda jeruwarsu (gwamuwarsu) da rana; lokacin da ya sake bayyana daga karkashin rana, sai Allah Ya haskaka shi, daga nan ya yi ta kara haske da girma, yana kara nisantar rana, haskensa na karuwa har sai sun zo kankankan shi da rana a daren 14, daga nan sai haskensa ya yi ta raguwa yayin da yake kara kusantar rana har sai sun sake Iktirani (gwamuwa).
Daga cikin Ayoyin da suka yi magana a kan tsarin da Allah Ta’ala Ya dora rana da wata a kai, akwai tsere da suke da juna; wannan ya wuce wannan. A cikin Aya ta 1 da ta 2 na Suratus Shamsi, Allah SWT Ya ce:
‘Na rantse da rana da kuma hantsinta. Na rantse da wata yayin da yake biye da ita’.
Malaman tafsiri sun ce; “yayin da yake biye da ita’’ shi ne cikin kwanaki 15 na farkon kowane wata; bayan an haifi sabon wata ya kasance yana biye da rana; sai bayan ta fito zai fito, kuma sai bayan ta fadi zai fadi. Daga (ranar) 16 ga wata, sai wata ya karbi gaba, rana na biye, har zuwa karshen wata. Daga nan sai rana ta sake karbar gaba; haka suke yi tun daga lokacin da Allah Ya halicce su har zuwa tashin kiyama. Duba littattafan tafsiri kamar Safawatut Tafasir na Sabuwniy.
**{Legacy activities, comments etc counter: 1272; topic series: 6; forum: MediaHausa; legacy score: 9; legacy ratings: 2; rating_ip: ***.*14.31.188; associated: 6- /*}