Topic: Maraba da Shekarar 1433 BH: Nazari kan shekarar Musulunci da hijira (1)
Timeline: 2012-03-27 18:49:11
Maraba da Shekarar 1433 BH: Nazari kan shekarar Musulunci da hijira (1)
A Rubuce Da Salihu Is’hak Makera
Al’ummar Musulmi, assalamu alaikum, barkanmu da wannan lokaci, muna fata Allah Ya sanya mu kasance a fadake cikin dukkan al’amuran da muke gudanarwa ta yadda za mu koma ga Allah muna masu imani. Bayan haka ga wadanda suka dauki addini da muhimmanci suna sane da cewa a gobe Asabar ne cikin yardar Allah za mu shiga sabuwar shekara ta 1433 Bayan Hijirar Manzon Allah (SAW).
Kuma a kokarinmu na tunatar da kanmu muhimmancin wannan rana muke gabatar da wani dan bincike kan hijirar da wadansu al’amura da suka shafe ta. Muna fata dan abin da za mu gabatar zai amfane mu a duniya da Lahira:.
Muharram: Ma’ana da bayani:
Muharram (Mai alfarma) ko watan Muharram (wata mai alfarma) shi ne watan farko na shekarar Musulunci. An kira shi da wannan sunan ne saboda a Jahiliyya Larabawa sun kasance suna haramta yaki a cikinsa. Kuma jam’insa shi ne muharrimati ko muharimu ko maharimu (da ya a tsakanin ra’un da mimun). (Subhu Al-A’ashiy, Mujalladi na 2 shafi na 401 da Lisanul Arab, Mujalladi na 2 shafi na 845).
Larabawa a zamanin Jahiliyya duk da abin da suke kai na bata da kafirci suna girmama shi wannan wata tare da sauran watanni masu alfarma, suna haramta yaki a cikinsu ta yadda da mutum zai hadu da wanda ya kashe mahaifinsa ba zai fada masa da fada ba, har zuwa lokacin da suka kirkiro salon nan na nasi’a, wato jinkirtawa, inda suka kasance suna jinkirta alfarmar wani watan zuwa wani wata na daban domin su halatta yaki a cikin watanni masu alfarma.
Ana jinigna sunan watan Muharram ga Allah a ce: Watan Allah Mai alfarma.
Idan aka ce mene ne hikimar jingina shi ga Allah Madaukaki alhali daukacin watanni dukkansu na Allah ne? Sai a ce: “Hakan yana nufin don ya kasance cikin watanni masu alfarma da Allah Ya haramta yaki a cikinsu ne, kuma saboda kasancewarsa wata na farko a shekara sai aka yi masa idafa na musamman. Kuma bai inganta daga Annabi (SAW) cewa an jingina wani wata daga cikin watanni zuwa ga Allah ba, face watan Allah na Muharram.” (A duba kalaman Abul Fadli Al-Iraki kamar yadda ya zo a Hashiyar Suyudi kan Sunnani Nisa’i, Mujalladi na 3 shafi na 206).
Kuma an ce: “Ana idafa (jingina shi) ga Allah ne don girmamawa gare shi.” (Lisanul Arab, Mujalladi na 2 shafi na 845).
Larabawan farko (Al-Aribah) suna kiransa da Al-Mu’utamir, cirowa daga kalmar amirar kaumi iza kasiru. Ma’ana suna haramta yaki a cikinsa sai su yawaita. An kuma ce an cizgo ne daga Al-I’itimar. Ma’ana ana umarni a cikinsa da barin yaki. Kuma ana jam’insa da Mu’utamirat da Ma’amir da Ma’amir (da ya a tsakanin mimun da ra’un).” (Subhu Al-A’ashiy, mujalladi na 2 shafi na 405).
Abin da ya zo na azumin Muharram:
An karbo daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mafi falalar azumi bayan Ramadan shi ne na watan Allah Al-Muharram. Kuma mafi falalar Sallah a bayan farilla sallar dare.” (Muslim ya fitar da shi a babin azumi, Hadisi na 1163)
Annawawi ya ce: “Fadinsa (SAW) cewa: “Mafi falalar azumi a bayan Ramadan shi ne na watan Allah Al-Muharram” yana nuni ne da cewa shi ne mafi falalar watanni ga yin azumi.” (Sharhin Sahihul Musulim, Mujalladi na 8 shafi na 55).
Asshaukani kuma ya ce: “A cikinsa (Hadisin) akwai dalilin cewa mafi falalar azumin tadawwu’i shi ne azumin watan Al-Muharram. Kuma Hadisin Anas na wurin Tirmizi bai warware shi, wato Hadisin da ke cewa: “An tambayi Manzon Allah (SAW) wane azumi ne mafi falala a bayan Ramadan? Sai ya ce: “Sha’aban domin girmama Ramadan.” (Tirmizi a babin zakka hadisi na 663. Kuma ya ce, wannan hadisi gari bi ne. Sadakatu Bin Musa ba mai karfi ba ne a wurinsu). Saboda a cikin isnadinsa akwai Sadakatah Bin Musa kuma shi ba mai karfi ba ne.” (Nilul Audar, Mujalladi na 4 shafi na 241-242).
Amma Ibn Rajab ya fassara hakan da cewa, azumtarsa (Muharram) ya fi falala a mudalakin tadawwu’i (yanke), saboda fadinsa (SAW): “Mafi falalar Sallah bayan wajibabbu na tsakar dare.” Sai ya ce: “Babu shakka salloli ratibai sun fi falala. To abin da yake nufi da fiffikon falala a cikin Sallah da azumin mudalaki ne. Ya ce: “Azumin Sha’aban ya fi falala daga azumin Muharram, domin shi kamar ratibi ne tare da na farillai. Ya ce sai ya bayyana tadawwu’i shi ne abin da ya kasance a kusa da Ramadan a gabaninsa ko a bayansa, wancan (azumin Sha’aban) yana ta’allake da zumin Ramadan sabosa kusancinsa da shi, kuma shi ne magana mafi bayyana.” (Lada’iful Ma’arif).
Sheikh Ibn Usaimin ya ce: “Malamai sun yi sabani kan wanne ne mafi falala: shin azumin watan Muharram ne ko azumin watan Sha’aban? Sai wadansu malaman suka ce watan Sha’aban ne mafi falala, domin Annabi (SAW) ya kasance yana azumtarsa kusan gaba daya face dan kadan daga cikinsa, kuma ba a kiyaye daga gare shi (SAW) cewa ya kasance yana azumtar watan Muharram ba, sai dai ya kwadaitar kan azumtarsa ta fadinsa (SAW): “Lallai shi ne mafi falalar azumi a bayan Ramadan.” Kuma suka ce domin azumin Sha’aban yana zuwa ne a matsayin ratibi a gabanin na farilla, yayin da azumin Muharram yake zuwa a matsayin nafila mudalaki. Matsayin ratibi ya fi matsayin nafila mudalaki. Duk da haka wadannan watanni biyu sunnah ne a azumce su.” (Sharhi Al-Mumta’u, Mujalladi na 6 shafi na 469).
**{Legacy activities, comments etc counter: 827; topic series: 4; forum: MediaHausa; legacy score: 10; legacy ratings: 2; rating_ip: ***.*14.31.188; associated: 4- /*}