Topic: Tuba da istigfari (5)
Timeline: 2012-03-27 18:52:23
Tuba da istigfari (5)
A Rubuce Da Daga Salihu Is’hak Makera
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mai gamammiyar kyauta a nan duniya, Mai kebantacciyar kyauta a Lahira. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halitta, Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da masu bin su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka a ci gaba da darasinmu kan tuba da istigfari mun tsaya ne a daidai lokacin da muka ambaci sharadi na hudu na karbar tuba. Yau cikin ikon Allah za mu dora daga sharadi na biyar. Da fatar Allah Ya sanya mu kiyaye tare da aiki da abin da muka karanta a baya:
Sharadi na biyar: Yin nadama
Yin nadama rukuni ne daga cikin rukunan tuba, kuma tuba ba ta cika said a ita. A luggah nadama tana nufin yin bakin ciki tare da sauya ra’ayi kana bin da aka yi a baya. (Almufradat na Ragib, shafin na 507).
Kuma Annabi (SAW) ya yi ishara kan kimar yin nadama inda ya ce: “Yin nadama tuba ne.” Ibn Majah da Ahmad suka ruwaito.
Ma’anar cewa tuba ce, yana nufin ita rukuni ce daga cikin rukunan tuba, kamar dai yadda (SAW) ya ce: “Hajji shi ne Arfa.”
Sharadi na shida: Yin azama kan tuba:
Yin azama yana jere ne da nadama, yana nufin tsayuwa da himma kan ba za a koma ga zunubin karo na biyu ba. Azama a luggah shi ne zuciya ta kulla dorewa kan wani al’amari da ta sa a gaba. (Almufradat, shafi na 346).
Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma lallai, hakika Mun yi alkawari zuwa ga Adamu a gabanin wannan, sai ya manta, kuma ba mu samu karfin zuciya a gare shi ba.” (k:20:115). Ma’ana ba Mu samu hakuri da azama daga gare shi ba, saboda bai kubuta daga gafala da wasi-wasin Shaidan ba. Wannan aya tana nuni ne cewa lallai mumini tilas ne ya zamo yana da azama mai karfi da himma. Kuma mai tuba ne ya fi sauran mutane bukatar azama da himma ta yadda zai samu damar fin karfin sha’awoyi da kwadayi. Ya kawar da kai daga gare su, ya toshe kafarsu da karfi, hakan ya sanya ba zai koma ga zunubi ba, tubarsa ta zama tuba sahihiya karbabbiya. (At-Taubah na Dokta Amal Nusair)
Sharadi na bakwai: Mayar da kayan zalunci:
Daga cikin sharuddan tuba wadanda tuba ba ta cika sai da su, akwai mayar da kayan zalunci ga masu su. Wadannan kayan zalunci kodai sun shafi kayayyakin duniya ko waninsu. Idan kayayyakin zalunci sun shafi kayan duniya kamar kwace dukiya, to wajibi ne mai tuban ya mayar da ita ga mai ita ko masu ita, idan dukiyar tana nan. Ko kuma ya nemi yafewarsu idan dukiyar ta halaka. Idan kuma zaluncin ba kayayyakin duniya ba ne, kamar cin mutunci da zunde da makamantansu, to wajibi ne mai tuban ya nemi afuwar wannan zalunci da ya yi, kuma ya nemi yardarm da wanda ya zalunta. A kan haka ne Mai tsira da amincin Allah yake cewa: “Duk wanda ya kasance akwai abin zalunci na dan uwansa a wurinsa to ya raba kansa da ita. Gabanin an karaba wad an uwansa daga kyawawan ayyukansa a lokacin da ba ya da Dinari ko Dirhami, idan kuma ba ya da kyawawan ayyuka, sai a debo miyagun ayyukan dan uwan nasa a jibga masa.” Buhar ya ruwaito a Kitabu Mazalimu wal Gasbi: (Hadisi na 2449)
Ibn Hajrin ya ce: “Abin da Hadisin yake nuni a wurina –Allah ne Mafi sani- shi ne ana ba muminai masu husuma (hakki) daga kyawawan ayyukan abokan husumansu gwargwadon ukubar miyagun ayyukansa. Idan kyawawan ayyukansa suka kare sai a debo miyagun ayyukan abokin husumansa a jibga masa, sannan a yi masa azaba, idan bai yafe masa a duniya ba. Idan ukubar wannan laifuf*****a suka kare, sai a shigar das hi Aljanna bisa abin da aka hukunta masa na tabbata a cikinta saboda imaninsa. Ba za a ba abokin husumansa abin da ya wuce kyawawan ayyukansa a bisa abin da ya mukabalanci miyagun ayyukansa ba, ma’ana a ninka masa, domin hakan yana dga cikin falalar Allah da Yake kebance wanda ya cika ranar kiyama yana mai imani da shi. Allah ne Mafi sani.” (Fathul Bari, sharh Sahihul Buhari).
Na biyu: Sharuddan da suka shafi lokacin karbar tuba
1. Sharadi na farko: Ta kasance gabanin magagin fitar rai, kaiwa gargara.
Ayoyi biyu a cikin suratu Nisa’i sun yi ishara ga haka idan Allah Madaukaki Yake cewa: “Abar da take tuba kawai ga Allah, ita ce ga wadanda suke aikatawar mugun aiki da jahilci sannan su tuba nan kusa. To, wadannan Allah Yana karbar tubarsu. Kuma Allah Ya kasance Masani ne, Mai hikima. Ba tuba ba ce ga wadanda suke aikatawar munanan ayyuka har idan mutuwa ta halarci dayansu ya ce: “Lallai ne ni na tuba yanzu.” Kuma ba tuba ba ce ga wadanda suke mutuwa alhali kuwa suna kafirai. Wadannan Mun yi musu tattalin wata azaba mai radadi.” (k:4:17-18).
Imam Khurdabi ya ce: “Allah Madaukaki Ya kore wanda mutuwa ta halarto masa ya kasance cikin hukuncin masu tuba a lokacin da ya zamo an yanke kauna daga rayuwarsa, kamar yadda ya kasance da Fir’auna lokacin day a kasance a tsakiyar igiyar ruwa za a nutsar da shi, don haka abin da ya bayyana na iman bai amfane shi ba, domin tuba a irin wannan lokaci ba ta da amfani, saboda lokaci ne na gushewar takalifi.” (Jami’u Li’ahkamil kur’an, Mujalladi na 5 shafin na 93).
A kan wannan ne Hadisin da Abdullahi Bin Amru (RA) ya ruwaito daga Annabi (SAW) yake ishara: “Lallai Allah Yana karbar tuban bawa matukar bai kai gargara ba.” Tirmizi da Ibn Majah suka ruwaito, kuma Albani ya inganta shi a cikin Sahihul Jami’u, (Hadisi na 1903).
Almubarakafuri ya ce: “Ma’ana: Matukar rai bai kai makogwaro ba, wato ana nufin matukar ba a sakankance da mutuwa ba, domin tuba bayan an sakankance da mutuwa ba a lissafa ta a tuba.” (Tuhfatul Ahawazi sharhu Jami’u Tirmizi, Mujalladi na 9 shafi na 521).
Sharadi na biyu: Tubar ta auku gabanin fitowar rana daga mfadarta:
Allah Madaukaki Ya ce: “A ranar da sashin ayoyin Ubangijinka yake zuwa, imanin rai wanda bai kasance ya yi imani ba a gabani, ko ya yi tsiwirwirin wani alheri, ba ya amfaninsa.” (k:6:158).
Alusiy yana cewa: “Gaskiyar magana abin da ake nufi da sashin abin da imani ba ya amfanar mutum shi ne a lokacin fitowar rana daga mafadarta.” (Ruhul Ma’ani, Mujalladi na 8, shafi na 68).
An karbo daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “kiyama ba za ta tsaya ba, har sai rana ta fito daga mafadarta, idan ta fito mutane suka gan ta, sai su yi imani gaba daya.” To wannan ne lokacin da imani ba ya amfanar ran da bai yi imani a gabani ba, kuma bai aikata wani aikin alheri a cikin imaninsa ba, sannan sai ya karanta ayar.” Buhari ya ruwaito a cikin Kitabu Tafsiril kur’an: Babin Ran da imaninta ba ya amfaninta. (Hadisi na 4636), kuma lafazinsa ne. Sai Muslim ya fitar da shi a cikin Kitabul Iman: Babin bayanin zamanin da ba a karbar imani a cikinsa. (Hadisi na 157).
Kuma an karbo daga Abu Huraira (RA) daga Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya tuba gabanin fitowar rana daga mafadarta, Allah Ya karbi tubarsa.” Muslim ya ruwaito a Kitabuz Zikri wad Du’a’i wat Taubati wal Istigfari. Babin mustahabbancin istigfari da yawaita yinsa, (Hadisi na 2703)
Sai mako na gaba insha-Allahu za mu dora daga kan falalar tuba da istigfari a cikin Alkur’ani da Sunnah.
Wassalamu alaikum
Za mu cigaba a mako mai zuwa
**{Legacy activities, comments etc counter: 1025; topic series: 3; forum: MediaHausa; associated: 3- /*}