Topic: Maraba da Shekarar 1433 BH: Nazari kan shekarar Musulunci da hijira (5)
Timeline: 2012-03-27 18:58:30
Maraba da Shekarar 1433 BH: Nazari kan shekarar Musulunci da hijira (5)
A Rubuce Da Salihu Is’hak Makera
A ci gaba da kawo wani abu kan Hijira, mun dauko bayani kan bidi’o’in da ake yi game da ranar Ashura inda ’yan Shi’a suka mayar da ranar ta bukukuwan nuna bakin ciki sakamako kashe Sayyidina Husain (RA), da yadda bangaren Nawasib da suke gaba da Ahlul Bait suka mayar da ranar ta murna da farin ciki da yalwata wa iyalai. kila wannan koyarwa ta Nawasib ko Nasibawa ta samu shigowa kasar Hausa, inda aka mayar da ranar Ashurar ta zama wani Idi da Hausawa ke kira da Idin Cika-Ciki, har ake cewa wanda bai ci abinci ya koshi a ranar ba, za a cika masa ciki da wuta ranar kiyama.
To amma fahimta sahihiya ita ce, duk wadannan bukukuwa biyu sun saba wa koyarwar Abu kasim Muhammad bin Abdullahi (SAW), wanda abin da ya ce a yi a ranar shi ne azumi, don koyi da dan uwansa Annabi Musa (AS) da Allah Ya kubutar a wannan rana daga Fir’auna da rundunarsa. Muna cikin gabatar da fatawar Shaihul Islam Ibnu Taimiyya ne kan wannan mas’ala fili ya kare mana a makon jiya. Don haka yau za mu dora daga inda ya tsaya. Bismillah!
“Ya kasance Sayyidina Hasan da Sayyidina Husain suna da babbar daukaka da matsayi mai girma a wurin Allah. Bai kamata a ce abin da ya faru da su na bala’i da ya faru da magabatansu ba, ya faru da su, saboda an haife su a cikin izzar Musulunci, an tarbiyyantar da su a cikin izza da karimci. Musulmi suna girmama su, suna karrama su, Annabi (SAW) ya rasu ba su kammala shekarun tamyiz (balaga) ba. To amma ni’imar Allah ce a kansu da aka jarraba su da abin da ya samu Ahlul Baitinsu kamar yadda aka jarrabi wadanda suka fi su falala. Domin Sayyidina Aliyu bin Abu dalib ya fi su falala, amma an kashe shi yana mai shahada.
Kuma kashe Husain (RA) na daga cikin abin da ya haifar da fitina a tsakanin mutane, kamar yadda kashe Usman (RA) ya zamo daga cikin sabubban da suka jawo fitina a tsakanin mutane (Musulmi), kuma a sababinsa ne al’umma ta rarrabu har zuwa yau. Kuma ya zo a cikin Hadisi cewa: “Abu uku, wanda ya kubuta daga gare su, hakika ya tsira: mutuwata da kashe Halifa Mai hakuri da kuma Dujjal.”
Haka abin da ya kasance, ya kasance, har ’yan Haruriyya karkatattu suka bayyana, wadanda duk da yawan sallarsu da azuminsu da tilawarsu suka yaki Amirul Muminina, Aliyu bin Abu dalib (RA) da wadanda suke tare da shi, shi ma ya yake su da umarnin Allah da ManzonSa…wannan Haruriyya ta zama karkatacciya. Rarrabuwa ta auku a tsakanin muminai, sai dai yaki a tsakanin muminai ba ya fitar da su daga imani…. Sannan Abdurrahman bin Muljim yana daga cikin wadancan karkatattu, shi ya kashe Amirul Muminina Aliyu (RA), Imam Aliyu ya wuce zuwa ga karamar Allah da yardarSa yana mai shahada. Sahabbai suka yi mubaya’a ga dansa Hasan (RA), sai daukakarsa da Annabi (SAW) ya bayar da labarinta cikin Hadisi ingantacce cewa: “Wannan dan nawa shugaba ne, kuma da sannu Allah zai sasanta bangarori biyu masu girma na Musulmi”, ta bayyana.
Sai ya sauka daga shugabancin, Allah Ya daidaita tsakanin bangarorin Musulmi da shi. Wannan ya kasance daga cikin abin da Annabi (SAW) ya yi masa yabo a kai. Wannan ya nuna cewa daidaitawa da sasanta tsakaninsu (Musulmi) yana daga cikin abin da Allah Yake so, kuma abin da ManzonSa (SAW) ke so. Allah Ya gode masa, haka ManzonSa (SAW). Sannan ya rasu ya wuce zuwa ga karamar Allah da yardarSa. Sai wadansu kungiyoyi suka tashi suka goya wa Husaini (RA) baya, suka yi masa alkawarin taimaka masa, har a kai ga nasara idan ya amince. Alhali ba za su iya haka ba, maimakon haka lokacin da ya aika musu dan Baffansa sai suka saba alkawarinsu suka warware shi, suka taimaki wadanda suka ce za su taimake shi a kansu, suka yake shi tare.
Ma’abuta ra’ayi da son Husaini (RA) kamar Ibnu Abbas da Ibnu Umar (Allah Ya yarda da su) da sauransu suka ba shi shawarar cewa kada ya tafi gare su (mutanen Kufa), kuma kada ya karbi komai daga gare su, suna ganin fitarsa zuwa gare su ba daidai ba ne. Amma ya tafi, al’amarin kuma ya kasance kamar yadda suka fada, al’amarin Allah da ma kaddararre ne gwargwado.
Lokacin da Husaini (RA) ya fita ya ga al’amura sun canja ya nemi su bar shi ya koma (Madina) ko ya riski dan Baffansa Yazid, amma suka hana shi, haka lamarin ya kasance har aka yi masa kawanya suka yake shi, ya yake su, suka kashe shi da jama’ar da suke tare da shi yana mai shahada, abin zalunta. Shahadar da Allah Ya girmama shi da ita Ya riskar da shi da Ahlu Baiti Tsarkaka, Ya wulakanta wadanda suka zalunce shi suka yi ta’adda gare shi.
Wannan ya haifar da sharri a tsakanin mutane (Musulmi), sai wata kungiya, jahila, azzaluma, wadda imam mulhida munafika ce ko batacciya tababbiya ta rika bayyana wilaya gare shi da Ahlul Baitinsa ta dauki ranar Ashura rana ta bukukuwa da bakin ciki da kuka. Ta rika bayyana halaye irin na Jahiliyya na daga marin fuskoki da yaga tufafi da koke-koken ta’aziyya irin na Jahiliyya. Sai kuma wadansu mutane(n) imam daga cikin Nasibawa masu ta’assubancin kin Husaini da Ahlu Baitinsa ko jahilai suka mayar da martani ta hanyar fuskantar fasadi da fasadi da karya da karya da sharri da sharri da bidi’a da bidi’a, suka kirkiro Hadisan karya kan nuna farin ciki da jin dadi a ranar Ashura, kamar sanya tozali da yin kaciya da yalwata wa iyali da dafa nau’o’in abinci da ba a saba yi kullum ba da makamantan abubuwan da ake yi ranar Idi da bukukuwa. Sai ya zamo wadannan sun dauki ranar Ashura kamar ranar Idi da farin ciki, wadancan kuma sun dauke ta ranar bukukuwa da nuna baki ciki da koke-koke.
To dukkan bangarorin biyu masu kuskure ne da suka kauce wa Sunna, idan wadancan sun fi mugun nufi da girman jahilci da bayyana zalunci, abin sani Allah Ya yi umarni da adalci da kyautatawa. Kuma Manzon Allah (SAW) bai sunnanta komai daga cikin wadannan al’amura a ranar Ashura ba, haka halifofinsa shiryayyu, ya alla bukukuwa na nuna bakin ciki da koke-koke ko bukukuwa na farin ciki da jin dadi.
Kuma sauran al’amura kamar yin abincin da ya saba wa al’ada kamar ’ya’yan itace da makamantansu, ko sake sababbin tufafi da yalwata wa iyali wajen ciyarwa ko sayen kayayyakin bukatun rayuwa na shekara ko aikata wata ibada kebabbiya kamar Sallah ko yanka ko adana naman layya zuwa ranar don dafa shi tare da ’ya’yan itatuwan ko sanya tozali ko yin kaciya ko yin wanka ko musabaha ko ziyace-ziyarcen juna ko ziyyartar masallatai da sauransu, wadannan duk bidi’o’i ne ababen ki da Manzon Allah (SAW) bai sunnanta su ba, haka halifofinsa shiryayyu, kuma babu wanda ya so haka daga cikin shugabannin Musulmi, ya alla Malik ne ko Sauriy ko Laisu bin Sa’ad ko Abu Hanifa ko Auza’i ko Shafi’i ko Ahmad bin Hambali ko Is’hak bin Rahawiyya ko makamantan wadannan shugabannin Musulunci da malaman Musulunci. Idan wadansu daga mutanen baya mabiya wadancan malamai sun kasance suna umarni da wasu daga cikin wadannan abubuwa suna ruwaito wasu Hadisai da maganganun sahabbai suna cewa: lallai wasu daga cikinsu ingantattu ne, to sun yi kuskure sun kuma jirkita abubuwa ba tare da shakka ba, a wurin ma’abuta sanin hakikanin al’amura.
**{Legacy activities, comments etc counter: 783; topic series: 4; forum: MediaHausa; associated: 4- /*}