Topic: Hikima da hukuncin hana Musulmi kwaikwayon kafirai
Timeline: 2012-03-27 19:01:27
Hikima da hukuncin hana Musulmi kwaikwayon kafirai
A Rubuce Da Salihu I. Makera
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa.
Bayan haka, a duk lokacin da aka ce Musulunci ya hana Musulmi kwaikwayon kafirai, ko kama da su sai wadansu daga cikin Musulmi su rika ganin mai fadar wannan magana ya cika tsauri da tsanantawa. kila ba su karanta abin da malamai magabata da mamaya suka ce kan wannan maudu’i mai girma ba ne. kila ba su san hikimar da ke cikin haka ba ne.
Ganin haka ya sanya muke gabatar da wannan takaitaccen nazari kan hikimar hana kwaikwayon ko kamanci da kafirai da fatar su fahimci hakan tare da aiki da su.
Malamai sun ambaci hikimomi da sabubba masu yawa kan hana kwaikwayo ko kama da kafirai.
Ga fahimtar malamai ayyukan kafirai imma sun ginu ne a kan bata da fasadi ko kan bidi’o’in da suka kirkiro. Koda Ma’abuta Littafi ne za a iske sun kirkiro wasu bidi’o’i a bayan wucewar Manzanni da suke da’awar suna binsu, ko su caccanja koyarwarsu kamar yadda a yau muke ganin kasashen Yamma suna fada da koyarwar addinin Kirista da sunan ’yancin dan Adam. Kowa yana ganin yadda suka amince ’yan luwadi da madigo suke zama limaman addinin Kirista duk da cewa hakan ya saba wa hakikanin koyarwar Yesu Almasihu (Alaihis Salam). Muna ganin yadda kasashen Turai suke kokarin tilasta duniya ta halatta abin da dukkan sama suka haramta. Suke barazanar sanya kafar wando da duk kasar da ta haramta aure tsakanin mace da mace da namiji da namiji!
Shaihul Islam Ibnu Taimiyya ya ce: “Lallai abin da (kafirai) suke himmantuwa a kansa na daga shiriya da dabi’u na iya kasancewa mai cutarwa ko mai nakasawa, don haka aka hana shi ko aka yi umarni da kishiyarsa da abin da ke da amfani da kamala. Babu wani abu daga al’amarinsu face ko dai mai cutarwa ko nakasasshe. Domin abin da ke hannunsu ayyukan da aka kirkira ne ko wadanda aka shafe hukuncinsu da makamantansu masu cutarwa. Kuma abin da ke hannunsu da ba a soke asalinsa ba, to ya hadu da kari ko ragi. Don haka saba musu a cikinsa ta hanyar shar’anta abin da zai haifar da kamala ne. Kuma ba zai yiwu ya kasance akwai wani abu daga al’amarinsu mai kamala ba koda yaya ne. Don haka akwai alfanu da islahi gare mu, wajen saba musu a cikin dukkan al’amuransu.” (Ikhtida’us Siradil Mustakim, Mujalladi na 1 shafi na 198).
Sannan wata himkima ta hana koyi da kafirai ita ce don a tabbatar an nisance su kuma an nisanci dabi’u da ayyukansu. Shaihul Islam Ahmad Ibnu Abdulhalim Ibnu Taimiyya ya ce: “Hakikanin manufar saba musu a cikin abin da ya shafi shiriya na zahiri akwai gyara da amfani ga bayin Allah muminai, saboda abin da ke cikin saba musu na guje wa abin da ke wajabta yin nesa daga ayyukan ma’abuta wuta. Sai dai wannan maslaha tana bayyana ne ga wanda aka haskaka zuciyarsa ga hasken gane abin da wadanda aka yi fushi a kansu da batattu suka siffanta da shi na daga cutar da za ta yi masa mummunar cutarwa fiye da cutar da ta shafi jiki.” (Ikhtida’us Siradil Mustakim, Mujalladi na 1 shafi na 197-198).
Wata muhimmiyar ka’ida ta Musulunci da rashin koyi da kafirai ke tabbatarwa ita ce ka’idar nan ta wulaya da barranta. Wato tawaye ga dabi’u da halayen kafirai zuwa ga jibinta da rungumar halaye da dabi’un muminai.
Ibnu Taimiyya ya ce kan haka: “Lallai saba wa shiriyar kafirai a zahiri tana wajabta nisa da rabuwar da ke yanke muminai daga abubuwan da suke wajabta fushin (Allah) da sabbaba bacewa. Kuma tana karfafa tsakanin ma’abuta shiriya da yardar Allah da tabbatar da abin da Allah Ya yanke na jibinta a tsakanin rundunarSa mai cin nasara da ta makiyanSa mai asara.” (Ikhtida’us Siradil Mustakim, Mujalladi na 1 shafi na 93).
Wata hikimar ita ce, rashin koyi da kafirai tana bambance Musulmi da sauran mutane da suka hada da kafirai da mulhidai (wadanda ba su yarda da kowane irin addini ba). Shaihul Islam Ibnu Taimiyya (Allah Ya lullube shi da rahamarSa) ya ce: “Lallai musharaka (haduwa ko kamanci) da su a cikin shiriya na fili tana wajabta cudanya na zahiri, har a kasa iya bambancewa a tsakanin shiryayyu, yardaddu da wadanda aka yi fushi a kansu da batattu.” (Ikhtida’us Siradil Mustakim, Mujalladi na 1 shafi na 94).
Hukuncin yin kama ko koyi da kafirai:
Sheikh Ibnu Usaimin (Allah Ya yi masa rahama) ya ce: “Abin da makiya Allah kuma makiyanmu wato kafirai suke aikatawa ya kasu kashi uku. Kashi na farko: Ibadoji. Kashi na biyu: Al’adu. Kashi na uku: Sana’o’i ko Ayyuka.
Amma ibada abu ne sananne cewa bai halatta ga kowane Musulmi ya yi kama ko ya kwaikwaye su a cikin ibadarsu ba. Duk wanda ya yi kama da su ko ya kwaikwaye su a ibadarsu, to, lallai shi yana kan hadari mai girma. Kuma hakika hakan yana iya kai shi ga kafirta ya fita daga da’irar Musulunci. Game da al’adu kamar sanya tufafi da makamantan haka, lallai ya haramta Musulmi ya yi kama da su ko ya kwaikwaye shi. Saboda fadin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa: “Wanda ya yi kama da mutane, to, yana cikinsu.” (Ahmad, mujalladi na 2, shafi na 50 da Abu Dawud, Fillibasi, Hadisi na na 4031, da Abdu bin Hamid, Mujalladi na 1shafi na 267 da Baihaki, Fi Shu’ubi, Mujalladi na 2 shafi na 75, kuma Albani ya inganta shi a cikin Hijabul Mar’atil Muslima, shafi na104).
Amma game da sana’o’i da ayyuka wadanda suka shafi jin dadin mutane, babu laifi a kwaikwaya ko a san irin abin da suka sana’anta a kuma amfana da shi. Wannan ba ya daga cikin abin da ake kira koyi da kafirai, sai dai a ce an hadu da su a ayyuka masu amfanarwa, ba za a kirga wanda ya yi haka a cikin masu kama da su ba.” (Majmu’u Fatwa war Rasa’il na Sheikh Muhammad bin Salihu Al-Usaimin, Mujalladi na 3 shafi na 40).
Ya kuma ce: “Lallai hukunce-hukuncen koyi da kafirai a bisa tafsili ba su zamo daya ba. Domin kowane hali daga cikin halayen yin kamar yana da hukuncin da ke bijiro masa bisa nassoshi da ka’idojin shari’a daga bangaren masu ilimi da fakihan addini. Sai dai akwai wasu hukunce-hukunce na bai-daya da suke tsara dukkan nau’o’in koyin a jumlance ba a tafsili ba kamar misalign da ke zuwa:
Na farko: Daga cikin nau’o’in yin koyi da kafirai akwai abin da yake shirka ne ko kafirci, kamar yin koyi da su a cikin akidoji da wasu ibadoji, kamar yin koyi da Yahudu da Nasara da Majusawa a al’amuran da suka saba wa tauhidi da akida kamar ilhadi da hululi da ba wadansu mutane matsayin Allantaka, kamar Annabawa da salihan bayi ko bauta musu da rokonsu, koma bayan Allah. Ko yin hukunce-hukunce da shari’a ko dokokin dan Adam da suka saba wa na Allah. Dukkan wadannan imma shirka ne ko kafirci.
Na biyu: Daga cikin abubuwan da ake koyi da su akwai abin da yake sabo ne da fasikanci, kamar koyi da kafirai a wasu al’adu. Kamar cin abinci da hannun hagu ko shan abin sha da hagu ko sanya zoben zinari ko yin ado da zinari ga maza, ko aske gemu da shiga irin ta mata ga maza, ko shiga irin ta maza ga mata da makamantansu.
Na uku: Akwai abin da yake makaruhi ne, shi ne abin da ake kai-kawo cikin hukuncinsa, saboda rashin bayani karara a cikin hukuncin. Wato ina nufin an samu kai-kawo kan suluki da al’adu da al’amuran duniya a tsakanin karhanci da halacci. Sai wannan ya jefa Musulmi ga fadawa a cikin koyi da kafirai, don haka sai hukuncinsa ya zamo makaruhi.
Na hudu: Abin da yake halal, shi ne abin da ba su kadai ne suka kebanta da shi ba na al’amuran duniya. Ma’ana ba wata dabi’a ce ta su kadai da ke bambance su da Musulmi ba, kuma ba ya kaiwa ga babbar fasadi a kan Musulmi ko jawo amfani ga kafirai amfanarwar da za ta jawo wa Musulmi kasakanci da makamancin haka. Kuma yana daga cikin abin da ya halatta cin gajiyar kayayyakin inganta rayuwa da binciken ilimi a abin da ya shafi kyautata rayuwa a duniya.”(Risalatu (Man Tashabbaha Bi kaumin Fahuwa Minhum), Shafi na 20-23).
Wasallallahu alan Nabiyil karim.
**{Legacy activities, comments etc counter: 1333; topic series: 5; forum: MediaHausa; legacy score: 9; legacy ratings: 2; rating_ip: ***.*14.31.188; associated: 5- /*}