Topic: Tuba Da Istigfari (8)
Timeline: 2012-03-27 19:02:24
Tuba Da Istigfari (8)
A Rubuce Da Salihu Is’hak Makera
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mai gamammiyar kyauta a duniya, Mai kebantacciyar kyauta a Lahira. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halitta, Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da masu bin su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka a ci gaba da darasinmu kan tuba da istigfari yau za mu kara bayani kan falalar tuba da istigfari a cikin Alkur’ani, sannan mu fada cikin falalarta a cikin Sunnah. Bismillah:
Game da ayar da ta gabata Abdullahi dan Abbas (RA) ya ce: “Akwai aminci biyu a cikinsu (Musulmi): Wato Annabi (SAW) da istigfari. To, Annabi (SAW) ya tafi, yanzu istigfari ne ya saura.” (Tafsiru Ibn Kasir, Mujalladi na 2 shafi na 317).
Ke nan idan mutane suka saki istigfari za su rasa daya amincin, kuma ta yin haka sai Allah Ya azabtar da su, domin Ya nuna kasancewar Annabi (SAW) da yin istigfari ne yake shamakance mutane daga azabarSa.
g) karuwar dukiya da ’ya’ya da saukar ruwan sama:
Allah Madaukaki Ya ce: “Sai na ce ku nemi gafara daga Ubangijinku, lallai ne Shi Ya kasance Mai gafara ne. Ya sako da (girgijen) sama a kanku da ruwa.mai bubbuga. Kuma Ya yalwata muku game da dukiya da ‘’ya’ya, kuma Ya sanya muku (albarka) ga gonaki kuma Ya sanya muku koguna.” (k: 71: 10-12).
Ibnu Abbas (RA) ya ce: “Ma’ana idan kuka tuba zuwa ga Allah kuka yi istigfari za a ba ku kuma a ciyar da ku arziki a saukar muku da albarkoki daga sama, an fitar muku albarkatun kasa a fitar muku da tsirrai a inganta gonakinku, kuma a albarkace ku da ’ya’ya, ma’ana a yalwata muku dukiya da ’ya’ya, kuma a sanya muku gonaki da suke dauke da nau’o’in kayan marmari da abinci, sannan a keta koramu su yi musu ado suna gudana a tsakaninsu.” (Tafsiru Ibn Kasir, Mujalladi na 4 shafi na 453).
Falalar tuba da istigfari a cikin Sunnah:
1. An karbo daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai idan bawa ya yi laifi sai ya zama wani digo baki a cikin zuciyarsa. Idan ya ciru kuma ya yi istigfari ya tuba, sai a wanke zuciyarsa, amma in ya ci gaba da zunubin sai a kara masa (bakin) a cikinta, har zuciyar ta yi tsatsa da zunubi. Shi ne tsatsa (ko rufi da toshewar) da Allah Ya ambata a cikin Suratul Mudaffifina cewa: “A’aha! Ba haka ba, abin da suka kasance suna aikatawa dai, ya yi tsatsa a cikin zukatansu.” (k:83:14)” Tirmizi da Ibn Majah suka ruwaito.
Al-Mubarakfuri ya ce: “ma’ana za a tsaftace a wanke zuciyarsa. Domin tuba kamar abin goge rubutu ne, inda take shafe kazantar zuciya da bakin da take yi a hakika ko mujazi.” (Tuhfatul Ahwazi bi sharh jami’I Tirmizi, Mujalladi na 9 shafi na 254).
2. An karbo daga Abu Musa Al-Ash’ari (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai Allah Yana shimfida hannunSa da daddare don mai laifin rana ya tuba, kuma Yana shimfida hannunsa da rana don mai laifin dare ya tuba, har zuwa lokacin da rana za ta fito daga mafadarta.” Buhari ya ruwaito.
3. An karbo daga Abu Sa’idul Khudiri (RA) ya ce: “Manzon Allah ya ce: “A cikin wadanda suka gabace ku akwai wanda ya kashe rayuka 99, sai ya tambaya a nuna masa wanda ya fi ilimi a kasar, sai aka tura shi wajen wani ma’abucin ibada. Ya je ya ce masa: “Na kashe mutum 99, shin za a karbi tubata?” Sai ya ce: “A’a.” Sai ya kashe shi ya cika na 100 da shi. Sannan ya sake tambayar wane ne mafi ilimi a kasar, aka shiryar das hi zuwa ga wani mutum masani. Sai ya ce: “Na kashe mutum 100, shin za a karbi tubata?” Sai ya ce, “Eh za a karba.” Wa zai shiga tsakaninsa da tuba. Ka tafi kasa kaza da kaza. Domin lallai a cikinta akwai mutanen da suke bauta wa Allah, ka bauta wa Allah tare da su, kada ka dawo kasarka, domun muguwar kasa ce.” Sai ya tafi har yana tsakiyar tafiya sai mutuwa ta zo masa. Sai Mala’ikun rahama da na azaba suka kama muhawara kansa. Mala’aikun rahama suka ce, ya taho yana mai tuba, zuciyarsa ta koma ga Allah. Mala’ikun azaba suka ce, lallai shi bai taba aikata alheri ba ko kadan. Sai Mala’ikan mutuwa ya zo musu a siffar dan Adam, ya shiga tsakaninsu, ya ce: “Ku lissafa tafiyar da ke tsakanin kasasshen biyu, duk kasar da ya fi kusa da ita, to nan yake. Da suka lissafa sai suka ga ya fi kusa da kasar da ya yi nufi. Sai Mala’ikun rahama suka dauke shi!” Buhari da Muslim suka ruwaito.
Ibnu Hajrin ya ce a cikin wannan Hadisi akwai wajibcin tuba daga dukkan kaba’irai ciki har daga kisan rai. Kuma yana nuna idan Allah Ya karbi tubar wanda ya yi kisa, sai ya kallafa wa abokin husumar yarda da haka. Sannan Iyad ya ce: “A cikinsa (Hadisin) akwai cewa lallai tuba tana amfana daga aikata kisan kai, kamar yadda take amfanar sauran zunubai. Kuma koda hakan ya kasance shari’a ce ga wadanda suke gabaninmu, a cikin kafa hujja da shi akwai sabani. Sai dai wannan ba wurin sabanin ba ne. Domin wurin da ake sabani shi ne inda ba a samu shari’armu ta tattabatar tare da muwafaka da abin da ya gabata ba. Amma idan mu ma ya zo mana to ya zama shari’a a gare mu ba tare da sabani (khilafa) ba.” (Fathul Bari, Mujalladi na 6 shafi na 518).
4. Daga Abdullahi dan Mas’ud (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: (Wallahi Allah ne mafi farin ciki da tubar bawanSa fiye da mutumin da ya sauka a wurin da ke da hadari (tsakiyar Hamada) tare da dabbarsa dauke da abincinsa da ruwan shansa. Sai ya kishingida har barci ya dauke shi, yana farkawa sai ya lura dabbarsa ta bace (da abin da take dauke da shi), zafi da kishin ruwa suka tsananta masa, ya yi dan dube-dube gwargwadon abin da Allah Ya so bai gan ta ba, ya ce: “Bari in koma wurin da nake (bisa yanke tsammani), sai ya koma ya sake barci, sannan ya farka yana daga kai, sai ya ga dabbarsa ta dawo wurinsa.” Buhari ya ruwaito.
Daga Shaddadu Bin Aus (RA) daga Annabi (SAW) ya ce: “Shugabar istigfari mutum ya ce: “Allahumma anta rabbi la ilaha illa anta, khalaktani wa ana abduka, wa ana ala ahadika wa wa’adika mastada’atu. A’uzu bika min sharri ma sana’atu, abu’u laka bi ni’imatika alayya, wa abu’u laka bi zambi fagfirli fa innahu la yagfiru zunuba illa anta.” Wanda ya fade ta a yininsa yana mai yakini da ita, ya mutu a wannan yini gabanin ya yi yammaci, yana daga ciki ’yan Aljannah. Wanda kuma ya fade ta da daddare yana mai yakini da ita ya mutu gabanin asuba yana daga cikin ‘’yan Aljannah.” Buhari ya ruwaito shi.
Ibnu Abu Hamza ya ce: “A cikin wannan Hadisi Manzon Allah (SAW) ya tara kyawawan ma’anoni da kyawawan lafuzza da suka cancanci a kira wannan istigfari da shugabar istigafarori. A cikinsa akwai ikrari ga Allah Shi kadai da uluhiyya da ubudiyya da furta cewa Shi ne Mahalicci da ikrari da alkawarin da aka dauka maSa da kwadayin abin da Ya yi alkawari da shi da neman tsari daga sharri abin da bawa ya aikata da jingina ni’ima zuwa ga Mai samar da ita, da jingina zunubi zuwa ga kansa da kwadayin samun gafara da furta cewa babu mai ikon haka sai Shi (Allah). Dukkan wadannan ishara ne zuwa ga haduwar shari’a da hakika, domin takalifancin shari’a ba ta yiwuwa sai in ya zamo a cikin hakan akwai taimako daga Allah.” (Fathul Bari, Mujalladi na 11 shafi na 103).
6. Daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Wallahi ni ina yin istigfari ga Allah da tuba gare shi a yini fiye das au saba’in.” Buhari ya ruwaito shi.
Ibnu Badda’u ya ce: “Annabawa sun fi saura mutane tsananin kokari a wajen yin ibada, saboda abin da Allah Ya ba su na sani. Su a kowane lokaci suna cikin godiyarSa ne, suna masu furuci gare Shi da nuna gazawa.” (Sharh Sahihul Muslim, Mujalladi na 10 shafi na 77).
**{Legacy activities, comments etc counter: 976; topic series: 3; forum: MediaHausa; associated: 3- /*}