Topic: Minti Daya!! Me Za Ku Iya Yi A Minti Daya?
Timeline: 2012-05-13 05:49:03
A Rubuce Da Babarku: Safiya Husaini Falaki
Minti Daya!! Me Za Ku Iya Yi A Minti Daya?
‘Ya’ya na Assalamu ‘Alaikum Wa Rahmatullah.
Bayan haka. Ku sani cewa ba abin da ya fi lokaci muhimmanci a rayuwarku; duk wata nasara da kuka ga wani ko wata sun samu a rayuwarsu a da ko yanzu, tana da alaka da amfani da lokacinsu da suka yi, hakanan kurar baya, da asararru a rayuwarsu za ku ga rashin amfani da lokacinsu yanada daga cikin manya-manyan abubuwan da suka kai su suka baro.
Don haka, ina yi muku wasici da ku kula da lokacinku yadda ya kamata, kada ku sake ku yi asarar ko da minti daya, ko ma in ce sakan daya na lokacinku ba tare da kun aikata wani abin da zai amfane ku a duniyarku, ko a lahirarku a cikinsa ba.
Na jarraba na ga cewa cikin minti daya mutum zai iya aikata alhairai masu tarin yawa.
Idan kuka dauki karatun Alqur’ani, inda mutum zai karanta ayoyi kadan a kowane harafi daya ya samu lada goma, sai ku ga cikin karamin lokaci kun tashi da daruruwa ko ma dubunnai na lada, haka nan Salati ga Manzon Allah (SAW) da sauran addu’o’i. Alal misali:
A MINTI DAYA: Za ku iya karanta Fatiha sau bakwai, kun ga ladan da za ku samu a nan kawai ya kai dubu daya da dari hudu.
A MINTI DAYA: Za ku iya karanta “Kulhuwallahu” sau ashirin, wannan kuma kamar yadda kuka sani dai dai yake da sauke Alkur’ani kusan sau bakwai, tun da Annabi (SAW) ya ce “Kulhullahu” dai dai take da daya bisa uku na Kur’ani” inda mutum kullum zai karanta “Kulhuwallahu” sau ashirin a minti daya a kowace rana, a wata zai samu dari shida, a shekara kuma zai karanta sau dubu bakwai da dari biyu, wanda wannan yana daidai da karanta Al’kur’ani sau dubu biyu da dari hudu! Kun kuwa san kamar yadda ya gabata kowne harafi daya lada goma, ai ku gwanayen lissafi ne lada nawa kenan!?
A MINTI DAYA: Za ku iya yi wa Annabi(SAW)salati sau hamsin da sigar: “Allahumma Salli ‘Ala Muhammad Wa Sallim” kun ga Allah (SWT) zai yi muku salati dari biyar kenan; domin duk wanda ya yi salati daya ga Annabi (SAW) sau daya, goma Allah (SWT) zai yi masa kamar yadda ya zo a ingataccen hadisi.
A MINTI DAYA: Za ku iya fadin “Subhanallah Walhamdulillah” sau dari. Ga shi kuwa Annabi (SAW) ya ce: “Idan mutum ya yi wannan addu’a sau dari za’a kankare masa zunubansa ko da kuwa sun kai cikin teku.
A MINTI DAYA: Za ku iya karanta (La’i laha Illallahu Wahdahu La Sharika Lahu, Lahul Mulku, Wa Lahul Hamdu, Wa Huwa ‘Ala Kulli Shai’In Kadir) sau ashirin, ladan kowace goma inji Annabi (SAW) kamar mutum ya ‘yanta rai hudu ne daga ‘ya’yan Annabi Isma’il (S.A.W) kun ga ladan ‘yanta rayuka takwas kenan.
A MINTI DAYA: Za ku iya yin salla ta nafila raka’a biyu in dai za ku takaita ne akan wajibai kawai, hada da tasbihi uku a ruku’i, uku a sujjada, a shekara raka’o'i dari bakwai kenan kowace raka’a tana da sujjada biyu, a shekara za ku sami sujjada dubu daya da dari hudu kenan, to ina kuma a ce kullum za ku yi raka’a goma, ko sama da haka? Ga shi kuwa hadisi ya inganta cewa: “Mutum ba zai yi sujjada saboda Allah ba, face an kara masa daraja, an kuma kankare maka zunubai”
Game da karatu da rubutu kuwa:
A MINTI DAYA: Za ku iya karanta shafi daya zuwa hudu gwargwadon nau’in littafin, da irin karatun, to idan kullum za ku yi karatun minti sittin kacal litattafai nawa za ku rika karancewa duk sati?
A MINTI DAYA: Za ku iya rubuta layi hudu zuwa biyar, kwatankwacin daya bisa uku na shafi kenan, idan kowaccenku za ta rubuta layi hudu a kullum a wata guda za ta rubuta shafi goma, a shekara kuma za ta rubuta shafi dari da ashirin, cikin shekara goma za ta iya rubuta sha*****a dubu daya da dari biyu kwatankwacin hamshakin littaffin nan na Ibnul kayyim (RA) mai suna “Zadul Ma’ad” ina kuma ga a ce za ta yi rubutun minti goma zuwa sama?
‘Ya’yana abin da nake so in nuna muku a nan shi ne, kimar kowane minti daya na rayuwarku; za ku iya ribatarsa ta hanyoyi masu tarin yawa; kamar zikiri, karatun Alqur’ani, addu’o'i, nazarin wasu littattafai da za su amfane ku, tunani akan wani abin da zai amfane ku da al’umma baki daya, taimakon mahaifanku dss. ‘
‘Yan albarka! kowane minti daya na rayuwarku yana da matukar girma da amfani idan har kun san yadda za ku yi tattalinsa, ina kuma ga sauran mintina da awoyi dake cikin wuni, ranaku, watanni, da shekaru?
Kar ku rika bata lokacinku a abubuwa mara sa amfani, – kamar surutu barkatai, yi da mutane, annamimanci, bin kwakkwafin asirin mutane, karance-karance da kalle kalle marasa amfani dss. Ababan alfaharina ku sani cewa: Duk wanda ya tafi da lokacinsa cikin wasanni da shirme sai ya yi cizon yatsa nan gaba, Allah ya kiyaye min ku daga duk wata nadama ko da-na-sani a rayuwarku.
Inda yawancin masu bata lokacinsu aikin alherin ne kwai ba sa yi a cikinsa da sai a ce “Dama-dama wai kibiya a ido” amma abin takaicin shi ne, bayan sun ki yin aikin alheri a ciki, su cika shi makil da sharri zunubai, da lai*****a iri-iri ko kin sauke wasu nauyaye-nauyaye da suke kansu (kamar ibada, aikin gida, taimakon iyaye, karatu, dss) Allah ya tsare mu daga lalaci da rashin himma, da mutuwar zuciya.
Ta hanyar dan bayanin da ya gabata, na tabbata kun fahimta, kun kuma gamsu da cewa cikin kowane minti daya na rayuwarku za ku iya aikata abubuwa na alheri masu tarin yawa a duniyarku da lahirarku.
Don haka ina yi muku wasiyya da ku yi amfani da damar da kuke da ita wurin amfani da lokacinku kafin lokaci ya kure muku.
‘Ya’yana na kaina ga wasu daga cikin hanyoyin da za su taimaka muku wurin amfani da lokacinku yadda ya kamata. 1) Kiyaye lokutan ibada. 2) Tsara jadawali (time table) na ayyukanku a kullum. 3) Karfafa alaka da nagartattun kawaye da suka san kimar lokacinsu, da nisatar malalata. 4) Tuna cewa duk sakan din da yafuce na lokacinku har abada ba zai dawo ba. 5)Ku sani cewa duk lokacin da kuka kara girma lokacinku da damar da kuke da ita raguwa take yi. 6) Ku rika hada aiki sama da daya a lokaci guda (kamar kuna wanki, kuna tilawa, ko kuna mota, kuna istigfari, ko salatin Annabi, ko karatu..dss). 7) Zaman hira makasa ce ta lokaci ku nisace shi.
Allah ya yi muku albarka!
**{Legacy activities, comments etc counter: 1606; topic series: 3; forum: MediaHausa; associated: 3- /*}