Shin, yã zama abin mãmaki ga mutãne dõmin Mun yi wahayi zuwa ga wani namiji daga
gare su cẽwa, "Ka yi gargaɗi ga mutãne kuma ka yi bushãra ga waɗanda suka yi
ĩmãni da cẽwa: Lalle ne sunã da abin gabãtarwar gaskiya a wurin
Ubangijinsu."Kãfirai suka ce: "Lalle ne wannan, haƙĩƙa, masihirci ne
bayyananne."
Lalle Allah ne Ubangijinku wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwãna shida,
sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi Yanã gudãnar da al'amari. Bãbu wani
macẽci fãce a bayan izninSa. Wannan ne Allah, Ubangijinku, sai ku bauta Masa.
Shin fa, ba ku tunãni?
zuwa gare Shi makõmarku take gabã ɗaya, wa'adin Allah gaskiya ne. Haƙĩƙa, Shi ne
Yake fara halitta, sa'an nan kuma Ya mayar da ita dõmin Ya sãka wa waɗanda suka
yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai da ãdalci, kuma waɗanda suka kãfirta
sunã da abin sha daga ruwan zãfi, da azãba mai raɗaɗi, sabõda abin da suka
kasance sunã yi na kãfirci.
Shĩ ne wanda Ya sanya muku rãnã, babban haske, da watã mai haske, kuma Ya
ƙaddara shi ga Manzilõli, dõmin ku san ƙidãyar shẽkaru da lissãfi. Allah bai
halitta wannan ba, fãce da gaskiya, Yanã bayyana ãyõyi daki-daki dõmin mutãne
waɗanda suke sani.
Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, Ubangijinsu Yanã
shiryar da su sabõda ĩmãninsu, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, a cikin
gidãjen Aljannar ni'ima.
Kiransu a cikinta, "TsarkinKa yã Allah!" Kuma gaisuwarsu a cikinta,"Salãmun",
kuma ƙarshen kiransu, cẽwa, "Gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu."
Kuma dã Allah Yana gaggãwa ga mutãne da sharri kamar yadda Yake gaggauta musu da
alhẽri, haƙĩƙa dã an hukunta ajalinsu zuwa gare su. Sabõda haka Munã barin
waɗanda ba su ƙaunar gamuwa da Mu, a cikin kangararsu sunã ta ɗimuwa.
Kuma idan cũta ta shãfi mutum, sai ya kirãye Mu, yanã (kwance) ga sãshensa kõ
kuwa zaune, kõ kuwa a tsaye. To, a lõkacin, da Muka kuranye cũtar daga gare shi,
sai ya shũɗe kamar ɗai bai kirãye Mu ba zuwa ga wata cũta wadda ta shãfe shi.
Kamar wannan ne aka ƙawãta ga maɓannata, abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Kuma, haƙĩƙa, Mun halakar da al'ummomi daga gabãninku, a lõkacin da suka yi
zãlunci, kuma manzanninsu suka jẽ musu da hujjõji bayyanannu, amma ba su kasance
sunã ĩmãni ba. Kamar wannan ne, Muke sãkãwa ga mutãne mãsu laifi.
Kuma idan anã karatun ãyõyĩnMu bayyanannu a kansu, sai waɗanda bã su ƙaunar
gawuwa da Mu, su ce: "Ka zo da wani Alƙur'ãni, wanin wannan, ko kuwa ka musunyã
shi." Ka ce: "Bã ya kasancẽwa a gare ni in musanyã shi da kaina. Bã ni biyar
kõme fãce abin da aka yiwo wahayi zuwa gare ni. Kuma, haƙĩƙa ni inã tsõro idan
na sãɓã wa Ubangijina, ga azãbar wani yini mai girma."
Ka ce: "Dã Allah Ya so dã ban karanta shi ba a kanku, kuma dã ban sanar da kũ ba
gameda shi, dõmin lalle ne nã zauna a cikinku a zãmani mai tsawo daga gabãnin
(fãra saukar) sa. Shin fa, bã ku hankalta?"
Kuma sunã bautã wa, baicin Allah, abin da bã ya cũtar dasu kuma bã ya amfãninsu,
kuma sunã cẽwa: "Waɗannan ne macẽtanmu a wurin Allah."Ka ce: "Shin, kunã bai wa
Allah lãbãri ne, ga abin da bai sani ba, a cikin sammai ko a cikin ƙasa?
TsarkinSa ya tabbata kuma Yã ɗaukaka daga gabin da duk suke yin shirki da Shi."
Kuma mutãne ba su kasance ba fãce al'umma guda, sa'an nan kuma suka sãɓã wa
jũna, kuma ba dõmin wata kalma ba wadda ta gabãta daga Ubangijinka, dã an yi
hukunci a tsakãninsu a kan abin da yake a cikinsa suke sãɓã wa jũna.
Kuma sunã cẽwa: "Don me ba a saukar da wata ãyã ba a gare shi, daga
Ubangijinsa?" To, ka ce: "Abin sani kawai, gaibi ga Allah yake. Sai ku yi jira.
Lalle ne nĩ, tãre da ku, inã daga mãsu jira."
Kuma idan Muka ɗanɗanã wa mutãne wata rahama, a bãyan wata cũta tã shãfe su, sai
gã su da mãkirci a cikin ãyõyinMu. Ka ce: "Allah ne mafi gaggãwar (sakamakon)
mãkirci." Lalle ne ManzanninMu sunã rubũta abin da kuke yi na mãkirci.
Shĩ ne wanda Yake tafiyar da ku a cikin tudu da (kuma) tẽku, sai idan kun
kasance a cikin jirãge, su gudãna tãre da su da iska mai dãɗi, kuma su yi farin
ciki da ita, sai wata gũguwa ta je wa jirãgen, kuma tãguwar ruwa ta jẽ musu daga
kõwane wuri, kuma su tabbata cẽwa sũ, an kẽwaye su, sai su kirãyi Allah, sunã
mãsu tsarkake addini gare Shi, (sunã cẽwa): Lalle ne idanKa kuɓutar da mu daga
wannan, haƙĩƙa munã kasancẽwa daga mãsu gõdiya.
To, a lõkacin da Ya kuɓutar da su, sai, gã su sunã zãlunci a cikin ƙasa, bã da
wanĩ hakki ba. Yã ku mutãne! Abin sani kawai, zãluncinku a kanku yake, a bisa
rãyuwar dũniya. Sa'an nan kuma zuwa gare Mu makõmarku take, sa'an nan Mu bã ku
lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa,
Abin sani kawai, misãlin rãyuwar dũniya kamar ruwa ne Muka saukar da shi daga
sama, sa'an nan tsiron ƙasa ya garwaya da shi. Daga abin da mutãne da dabbõbi
suke ci, har idan ƙasa ta riƙi zinãriyarta kuma ta yi ƙawa, kuma mutãnenta suka
zaci cẽwa sũ ne mãsu ĩkon yi a kanta, sai umurninMu ya je mata da dare kõ kuma
da rãna, sai Mu maishẽta girbabba kamar ba ta wadãta ba a jiya. Kamar wannan ne
Muke rarrabe ãyõyi, daki-daki, ga mutãne waɗanda suke tunãni.
Waɗanda suka kyautata yi, sunã da abu mai kyãwo kuma da ƙari, wata ƙũra bã ta
rufe fuskõkinsu, kuma haka wani ƙasƙanci. waɗancan ne abokan Aljanna, sunã
madawwama a cikinta.
Kuma waɗanda suka yi tsirfar mũnanan ayyuka, sakamakon mummuna da kamarsa yake,
kuma ƙasƙanci yanã rufe su. Bã su da wani matsari daga Allah, kamar an rufe
fuskokinsu da guntãyen ƙirãruwa daga dare mai duhu. Waɗannan ne abõkan wuta,
sunã madawwama a cikinta.
Kuma a rãnar da Muke tãra su gabã ɗaya, sa'an nan kuma Mu ce wa waɗanda suka yi
shirki, "Ku kãma matsayinku, kũ da abũbuwan shirkĩnku." Sa'an nan Mu rarrabe a
tsakãninsu, kuma abũbuwan shirkinsu su ce: "Bã mũ kuka kasance kunã bauta wa
ba."
A can ne kõwane rai yake jarraba abin da ya bãyar bãshi, kuma aka mayar da su
zuwa ga Allah, Majiɓincinsu Tabbatacce kuma, abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa
ya ɓace musu.
Ka ce: "Wãne ne Yake azurtã ku daga sama da ƙasa? Shin kõ kuma Wãne ne Yake
mallakar jĩ da ganĩ, kuma Wãne ne Yake fitar da mai rai daga mamaci, kuma Ya
fitar da mamaci daga mai rai, Kuma Wãne ne Yake shirya al'amari?" To, zã su ce:
"Allah ne." To, ka ce: "Shin fa, bã zã ku yi taƙawa ba?"
Ka ce: "Shin, daga abũbuwan shirkinku akwai wanda yake fãra halitta, sa'an nan
kuma ya mayar da ita?" Ka ce: "Allah ne Yake fãra halitta, sa'an nan kuma Ya
mayar da ita. To, yãyã akejũyar da ku?"
Ka ce: "Shin, daga abũbuwan shirkinku akwai wanda yake shiryarwa zuwa ga
gaskiya?" Ka ce: "Allah ne Yake shiryarwa zuwa ga gaskiya. Shin fa, wanda Yake
shiryarwa ne mafi cancantar a bi Shi, ko kuwa wanda bã ya shiryarwa fãce dai a
shiryar da shi? To, mẽne ne a gare ku? Yãya kuke yin hukunci?"
Kuma wannan Alƙur'ãni bai kasance ga a ƙirƙira shi ba daga wanin Allah, kuma
amma shi gaskatawar wannan ne da yake a gabãninsa da bayãnin hukuncin littãffan
Allah, Bãbu shakka a cikinsa, daga Ubangijin halittu yake.
Kõ sunã cẽwa, "Yã ƙirƙira shi?" Ka ce: "Ku zo da sũra guda misãlinsa, kuma ku
kirãyi wanda kuka iya duka, baicin Allah, idan kun kasance mãsu gaskiya."
Ã'a, sun ƙaryata game da abin da ba su kẽwaye da saninsa ba, kuma fassararsa ba
ta riga ta jẽ musu ba. Kamar waɗancan ne waɗanda suke a gabãninsu. Sai ka dũba,
yãya ãƙibar azzãlumai ta kasance?
Kuma idan sun ƙaryata ka, to, ka ce: "Inã da aikĩna kuma kunã da aikinku, kũ
kuɓutattu ne daga abin da nake aikatãwa kuma ni kuɓutacce ne daga abin da kuke
aikatãwa."
Kuma rãnar da Yake tãra su, kamar ba su zauna ba fãce sa'a guda daga yini. Sunã
gãne jũna a tsakãninsu. Haƙĩƙa, waɗanda suka ƙaryata game da gamuwa da Allah sun
yi hasãra. Kuma ba su kasance mãsu shiryuwa ba.
Kuma imma dai, haƙĩƙa, Mu nũna maka sãshen abin da Muke yi musu alkawari, kõ
kuwa Mu karɓi ranka, to, zuwa gare Mu makõmarsu take. Sa'an nan kuma Allah ne
shaida a kan abin da suke aikatãwa.
Ka ce: "Ba na mallaka wa kaina wata cũta, haka kuma wani amfãni, sai abin da
Allah Ya so. Ga kõwace al'umma akwai ajali, idan ajalinsu ya zo, to, bã zã su yi
jinkiri daga gare shi ba, kõ dã sã'ã guda, kuma bã zã su gabãta ba."
Kuma dã kõwane rai wanda ya yi zãlunci yã mallaki duka abin da yake a cikin
ƙasa, to, dã yã yi fansa da shi. Kuma suka dinga nadãma a lõkacin da suka ga
azãba. Sa'an nan aka yi hukunci a tsakãninsu da ãdalci, kuma bã zã a zãlunce su
ba.
Ka ce: "Shin, kun ga abin da Allah Ya saukar sabõda ku na arziki, sai kuka sanya
hukuncin haramci da halacci a gare shi?" Ka ce: "Shin, Allah ne Ya yi muku izni,
ko ga Allah kuke ƙirƙirãwar ƙarya?"
Kuma mẽne ne zaton waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, a Rãnar ¡iyãma? Lalle
haƙĩƙa,Allah Ma, abũcin falala ne a kan mutãne, amma kuma mafi yawansu bã su
gõdẽwa.
Kuma ba ka kasance a cikin wani sha'ani ba, kuma ba ka karanta wani abin karatu
daga gare shi ba, kuma ba ku aikata wani aiki ba, fãce Mun kasance Halarce a
lõkacin da kuke zubuwa a cikinsa. Kuma wani ma'aunin zarra bã zai yi nĩsa ba
daga Ubangijinka a cikin ƙasa, haka kuma a cikin sama, kuma bãbu wanda yake mafi
ƙaranci daga haka, kuma bãbu mafi girma, fãce yana a cikin littãfi bayyananne.
To! Haƙĩƙa Allah Yanã da mulkin wanda ke a cikin sammai da wanda ke a cikin ƙasa
kuma waɗanda suke kiran wanin Allah, bã su biyar waɗansu abõkan tarẽwa (ga Allah
a MulkinSa). Bã su biyar kõme fãce zato. Kuma ba su zama ba fãce sunã ƙiri faɗi
kawai.
Suka ce: "Allah Ya riƙi ɗa." Tsarkinsa yã tabbata! Shi ne wadãtacce Yanã da
mallakar abin da yake, a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, A wurinku
bãbu wani dalĩli game da wannan! Shin, kunã faɗar abin da ba ku sani ba game da
Allah?
Jin dãɗi ne a cikin dũniya, sa'an nan kuma makõmarsu zuwa gare Mu take, sa'an
nan Mu ɗanɗana musu azãba mai tsanani sabõda abin da suka kasance sunã yi na
kãfirci.
Kuma ka karanta musu lãbãrin Nũhu, a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, "Ya
mutãnẽna! Idan matsayĩna da tunãtarwata ameda ãyõyin Allah sun kasance sun yi
nauyi a kanku, to, ga Allah na dõgara. Sai ku tãra al'amarinku, kũ da abũbuwan
shirkinku, sa'annan kuma kada al'amarinku ya kasance rufaffe a kanku, sa'an nan
kuma ku kashe ni, kada ku yi mini jinkiri."
"Kuma idan kuka jũya bãya, to, ban tambaye ku wata ijãra ba. ljãrata ba ta zama
ba fãce daga Allah, kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa."
Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan Muka kuɓutar da shi da wanda yake tãre da shi, a
cikin jirgi, kuma Muka sanya su mãsu mayẽwa, kuma Muka nutsar da waɗanda suka
ƙaryata ãyõyinMu. Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance.
Sa'an nan kuma Muka aika waɗansu Manzanni daga bãyansa zuwa ga mutãnensu, suka
jẽmusu da hujjõji bayyanannu, to, ba su kasance zã su yi ĩmãni ba sabõda sun
ƙaryata shi a gabani. Kamar wannan ne Muke rufẽwa a kan zukãtan mãsu ta'addi.
Sa'an nan kuma a bãyansu Muka aika Mũsa da Hãrũna zuwa ga Fir'auna da
mashãwartansa, tãre da ãyõyinMu. Sai suka kangara kuma sun kasance mutãne mãsu
laifi.
Suka ce: "Shin, ka zo mana ne dõmin ka jũyar da mu daga abin da muka iske
ubanninmu a kansa, kuma girma ya kasance gare ku, ku biyu a cikin ƙasa? Bã zã mu
zama mãsu ĩmãni ba sabõda ku."