Kuma da yẽkuwa daga Allah da ManzonSa zuwa ga mutãne, a Rãnar Haji Babba cẽwa
lallene Allah Barrantacce ne daga mãsu shirki, kuma ManzonSa (haka). To, idan
kun tũba to shi ne mafi alhẽri a gare ku, kuma idan kun jũya, to, ku sani lalle
ne kũ, bã mãsu buwãyar Allah ba ne. Kuma ka bãyar da bishãra ga waɗanda suka
kãfirta, da azãba mai raɗaɗi.
Sai waɗanda kuka yi wani alkawari daga mãsu shirki, sa'an nan kuma ba su rage ku
da kõme ba, kuma ba su taimaki kõwa a kanku ba, to, ku cika alkawarin, zuwa gare
su, har ga iyakar yarjẽjẽyarsu. Lalle ne Allah Yanã son mãsu taƙawa.
Kuma idan watanni, mãsu alfarma suka shige, to, ku yãki mushirikai inda kuka
sãmẽ su, kuma ku kãmã su, kuma ku tsare su, kuma ku zaune musu dukkan madãkata.
To, idan sun tũba, kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka to ku
sakar musu da hanyarsu. Lalle Allah ne Mai gãfara,Mai jin ƙai.
Idan wani daga mushirikai ya nemi maƙwabtakarka to, ka ba shi maƙwabtakar har ya
ji, maganar Allah, sa'an nan ka isar da shi ga wurin amincewarsa. Wancan fa
domin lalle ne su, mutãne ne waɗanda ba su sani ba.
Yãya wani alkawari a wurin Allah a wurin ManzonSa yake kasancẽwa ga mushirikai,
fãce ga waɗanda kuka yi wa alkawari wurin Masallaci Mai alfarma? To matuƙar sun
tsaya sõsai gare ku, sai ku tsayu sõsai gare su. Lalle ne Allah Yanã son mãsu
taƙawa.
Yãya, alhãli idan sun ci nasara a kanku, bã zã su tsare wata zumun ta ba a
cikinku, kuma haka wata amãna, sunã yardar da ku da bãkunansu kuma zukãtansu
sunã ƙi? Kuma mafi yawansu fãsiƙai ne.
Sa'an nan idan sun tũba kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka, to,
'yan'uwanku ne a cikin addini, kuma Munã rarrabe ãyõyi daki-daki, ga mutãne
waɗanda suke sani.
Kuma idan suka warware rantsuwõyin amãna daga bãyan alkawarinsu, kuma suka yi
sũka a cikin addininku, to, ku yaki shũgabannin kãfirci. Lalle ne sũ, bãbu
rantsuwõyin amãna a gare su. Tsammãninsu sunã hanuwa.
Shin, bã ku yaƙin mutãne, waɗanda suka warware rantsuwõyinsu, kuma suka yi niyya
ga fitar da Manzo, kuma sũ ne suka fãra muku, tun a farkon lõkaci? Shin kunã
tsõron su ne? To, Allah ne marfi cancantar ku ji tsõronSa, idan kun kasance
mũminai!
Kõ kunã zaton a bar ku, tun Allah bai bayyana waɗanda suka yi jihãdi ba daga
gare ku, kuma sũ ba su riƙi wani shigeba, baicin Allah da ManzonSa da mũminai?
Kuma Allah ne Mai jarrabãwa ga abin da kuke aikatãwa.
Bã ya kasancewa ga mãsu shirki su rãya masallatan Allah, alhãli kuwa sunã mãsu
bãyar da shaida a kan rãyukansu da kafirci, waɗannan ayyukansu sun ɓãci, kuma a
cikin wutã sũ madawwama
Abin sani kawai, mai rãya masallãtan Allah, shĩ ne wanda ya yi ĩmãni da Allah da
Rãnar Lãhira, kuma ya tsayar da salla kuma ya bãyar da zakka, kuma bai ji tsõron
kõwa ba fãce Allah. To, akwai tsammãnin waɗannan su kasance daga shiryayyu.
Shin, kun sanya shãyar da mahajjata da rãyar da Masallaci Mai alfarma kamar
wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya yi jihãɗi a cikin hanyar
Allah? Bã su daidaita a wurin Allah. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne
azzãlumai.
Waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihãdi, a cikin hanyar
Allah, da dũkiyõyinsu, da rãyukansu, sũ ne mafi girma ga daraja, a wurin Allah,
kuma waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi ubanninku da 'yan'uwanku masõya, idan
sun nũna son kãfirci a kan ĩmãni. Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to,
waɗannan sũ ne azzãlumai.
Ka ce: "Idan ubanninku da ɗiyanku da 'yan'uwanku da mãtanku da danginku da
dũkiyõyi, waɗanda kuka yi tsiwirwirinsu, da fatauci wanda kuke tsõron
tasgaronsa, da gidaje waɗanda kuke yarda da su, sun kasance mafiya sõyuwa a gare
ku daga Allah da ManzonSa, da yin jihãdi ga hanyarSa, to, ku yi jira har Allah
Ya zo da umurninSa! Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fãsiƙai."
Lalle ne, haƙĩƙa, Allah Yã taimake ku a cikin wurãre mãsu yawa, da Rãnar
Hunainu, a lõkacin da yawanku ya bã ku sha'awa, sai bai amfãnar da ku da kõme
ba, kuma ƙasa ta yi ƙunci a kanku da yalwarta, sa'an nan kuma kuka jũya kunã
mãsu bãyar da bãya.
Sa'an nan kuma Allah Ya saukar da natsuwarSa a kan ManzonSa kuma a kan mũminai,
kuma Ya saukar da rundunõni waɗanda ba ku gan su ba, kuma Ya azabtar da waɗanda
suka kãfirta: Wancan ne sakamakon kãfirai.
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai, mushirikai najasa ne, sabõda haka
kada su kusanci Masallaci Mai alfarma a bãyan shẽkararsu wannan. Kuma idan kun
ji tsõron talauci to, da sannu Allah zai wadãta ku daga falalarSa, idan Ya so.
Lalle Allah ne Masani, mai hikima.
Ku yãƙi waɗanda bã su yin ĩmãni da Allah kuma bã su ĩmãni da Rãnar Lãhira kumabã
su haramta abin da Allah da ManzonSa suka haramta, kuma bã su yin addini,
addinin gaskiya, daga waɗanda aka bai wa Littãfi, har sai sun bãyar da jizya
daga, hannu, kuma sunã ƙasƙantattu.
Kuma Yahũdãwa suka ce: "Uzairu ɗan Allah ne."Kuma Nasãra suka ce: "Masĩhu ɗan
Allah ne." Wancan zancensu ne da bãkunansu. Sunã kamã da maganar waɗanda suka
kãfirta daga gabãni. Allah Yã la'ance su! Yãya aka karkatar da su?
Sun riƙi mãlamansu (Yahũdu) da ruhubãnãwansu (Nasãra) Ubannangiji, baicin Allah,
kuma sun riƙi Masĩhu ɗan Maryama ( haka). Kuma ba a umurce su ba fãce da su
bautã wa Ubangiji Guda. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. TsarkinSa ya tabbata daga
barin abin da suke yin shirki da shi.
Yã waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle ne mãsu yawa daga Ahbãr da Ruhbãnãwa haƙĩƙa sunã
cin dũkiyar mutãne da ƙarya, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma waɗanda
suke taskacẽwar zĩnãriya da azurfa, kuma bã su ciyar da ita a cikin hanyar
Allah, to, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi.
A Rãnar da ake ƙõna shi a kanta a cikin wutar Jahannama, sai a yi lalas da ita
ga gõshinansu da sãshinansu da bãyayyakinsu, (a ce musu): "Wannan ne abin da
kuka taskace dõmin rãyukanku. To, ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã sanyãwa a
taska."
Lallai ne ƙidãyayyun watanni a wurin Allah watã gõma shã biyu ne a cikin
Littãfin Allah, a Rãnar da Ya halicci sammai da ƙasa daga cikinsu akwai huɗu
mãsu alfarma. Wannan ne addini madaidaici. Sabõda haka kada ku zãlunci kanku a
cikinsu. Kuma ku yãƙi mushirikai gabã ɗaya, kamar yadda suke yãƙar ku gabã ɗaya.
Kuma ku sani cẽwa lallai ne Allah Yanã tãre da mãsu taƙawa.
Abin sani kawai, "Jinkirtãwa" ƙãri ne a cikin kãfirci, anã ɓatar da waɗanda suka
kãfirta game da shi. Sunã halattar da watã a wata shẽkara kuma su haramtar da
shi a wata shẽkara dõmin su dãce da adadin abin da Allah Ya haramta. Sabõda haka
sunã halattar da abin da Allah Ya haramtar. An ƙawãce musu mũnanan ayyukansu.
Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne kãfirai.
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Mẽne ne a gare ku, idan ance muku, "Ku fita da yãƙi
a cikin hanyar Allah," sai ku yi nauyi zuwa ga ƙasa. Shin, kun yarda da rãyuwar
dũniya ne daga ta Lãhira? To jin dãɗin rãyuwar dũniya bai zama ba a cikin
Lãhira, fãce kaɗan.
Idan ba ku fita da yãƙi ba, Allah zai azabta ku da azãba mai raɗaɗi, kuma Ya
musanya wasu mutãne, wasunku (a maimakonku). Kuma bã zã ku cũtar da Shida kõme
ba. Kuma Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne.
Idan ba ku taimake shi ba, to, lalle ne Allah Yã taimake shi, a lõkacin da
waɗanda suka kãfirta suka fitar da shi, Yanã na biyun biyu, a lõkacin da suke
cikin kõgon dũtse, a lõkacin da yake cẽwa da sãhibinsa: "Kada ka yi baƙin ciki,
lalle ne Allah Yanã tãre da mu." Sai Allah Ya saukar da natsuwarSa a kansa, kuma
Ya taimake shi da waɗansu rundunõni, ba ku gan su ba, kuma Ya sanya kalmar
waɗanda suka kãfirta maƙasƙanciya, kuma kalmar Allah ita ce maɗaukakiya. Kuma
Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima.
Ku fita da yãƙi kunã mãsu sauƙãƙan kãyã da mãsu nauyi, kuma ku yi jihãdi da
dũkiyõyinku da kuma rãyukanku a cikin hanyar Allah. Wancan ne mafi alhẽri a gare
ku, idan kun kasance kunã sani.
Dã yã kasance wata siffar dũniya ce: makusanciya, da tafiya matsakaiciya, dã sun
bĩ ka, kuma amma fagen yã yi musu nĩsa.Kuma zã su yi ta yin rantsuwa da Allah,
"Dã mun sãmi dãma, dã mun tafi tare da ku." Sunã halakar da kansu (da rantsuwar
ƙarya) ne, kuma Allah Yanã sanin lalle, haƙĩƙa, sumaƙaryata ne.'
Waɗanda suke yin ĩmãnida Allah da Rãnar Lãhira, bã zã su nẽmi izininka ga yin,
jihãdida dũkiyõyinsu da rãyukansu ba. Kuma Allah ne Masani ga mãsu taƙawa.
Abin sani kawai, waɗanda bã sa ĩmãni da Allah, da Rãnar Lãhira, kuma zukãtansu
suka yi shakka, sũ ne ke nẽman izininka, sa'an nan a cikin shakkarsu sunã ta yin
kai kãwo.
Kuma dã sun yi nufin fita, dã sun yi wani tattali sabõda shi, kuma amma Allah Ya
ƙi zãburarsu, sai Ya nauyayar da zamansu. Kuma aka ce ku zauna tãre da mãsu
zama.
Dã sun fita a cikinku bã zã su ƙãre ku da kõme ba fãce da ɓarna, kuma lalle dã
sun yi gaggãwar sanya annamĩmanci a tsakãninku, sunã nẽma muku fitina. Kuma a
cikinku akwai 'yan rahõto sabõda su. Kuma Allah ne Masani ga azzãlumai,
Kuma lalle ne, haƙĩƙa sun nẽmi fitina daga gabãni, kuma, suka jũya maka
al'amari, har gaskiya ta zo, kuma umurnin Allah Ya bayyana, alhãli sunã mãsu
ƙyãma,
Kuma daga cikinsu akwai mai cẽwa, "Ka yi mini izinin zama, kuma kada ka fitine
ni." To, a cikin fitinar suka fãɗa. Kuma lalle ne Jahannama, haƙĩƙa, mai
ƙẽwayẽwa ce ga kãfirai.
Idan wani alhẽri ya sãme ka, zai ɓãta musu rai, kuma idan wata masifa ta sãme ka
sai su ce: "Haƙĩƙa, mun riƙe al'amarinmu daga gabãni."Kuma sujũya, alhãli kuwa
sunã mãsu farin ciki.
Ka ce: "Shin, kunã dãko ne da mu? Fãce dai da ɗayan abũbuwan biyu mãsu kyau,
alhãli kuwa mũ, munã dãko da ku, AllahYa sãme ku da wata azãba daga gare Shi, kõ
kuwa da hannayenmu. To, ku yi dãko. Lalle ne mũ, tãre da ku mãsu dãkon ne."
Kuma bãbu abin da ya hana a karɓi ciyarwarsu daga gare su fãce dõmin sũ, sun
kãfirta da Allah da ManzonSa, kuma bã su zuwa ga salla fãce Luma sunã mãsu
kasãla, kuma bã su ciyarwa fãce sunã mãsu ƙyãma.
Sabõda haka, kada dũkiyõyinsu su bã ka sha'awa, kuma haka 'ya'yansu. Abin sani
kawai, Allah Yanã nufin Ya yi musu azãba, da su a cikin rãyuwar dũniya, kuma
rãyukansu su fita alhãli kuwa sunã kãfirai.
Kuma daga cikinsu akwai wanda yake zunɗen ka a kan sha'anin dũkiyõyin sadaka,
sai idan an bã su daga cikinta, su yarda, kuma idan ba a bã su ba daga cikinta
sai su zamo sunã mãsu fushi.
Kuma dã dai su lalle sun yarda da abin da Allah Ya bã su, da ManzonSa kuma suka
ce: "Ma'ishinmu Allah ne, zai kãwo mana daga falalarSa kuma ManzõnSa (zai bã
mu). Lalle ne mũ, zuwa ga Allah mãsu kwaɗayi ne."
Abin sani kawai, dũkiyõyin sadaka na faƙĩrai ne da miskinai da mãsu aiki a
kansu, da waɗanda ake lallãshin zukãtansu, kuma a cikin fansar wuyõyi, da
mabarta, da a cikin hanyar Allah da ɗan hanya (matafiyi). Farilla daga Allah.
Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.
Kuma daga cikinsu akwai waɗanda suke cũtar Annabi, kuma sunã cẽwa "Shi kunne
ne." Ka ce: "Kunnen alhẽri gare ku,Yanã ĩmãni da Allah, kuma Yanã yarda da
mũminai, kuma rahama ne ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare ku."Kuma waɗanda suke
cũtar Manzon Allah sunã da azãba mai raɗaɗi.
Shin, ba su sani ba cẽwa "Lalle ne wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, haƙĩƙa
Yanã da wutar Jahannama, Yanã madawwami a cikinta? Waccan ita ce wulãkantãwa
babba!"
Munãfukai sunã tsõron a saukar da wata sũra a kansu,wadda take bã su lãbãri ga
abin da yake cikin zukãtansu. Ka ce: "Ku yi izgili. Lalle ne, Allah ne Mai fitai
da abin da kuke tsõro."
Kuma lalle ne, idan ka tambaye , su haƙĩƙa, sunã cẽwa, "Abin sani kawai, mun
kasance munã hĩra kuma munã wãsã. Ka ce: "Shin da Allah, da kuma ãyõyinSa da
ManzonSa kuka kasance kunã izgili?"
"Kada ku kãwo wani uzuri, haƙĩƙa, kun kãfirta a bãyanĩmãninku. Idan Mun yãfe
laifi ga wata ƙungiya daga gare ku, zã Mu azabta wata ƙungiya sabõda, lalle, sun
kasance mãsu laifi."
Munãfukai maza da munãfukai mãtã, sãshensu daga sãshe, sunã umurni da abin ƙi
kuma sunã hani daga alhẽri.Kuma sunã damƙẽwar hannayensu.Sun mance Allah, sai Ya
mantã da su. Lalle ne munãfukai sũ ne fãsiƙai.
Allah yã yi wa'adi ga munãfukai maza da munãfukai mãtã da kãfirai da wutar
Jahannama, sunã madawwama a cikinta. Ita ce ma'ishiyarsu. Kuma Allah Yã la'ance
su, kuma sunã da azãba zaunanniya.
Kamar waɗanda suke a gabãninku, sun kasance mafi tsananin ƙarfi daga gare ku,
kuma mafi yawan dũkiyõyi da ɗiya. Sai suka ji daɗi da rabonsu, sai kuka ji daɗi
da rabonku kamar yadda waɗanda suke a gabãninku suka ji dãɗi, da rabonsu, kuma
kuka kũtsa kamar kũtsãwarsu. Waɗancan ayyukansu sun ɓãci a dũniya da Lãhira,
kuma waɗannan sũ ne mãsu hasãra.
Shin lãbarin waɗanda suke a gabãninsu bai je musu ba, mutãnen Nũhu da Ãdãwa da
Samũdãwa da mutãnen Ibrãhĩm da Ma'abũta Madyana da waɗanda aka birkice?
Manzanninsu sun jẽ musu da ãyõyayi bayanannu. To, Allah bai kasance Yanã
zãluntar su ba, amma sun kasance rãyukansu suke zãlunta.
Kuma mummunai maza da mummunai mãtã sãshensu majiɓincin sãshe ne, sunã umurni da
alhẽri kuma sunã hani daga abin da bã a so, kuma sunã tsayar da salla, kuma sunã
bãyar da zakka, kuma sunãɗã'a ga Allah da ManzonSa. Waɗannan Allah zai yi musu
rahama. Lalle Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima.
Kuma Allah Yã yi wa'adi ga mummunai maza da mummunai mãtã da gidãjen Aljanna
ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwamã a cikinsu, da wurãren zama
mãsu dãɗi a cikin gidãjen Aljannar. Kuma yarda daga Allah ce mafi girma. Wancan
shi ne babban rabo, mai girma.
Sunã rantsuwa da Allah, ba su faɗa ba, alhãli kuwa lalle ne, haƙĩƙa, sun faɗi
kalmar kãfirci, kuma; sun kãfirta a bãyan musuluntarsu, kuma sun yi himma ga
abin da ba su sãmu ba. Kuma ba su zargi kõme ba fãce dõmin Allah da ManzonSa Ya
wadãtar da su daga falalarSa. To, idan sun tũba zai kasance mafi alhẽri gare
su,kuma idan sun jũya bãya, Allah zaiazabtã su da azãba mai raɗaɗi a cikin
dũniya da Lãhira, kuma bã su da wani masõyi kõ wani mataimaki a cikin kasa.
Kuma daga cikinsu akwai wadɗanda suka yi wa Allah alkawari, "Lalle ne idan ya
kãwo mana daga falalarSa, haƙĩƙa, munãbãyar da sadaka, kuma lalle ne munã
kasancẽwa, daga sãlihai."
Sai Ya biyar musu da munãfunci a cikin zukatansu har zuwa ga Rãnar da suke
haɗuwa da Shi sabõda sãɓã wa Allah a abin da suka yi Masa alkawari, kuma sabõda
abin da suka kasance sunã yi na ƙarya.