Suna tambayar ka ga ganĩma. ka ce: "Ganĩma ta Allah daManzonSa ce. Sai ku bi
Allah da taƙawa, kuma ku gyãra abin da yake a tsakãninku, kuma ku yi ɗã'a ga
Allah da ManzonSa, idan kun kasance mũminai."
Abin sani kawai, nũminai sũ ne waɗanda suke idan an ambaci, Allah, zukãtansu su
firgita, kuma idan an karanta ãyõyinSa a kansu, su ƙãrã musu wani ĩmãni, kuma ga
Ubangijinsu suke dõgara.
Kuma a lõkacin da Allah Yake yi muku alkawari da ɗayan ƙungiya biyu, cẽwa lalle
ita tãku ce: kuma kunã gũrin cẽwa lalle ƙungiya wadda bã ta da ƙaya ta kasance
gare ku, kuma Allah Yanã nufin Ya tabbatar da gaskiya da kalmõminSa, kuma Ya
kãtse ƙarshen kãfirai;
Kuma Allah bai sanya shi ba fãce Dõmin bishãra, kuma dõmin zukãtanku su natsu da
shi, kuma taimakon, bai zama ba fãce daga wurin Allah; Lalle ne Allah Mabuwãyi
ne, Mai hikima.
A lõkacin da (Allah) Yake rufe ku da gyangyaɗi, ɗõmin aminci daga gare Shi, kuma
Yanã saukar da ruwa daga sama, a kanku, dõmin Ya tsarkake ku da shi, kuma Ya
tafiyar da ƙazantar Shaiɗan daga barinku, kuma dõmin Ya ɗaure a kan zukãtanku,
kuma Ya tabbatar da ƙafãfu da shi.
A lõkacin da Ubangijinka Yake yin wahayi zuwa ga Malã'iku cẽwa: "Lalle ne Ni,
Inã tãre da ku, sai ku tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni: Zã Ni jẽfa tsõro a
cikin zukãtan waɗanda suka kãfirta, sai ku yi dũka bisa ga wuyõyi kuma ku yi
dũka daga gare su ga dukkan yãtsu .
Kuma duka wanda ya jũya musu bãyansa a yinin nan, fãce wanda ya karkata dõmin
kõɗayya, kõ kuwa wanda ya jẽ dõmin haɗuwa da wata ƙungiya, to, lalle ne ya kõma
da fushi daga Allah, kuma matattararsa Jahannama, kuma tir da makõma ita!
To, bã kũ ne kuka kashe su ba; kuma amma Allah ne Ya kashe su: kuma ba ka yi
jĩfa ba a lõkacin da ka yi jĩfa; kuma amma Allah ne Ya yi jĩfar. Kuma dõminYa
jarraba Musulmi da jarrabãwa mai kyau daga gare shi. Kuma Allah Mai ji ne,
Masani.
Idan kun yi alfãnun cin nasara to lalle nasarar tã je muku, kuma idan kun hanu,
to Shi ne Mafi alhẽri a gare ku, kuma idan kun kõma zã Mu kõma, kuma jama'arku
bã zã ta wadãtar muku da kõme ba, kõ dã tã yi yawa. Kuma lalle ne cẽwa Allah
Yanã tãre da mũminai!
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku karɓa wa Allah, kuma ku karɓa wa Manzo, idan Ya
kirãye ku zuwa ga abin da Yake rãyar da ku; Kuma ku sani cẽwa Allah Yanã
shãmakacẽwa a tsakãnin mutum da zũciyarsa, kuma lalle ne Shĩ, a zuwa gare Shi
ake tãra ku.
Ku tuna a lõkacin da kuke kaɗan, waɗanda ake raunanarwã a cikin ƙasa kunã tsõron
mutãne su cafe ku, sai Ya tattara ku (a wurin natsuwa, Maɗina), kuma Ya ƙarfafã
ku da taimakonSa kuma Ya azurtã ku daga abũbuwa mãsu dãɗi; Tsammãninku, kunã
gõdẽwa.
Ya kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun bi Allah da taƙawa, zai sanyã muku
mararraba (da tsõro) kuma Ya kankare ƙanãnan zunubanku daga barinku. Kuma Ya
gãfartã muku. Kuma Allah ne Ma'abũcin falalã Mai girma.
Kuma a lõkacin da waɗanda suka kãfirta sukẽ yin mãkirci game da kai, dõmin su
tabbatar da kai, kõ kuwa su kashe ka, kõ kuwa su fitar da kai, sunã mãkirci kuma
Allah Yanã mayar musa da mãkirci kuma Allah ne Mafificin mãsu mãkirci.
Kuma idan aka karanta, ãyõyinMu a kansu, sukan ce: "Lalle ne mun ji dã muna so,
haƙĩƙa, da mun faɗi irin wannan; wannan bai zama ba fãce tãtsunãyõyin mutãnen
farko."
A lõkacin da suka ce: "Yã Allah! Idan wannan ya kasancc shĩ ne gaskiya daga
wurinKa, sai Ka yi ruwan duwãtsu, a kanmu, daga sama, kõ kuwa Kazõ mana da wata
azãba, mai raɗaɗi."
Kuma mẽne ne a gare su da Allah ba zai yi musu azãba ba, alhãli kuwa sũ, sunã
kangẽwa daga Masallaci Mai alfarma kuma ba su kasance majiɓintanSa ba? Bãbu
majiɓintanSa fãce mãsu taƙawa. Kuma mafi yawansu ba su sani ba.
Lalle ne waɗanda suka kãfirta, sunã ciyar da dũkiyõyinsu, dõmin su kange daga
hanyar Allah; to, zã a su ciyar da ita, sa' an nan kuma ta kasance nadãma a
kansu, sa'an nan kuma a rinjãye su. Kuma waɗanda suka kãfirta zuwa ga Jahannama
ake tãra su;
Dõmin Allah Ya rarrabe mummũna daga mai kyau, kuma Ya sanya mummũnan, sãshensa a
kan sãshe, sa'an nan Ya shirga shi gabã daya, sa'an nan Ya sanyã shi a cikin
Jahannama. Waɗannan sũ ne mãsu hasãra.
Ka ce wa waɗanda suka kãfirta, idan sun hanu, zã a gãfarta musu abin da ya riga
ya shige, kuma idan sun kõma, to, hanyar kãfiran farko, haƙĩƙa, ta shũɗe.
Kuma ku yãƙe su har wata fitina bã zã ta kasance ba, kuma addini dukansa ya
kasance na Allah. To, idan sun hanu to lalle ne, Allah ia abin da kuke aikatãwa
Mai gani ne.
Kuma ka sani, abin sani kawai, abin da kuka sãmi ganĩma daga wani abu, to, lalle
ne Allah Yanã da humusinsa kuma da Manzo, kuma da mãsu zumunta, da marãyu da
miskĩnai da ɗan hanya, idan kun kasance kun yi ĩmãni da Allah da abin da Muka
saukar a kan bãwanMu a Rãnar Rarrabẽwa, a Rãnar da jama'a biyu suka haɗu, kuma
Allah ne, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi.
A lõkacin da kuke a gãɓa ta kusa sũ kuma sunã a gãɓa tanẽsa, kuma ãyarin yana a
wuri mafi gangarãwa daga gare ku, kuma dã kun yi wa jũna wa'adi, dã kun sãɓa ga
wa'adin; kuma amma dõmin Allah Ya hukunta abin da yake ya kasance abin aikatãwa.
Dõmin wanda yake halaka ya halaka daga shaida, kuma mai rãyuwa ya rãyu daga
shaida, kuma lalle Allah ne, haƙĩƙa, Mai ji Masani.
A lõkacin da Allah Yake nũna maka sũ sunã kaɗan, a cikin barcinka, kuma dã Ya
nũna maka su sunã da, yawa, lalle ne dã kun ji tsõro, kuma lalle ne dã kun yi
jãyayya a cikin al'amarin, kuma amma Allah Yã tsare ku: Lalle Shĩ ne Masani ga
abin da yake a cikin ƙirãza.
Kuma a lõkacin da Yake nũna muku su, a lõkacin da kuka haɗu, a cikin idanunku
sunã kaɗan, kuma Ya ƙarantar da ku a cikin idanunsu dõmin Allah Ya hukunta wani
al'amari wanda ya kasance abin aikatãwa. Kuma zuwa ga Allah ake mayar da
al'umurra.
Kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, kuma kada ku yi jãyayya har ku raunana
kuma iskarku ta tafi, kuma ku yi haƙuri. Lalle ne Allah Yanã tãre da mãsu
haƙuri.
Kada ku kasance kamar waɗanda suka fita daga gidãjensu , sunã mãsu alfahari da
yin riya ga mutãne, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma Allah ne ga abin
da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa.
Kuma a lõkacin da Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, kuma ya ce: "Bãbu marinjayi
a gareku a yau daga mutãne, kuma nĩ maƙwabci ne gare ku." To, a lõkacin da
ƙungiya biyu suka haɗu, ya kõma a kan digãdigansa, kuma ya ce: "Lalle ne nĩ
barrantacce ne daga gare ku! Nĩ inã ganin abin da bã ku gani; ni inã tsõron
Allah: Kuma Allah Mai tsananin uƙũba ne."
A lõkacin da munãfukai da waɗanda suke akwai cũtã a cikin zukãtansu, suke cẽwa:
"Addĩnin waɗannan yã rũɗe su" Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to, lalle ne Allah
Mabuwãyi ne, Mai hikima.
"Kamar al'ãdar mutãnen Fir'auna da waɗanda suke gabãninsu, sun kãfirta da ãyõyin
Allah, sai Allah Ya kãma su da zunubansu. Lalle Allah ne Mai ƙarfi, Mai tsananin
uƙũba.
"Wancan ne, dõmin lalle ne, Allah bai kasance Mai canza wata ni'ima wadda ya
ni'imtar da ita a kan wasu mutãne ba fãce sun sãke abin da yake ga rãyukansu,
kuma dõmin lalle Allah ne Mai jĩ,Masani."
Kamar al'adar mutãnen Fir'auna da waɗanda suke a gabãninsu, sun ƙaryata game da
ãyõyin Ubangijinsu, sai Muka halaka su, sabõda zunubansu, kuma Muka nutsar da
mutãnen Fir'auna. Kuma dukansu sun kasance ne mãsu zãlunci.
Kuma ku yi tattali, dõminsu, abin da kuka sãmi ĩkon yi na wani ƙarfi, kuma da
ajiye dawaki, kunã tsoratarwa, game da shi, ga maƙiyin Allah kuma maƙiyinku da
wasu, baicin su, ba ku san su ba, Allah ne Yake sanin su, kuma abin da kuka
ciyar daga wani abu a cikin hanyar Allah, zã a cika muku sakamakonsa, kuma kũ ba
a zãluntar ku.
Kuma Ya sanya sõyayya a tsakãnin zukãtansu. Dã kã ciyar da abin da yake cikin
ƙasa, gabã ɗaya, dã ba ka sanya sõyayya a tsakãnin zukãtansu ba, kuma amma Allah
Yã sanya sõyayya a tsakãninsu. Lalle Shi ne Mabuwãyi, Mai hikima.
Ya kai Annabi! Ka kwaɗaitar da mũminai a kan yãƙi. Idan mutum ashirin mãsu
haƙuri sun kasance daga gare ku, zã su rinjãyi mẽtan kuma idan ɗari suka kasance
daga gare ku, zã su rinjãyi dubu daga waɗanda suka kãfirta, dõmin sũ, mutãne ne
bã su fahimta.
A yanzu Allah Yã sauƙaƙe daga gare ku, kuma Yã sani cẽwa lalle ne akwai mãsu
rauni a cikinku. To, idan mutum ɗari, mãsu haƙuri, suka kasance daga gare ku, zã
su rinjãyi mẽtan, kuma idan dubu suka kasance daga gare ku, zã su rinjãyi dubu
biyu, da iznin Allah. Kuma Allah Yanã tãre da mãsu haƙuri.
Bã ya kasancewa ga wani annabi, kãmammu su kasance a gare shi sai (bãyan) yã
zubar da jinainai a cikin ƙasa. Kunã nufin sifar dũniya kuma Allah Yanãnufin
Lãhira. Kuma Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima.
Ya kai Annabi! Ka ce wa wanda yake a cikin hannãyenku daga kãmammu: "Idan Allah
Ya san akwai wani alhẽri a cikin zukãtanku, zai kawo muku mafi alhẽri daga abin
da aka karɓa daga gare ku, kuma Ya yi muku gãfara. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai
jin ƙai."
Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihãdi da
dũkiyõyinsuda rãyukansu, a cikin hanyar Allah, da waɗanda suka bãyar da masauki,
kuma suka yi taimako. Waɗancan, sãshensu waliyyai ne ga sãshe. Kuma waɗanda suka
yi ĩmãni kuma ba su yi hijira ba, bã ku da wani abu daga waliccinsu, sai sun yi
hijira. Kuma idan suka nẽme ku taimako a cikin addini, to taimako yã wajaba a
kanku, fãce a kan mutãne waɗanda a tsakãninku da tsakãninsu akwai wani alkwari.
Kuma Allah ne, ga abin da kuke aikatãwa, Mai gani.
Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka yi hijira, kuma suka yi Jihãdi, a cikin
hanyar Allah, kuma da waɗanda suka bãyar da masauki, kuma suka yi tamiako,
waɗannan sũ ne mũminai da gaskiya, sunãda gãfara da wani abinci na karimci.
Kuma waɗanda suka yi ĩmãni daga bãya, kuma suka yi hijira kuma suka yi jihãdi
tãre da ku, to, waɗannan daga gare ku suke. Kuma ma'abũta zumunta, sãshensu ne
waliyyan sãshe a cikin Littãfin Allah. Lalle Allah ne ga dukkan kõme Masani.