Prev

101. Surah Al-Qri'ah سورة القارعة

Next
First Ayah   1   الأية الأولي
بِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
الْقَارِعَةُ
Hausa
 
Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsro)!

Ayah   101:2   الأية
مَا الْقَارِعَةُ
Hausa
 
Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa?

Ayah   101:3   الأية
وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْقَارِعَةُ
Hausa
 
Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa?

Ayah   101:4   الأية
يَوْمَ يَكُونُ النَّاسُ كَالْفَرَاشِ الْمَبْثُوثِ
Hausa
 
Rnar da mutne za su kasance kamar 'ya'yan fari msu wtsuwa.

Ayah   101:5   الأية
وَتَكُونُ الْجِبَالُ كَالْعِهْنِ الْمَنفُوشِ
Hausa
 
Kuma duwtsu su kasance kamar gshin sũfin da aka saɓe.

Ayah   101:6   الأية
فَأَمَّا مَن ثَقُلَتْ مَوَازِينُهُ
Hausa
 
To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi.

Ayah   101:7   الأية
فَهُوَ فِي عِيشَةٍ رَّاضِيَةٍ
Hausa
 
To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda.

Ayah   101:8   الأية
وَأَمَّا مَنْ خَفَّتْ مَوَازِينُهُ
Hausa
 
Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bbu nauyi).

Ayah   101:9   الأية
فَأُمُّهُ هَاوِيَةٌ
Hausa
 
To, uwarsa Hwiya ce.

Ayah   101:10   الأية
وَمَا أَدْرَاكَ مَا هِيَهْ
Hausa
 
Kuma me ya sanar da kai mece ce ita?

Ayah   101:11   الأية
نَارٌ حَامِيَةٌ
Hausa
 
Wata wuta ce mai zafi.

EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us