1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
وَالطُّورِ
Wattoor
Hausa
Ină rantsuwa da ¦ũr (Dũtsen Mũsă).
|
Ayah 52:2 الأية
وَكِتَابٍ مَّسْطُورٍ
Wakitabin mastoor
Hausa
Da wani littăfi rubũtacce.
|
Ayah 52:3 الأية
فِي رَقٍّ مَّنشُورٍ
Fee raqqin manshoor
Hausa
A cikin wata takardar făta shimfiɗaɗɗa.
|
Ayah 52:4 الأية
وَالْبَيْتِ الْمَعْمُورِ
Walbayti almaAAmoor
Hausa
Da Gidan da aka răyar da shi (da ibăda).
|
Ayah 52:5 الأية
وَالسَّقْفِ الْمَرْفُوعِ
Wassaqfi almarfooAA
Hausa
Da rufin nan da aka ɗaukaka.
|
Ayah 52:6 الأية
وَالْبَحْرِ الْمَسْجُورِ
Walbahri almasjoor
Hausa
Da tẽkun nan da aka cika (da ruwa).
|
Ayah 52:7 الأية
إِنَّ عَذَابَ رَبِّكَ لَوَاقِعٌ
Inna AAathaba rabbika lawaqiAA
Hausa
Lalle, azăbar Ubangijinka, haƙĩƙa, mai aukuwa ce.
|
Ayah 52:8 الأية
مَّا لَهُ مِن دَافِعٍ
Ma lahu min dafiAA
Hausa
Bă ta da mai tunkuɗẽwa.
|
Ayah 52:9 الأية
يَوْمَ تَمُورُ السَّمَاءُ مَوْرًا
Yawma tamooru assamao mawra
Hausa
Rănar da samă ke yin mőtsi tană kai kăwo.
|
Ayah 52:10 الأية
وَتَسِيرُ الْجِبَالُ سَيْرًا
Wataseeru aljibalu sayra
Hausa
Kuma duwătsu nă tafiya sună shũɗẽwa.
|
Ayah 52:11 الأية
فَوَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Fawaylun yawma-ithin lilmukaththibeen
Hausa
To, bone yă tabbata a rănar nan ga măsu ƙaryatăwa.
|
Ayah 52:12 الأية
الَّذِينَ هُمْ فِي خَوْضٍ يَلْعَبُونَ
Allatheena hum fee khawdinyalAAaboon
Hausa
Waɗanda suke a cikin kududdufi sună wăsă.
|
Ayah 52:13 الأية
يَوْمَ يُدَعُّونَ إِلَىٰ نَارِ جَهَنَّمَ دَعًّا
Yawma yudaAAAAoona ila narijahannama daAAAAa
Hausa
Rănar da ză a tunkuɗa su zuwa wutar Jahannama, tunkuɗăwa.
|
Ayah 52:14 الأية
هَٰذِهِ النَّارُ الَّتِي كُنتُم بِهَا تُكَذِّبُونَ
Hathihi annaru allateekuntum biha tukaththiboon
Hausa
(A ce musu): "Wannan ita ce wutar da kuka kasance kună ƙaryatăwa game da ita."
|
Ayah 52:15 الأية
أَفَسِحْرٌ هَٰذَا أَمْ أَنتُمْ لَا تُبْصِرُونَ
Afasihrun hatha am antum latubsiroon
Hausa
"To, shin wannan sihiri ne kő kuwa kũ ne bă ku gani?"
|
Ayah 52:16 الأية
اصْلَوْهَا فَاصْبِرُوا أَوْ لَا تَصْبِرُوا سَوَاءٌ عَلَيْكُمْ ۖ إِنَّمَا
تُجْزَوْنَ مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Islawha fasbirooaw la tasbiroo sawaon AAalaykum innamatujzawna ma kuntum
taAAmaloon
Hausa
"Ku shigẽ ta. To, ku yi haƙuri ko kuma kada ku yi haƙuri, dai dai ne a kanku,
kawai ană yi muku sakamakon abin da kuka kasance kună aikatăwa."
|
Ayah 52:17 الأية
إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي جَنَّاتٍ وَنَعِيمٍ
Inna almuttaqeena fee jannatinwanaAAeem
Hausa
Lalle, măsu taƙawa, sună a cikin gidăjen Aljanna da wata ni'ima.
|
Ayah 52:18 الأية
فَاكِهِينَ بِمَا آتَاهُمْ رَبُّهُمْ وَوَقَاهُمْ رَبُّهُمْ عَذَابَ الْجَحِيمِ
Fakiheena bima atahumrabbuhum wawaqahum rabbuhum AAathaba aljaheem
Hausa
Sună măsu jin dăɗi da abin da Ubangijinsu Ya ba su, kuma Ubangijinsu Ya tsăre
musu azăbar Jahĩm.
|
Ayah 52:19 الأية
كُلُوا وَاشْرَبُوا هَنِيئًا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Kuloo washraboo hanee-an bimakuntum taAAmaloon
Hausa
(A ce musu): "Ku ci, ku sha, da ni'ima, dőmin abin da kuka kasance kună
aikatăwa."
|
Ayah 52:20 الأية
مُتَّكِئِينَ عَلَىٰ سُرُرٍ مَّصْفُوفَةٍ ۖ وَزَوَّجْنَاهُم بِحُورٍ عِينٍ
Muttaki-eena AAala sururin masfoofatinwazawwajnahum bihoorin AAeen
Hausa
Sună kishingiɗe a kan karagu waɗanda ke cikin sahu, kuma Muka aurar da su
waɗansu mătă măsu farin idănu, măsu girmansu.
|
Ayah 52:21 الأية
وَالَّذِينَ آمَنُوا وَاتَّبَعَتْهُمْ ذُرِّيَّتُهُم بِإِيمَانٍ أَلْحَقْنَا بِهِمْ
ذُرِّيَّتَهُمْ وَمَا أَلَتْنَاهُم مِّنْ عَمَلِهِم مِّن شَيْءٍ ۚ كُلُّ امْرِئٍ
بِمَا كَسَبَ رَهِينٌ
Wallatheena amanoo wattabaAAat-humthurriyyatuhum bi-eemanin alhaqnabihim
thurriyyatahum wama alatnahum minAAamalihim min shay-in kullu imri-in bima
kasaba raheen
Hausa
Kuma waɗanda suka yi ĩmăni kuma zũriyarsu suka bĩ su ga ĩmănin, Mun riskar da
zũriyarsu da su, alhăli kuwa bă da Mun rage musu kőme ba daga aikinsu, kőwane
mutum jingina ne ga abin da ya sana'anta.
|
Ayah 52:22 الأية
وَأَمْدَدْنَاهُم بِفَاكِهَةٍ وَلَحْمٍ مِّمَّا يَشْتَهُونَ
Waamdadnahum bifakihatin walahminmimma yashtahoon
Hausa
Kuma Muka yalwata musu 'ya'yan ităce da năma irin wanda suke marmari.
|
Ayah 52:23 الأية
يَتَنَازَعُونَ فِيهَا كَأْسًا لَّا لَغْوٌ فِيهَا وَلَا تَأْثِيمٌ
YatanazaAAoona feeha ka/san lalaghwun feeha wala ta/theem
Hausa
Sună mĩƙa wa jũnansu a cikinta hinjălan giya, wadda băbu yăsassar magana a
cikinta, kuma băbu jin nauyin zunubi.
|
Ayah 52:24 الأية
وَيَطُوفُ عَلَيْهِمْ غِلْمَانٌ لَّهُمْ كَأَنَّهُمْ لُؤْلُؤٌ مَّكْنُونٌ
Wayatoofu AAalayhim ghilmanunlahum kaannahum lu/luon maknoon
Hausa
Kuma waɗansu samări nă gẽwayăwa a kansu, kamar dai sũ lu'ulu'u ne wanda ke
kulle.
|
Ayah 52:25 الأية
وَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَسَاءَلُونَ
Waaqbala baAAduhum AAala baAAdinyatasaaloon
Hausa
Waɗansunsu suka fuskanta zuwa ga waɗansu, sună tambayar jũna.
|
Ayah 52:26 الأية
قَالُوا إِنَّا كُنَّا قَبْلُ فِي أَهْلِنَا مُشْفِقِينَ
Qaloo inna kunna qablufee ahlina mushfiqeen
Hausa
Suka ce: "Lalle mũ mun kasance a gabănin wannan (a dũniya ) a cikin iyălanmu
mună jin tsőro."
|
Ayah 52:27 الأية
فَمَنَّ اللهُ عَلَيْنَا وَوَقَانَا عَذَابَ السَّمُومِ
Famanna Allahu AAalayna wawaqanaAAathaba assamoom
Hausa
"To, Allah Yă yi mana kyautar falala, kuma Yă tsare mana azăbar iskar zăfi."
|
Ayah 52:28 الأية
إِنَّا كُنَّا مِن قَبْلُ نَدْعُوهُ ۖ إِنَّهُ هُوَ الْبَرُّ الرَّحِيمُ
Inna kunna min qablu nadAAoohuinnahu huwa albarru arraheem
Hausa
"Lalle mũ mun kasance, a găbanin haka, mună kiran sa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai
kyautatăwa, Mai rahama."
|
Ayah 52:29 الأية
فَذَكِّرْ فَمَا أَنتَ بِنِعْمَتِ رَبِّكَ بِكَاهِنٍ وَلَا مَجْنُونٍ
Fathakkir fama anta biniAAmatirabbika bikahin wala majnoon
Hausa
To, ka tunătar kai fa sabőda ni'imar Ubangjinka, bă bőka kake ba, kuma bă
mahaukaci ba.
|
Ayah 52:30 الأية
أَمْ يَقُولُونَ شَاعِرٌ نَّتَرَبَّصُ بِهِ رَيْبَ الْمَنُونِ
Am yaqooloona shaAAirun natarabbasubihi rayba almanoon
Hausa
Shin ză su ce: "Mawăƙi ne, mună jiran, masĩfun mutuwa game da shĩ"?
|
Ayah 52:31 الأية
قُلْ تَرَبَّصُوا فَإِنِّي مَعَكُم مِّنَ الْمُتَرَبِّصِينَ
Qul tarabbasoo fa-innee maAAakum minaalmutarabbiseen
Hausa
Ka ce: "Ku yi jira, domin nĩ ma lalle ină a cikin măsu jira tăre da ku."
|
Ayah 52:32 الأية
أَمْ تَأْمُرُهُمْ أَحْلَامُهُم بِهَٰذَا ۚ أَمْ هُمْ قَوْمٌ طَاغُونَ
Am ta/muruhum ahlamuhum bihathaam hum qawmun taghoon
Hausa
Shin, hankulansu ne ke umarin su da wannan, kő kuwa sũ wasu mutăne ne măsu
ƙetare haddi?
|
Ayah 52:33 الأية
أَمْ يَقُولُونَ تَقَوَّلَهُ ۚ بَل لَّا يُؤْمِنُونَ
Am yaqooloona taqawwalahu bal layu/minoon
Hausa
Shin, cẽwa suke yi: "Shi ne ke ƙăga faɗarsa"? Ă'a ba su dai yi ĩmăni ba.
|
Ayah 52:34 الأية
فَلْيَأْتُوا بِحَدِيثٍ مِّثْلِهِ إِن كَانُوا صَادِقِينَ
Falya/too bihadeethin mithlihi in kanoosadiqeena
Hausa
Sai su ző da wani lăbări mai misălinsa idan sun kasance sũmăsu gaskiya ne.
|
Ayah 52:35 الأية
أَمْ خُلِقُوا مِنْ غَيْرِ شَيْءٍ أَمْ هُمُ الْخَالِقُونَ
Am khuliqoo min ghayri shay-in am humu alkhaliqoon
Hausa
Shin, an halitta su ne bă daga kőme ba, kő kuwa sũ ne măsu yin halitta?
|
Ayah 52:36 الأية
أَمْ خَلَقُوا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ ۚ بَل لَّا يُوقِنُونَ
Am khalaqoo assamawatiwal-arda bal la yooqinoon
Hausa
Shin, sun halitta sammai da ƙasa ne? Ă'a ba su dai yi ĩmănin yaƙĩni ba.
|
Ayah 52:37 الأية
أَمْ عِندَهُمْ خَزَائِنُ رَبِّكَ أَمْ هُمُ الْمُصَيْطِرُونَ
Am AAindahum khaza-inu rabbika amhumu almusaytiroon
Hausa
Shin, taskőkin Ubangijinka, sună a wurinsu ne? Kő kuwa sũ ne măsu rinjăya?
|
Ayah 52:38 الأية
أَمْ لَهُمْ سُلَّمٌ يَسْتَمِعُونَ فِيهِ ۖ فَلْيَأْتِ مُسْتَمِعُهُم بِسُلْطَانٍ
مُّبِينٍ
Am lahum sullamun yastamiAAoona feehifalya/ti mustamiAAuhum bisultanin mubeen
Hausa
Shin, sună da wani tsăni ne wanda suke (hawa sună) saurăron (lăbărin samă) a
cikinsa? Sai mai saurarőnsu ya zo da wani dalĩli bayyananne.
|
Ayah 52:39 الأية
أَمْ لَهُ الْبَنَاتُ وَلَكُمُ الْبَنُونَ
Am lahu albanatu walakumu albanoon
Hausa
Shin, Yană da 'ya'ya mătă ne kuma kũ, kună da ɗiya maza ne?
|
Ayah 52:40 الأية
أَمْ تَسْأَلُهُمْ أَجْرًا فَهُم مِّن مَّغْرَمٍ مُّثْقَلُونَ
Am tas-aluhum ajran fahum min maghraminmuthqaloon
Hausa
Shin, kană tambayar su wata ijăra ne, sabőda haka suka zama măsu jin nauyin
biyan tărar?
|
Ayah 52:41 الأية
أَمْ عِندَهُمُ الْغَيْبُ فَهُمْ يَكْتُبُونَ
Am AAindahumu alghaybu fahum yaktuboon
Hausa
Shin, a wurinsu akwai ilmin gaibi, sabőda haka sună rubũtăwa?
|
Ayah 52:42 الأية
أَمْ يُرِيدُونَ كَيْدًا ۖ فَالَّذِينَ كَفَرُوا هُمُ الْمَكِيدُونَ
Am yureedoona kaydan fallatheenakafaroo humu almakeedoon
Hausa
Shin, sună nufin wani kaidi ne? To, waɗanda suka kăfirta sũ ne waɗanda ake yi wa
kaidi.
|
Ayah 52:43 الأية
أَمْ لَهُمْ إِلَٰهٌ غَيْرُ اللهِ ۚ سُبْحَانَ اللهِ عَمَّا يُشْرِكُونَ
Am lahum ilahun ghayru Allahisubhana Allahi AAamma yushrikoon
Hausa
Shin, sună da wani abin bautăwa ne wanda bă Allah ba? Tsarki ya tabbata ga Allah
daga abin da suke yi na shirki!
|
Ayah 52:44 الأية
وَإِن يَرَوْا كِسْفًا مِّنَ السَّمَاءِ سَاقِطًا يَقُولُوا سَحَابٌ مَّرْكُومٌ
Wa-in yaraw kisfan mina assama-isaqitan yaqooloo sahabun markoom
Hausa
Kuma idan sun ga wani ɓaɓɓake daga samă yănă făɗuwa, sai su ce wani girgije ne,
mai hauhawar jũna.
|
Ayah 52:45 الأية
فَذَرْهُمْ حَتَّىٰ يُلَاقُوا يَوْمَهُمُ الَّذِي فِيهِ يُصْعَقُونَ
Fatharhum hatta yulaqooyawmahumu allathee feehi yusAAaqoon
Hausa
To, ka bar su, sai sun haɗu da yinin nan da za a sũmar da su a cikinsa.
|
Ayah 52:46 الأية
يَوْمَ لَا يُغْنِي عَنْهُمْ كَيْدُهُمْ شَيْئًا وَلَا هُمْ يُنصَرُونَ
Yawma la yughnee AAanhum kayduhumshay-an wala hum yunsaroon
Hausa
Rănar da kaidinsu bă ya wadătar masu da kőme, kuma bă a taimakon su.
|
Ayah 52:47 الأية
وَإِنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا عَذَابًا دُونَ ذَٰلِكَ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا
يَعْلَمُونَ
Wa-inna lillatheena thalamooAAathaban doona thalika walakinna aktharahumla
yaAAlamoon
Hausa
Kuma lalle, waɗannan da suka yi zăluncin, sună da azăba (a nan dũniya) banda
waccan, kuma mafi yawansu ba su sani ba.
|
Ayah 52:48 الأية
وَاصْبِرْ لِحُكْمِ رَبِّكَ فَإِنَّكَ بِأَعْيُنِنَا ۖ وَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ
حِينَ تَقُومُ
Wasbir lihukmi rabbikafa-innaka bi-aAAyunina wasabbih bihamdirabbika heena
taqoom
Hausa
Sai ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, lalle kai fa kană idănunMu, kuma ka
tsarkake Ubangijinka da (tasbĩhi) game da gőde Masa a lőkacin da kake tăshi
tsaye (dőmin salla kő wani abu).
|
Ayah 52:49 الأية
وَمِنَ اللَّيْلِ فَسَبِّحْهُ وَإِدْبَارَ النُّجُومِ
Wamina allayli fasabbihhu wa-idbaraannujoom
Hausa
Kuma daga dare, sai ka tsarkake Shi (da tasbĩhin) dalőkacin jũyăwar taurări.
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|