1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
الْحَاقَّةُ
Alhaqqa
Hausa
Kiran gaskiya!
|
Ayah 69:2 الأية
مَا الْحَاقَّةُ
Ma alhaqqa
Hausa
Mẽne ne kiran gaskiya?
|
Ayah 69:3 الأية
وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْحَاقَّةُ
Wama adraka ma alhaqqa
Hausa
Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya?
|
Ayah 69:4 الأية
كَذَّبَتْ ثَمُودُ وَعَادٌ بِالْقَارِعَةِ
Kaththabat thamoodu waAAadun bilqariAAa
Hausa
Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya!
|
Ayah 69:5 الأية
فَأَمَّا ثَمُودُ فَأُهْلِكُوا بِالطَّاغِيَةِ
Faamma thamoodu faohlikoo bittaghiya
Hausa
To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani.
|
Ayah 69:6 الأية
وَأَمَّا عَادٌ فَأُهْلِكُوا بِرِيحٍ صَرْصَرٍ عَاتِيَةٍ
Waamma AAadun faohlikoo bireehinsarsarin AAatiya
Hausa
Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare
haddi.
|
Ayah 69:7 الأية
سَخَّرَهَا عَلَيْهِمْ سَبْعَ لَيَالٍ وَثَمَانِيَةَ أَيَّامٍ حُسُومًا فَتَرَى
الْقَوْمَ فِيهَا صَرْعَىٰ كَأَنَّهُمْ أَعْجَازُ نَخْلٍ خَاوِيَةٍ
Sakhkharaha AAalayhim sabAAa layalinwathamaniyata ayyamin husooman fataraalqawma
feeha sarAAa kaannahum aAAjazunakhlin khawiya
Hausa
(Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna,
sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne,
waɗanda suka fãɗi.
|
Ayah 69:8 الأية
فَهَلْ تَرَىٰ لَهُم مِّن بَاقِيَةٍ
Fahal tara lahum min baqiya
Hausa
To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu?
|
Ayah 69:9 الأية
وَجَاءَ فِرْعَوْنُ وَمَن قَبْلَهُ وَالْمُؤْتَفِكَاتُ بِالْخَاطِئَةِ
Wajaa firAAawnu waman qablahu walmu/tafikatubilkhati-a
Hausa
Kuma Fir'auna yã zo da waɗanda ke gabãninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu,
sabõda laifi.
|
Ayah 69:10 الأية
فَعَصَوْا رَسُولَ رَبِّهِمْ فَأَخَذَهُمْ أَخْذَةً رَّابِيَةً
FaAAasaw rasoola rabbihim faakhathahumakhthatan rabiya
Hausa
Dõmin sun sãɓã wa manzon Ubangijinsu, sabõda haka ya kãmã su da wani irin kãmu
mai ƙãruwar (tsanani).
|
Ayah 69:11 الأية
إِنَّا لَمَّا طَغَى الْمَاءُ حَمَلْنَاكُمْ فِي الْجَارِيَةِ
Inna lamma taghaalmao hamalnakum fee aljariya
Hausa
Lalle ne, Mũ, a lõkacin da ruwa ya ƙẽtare haddi, Munɗauke aaku a cikin jirgin
ruwan nan.
|
Ayah 69:12 الأية
لِنَجْعَلَهَا لَكُمْ تَذْكِرَةً وَتَعِيَهَا أُذُنٌ وَاعِيَةٌ
LinajAAalaha lakum tathkiratanwataAAiyaha othunun waAAiya
Hausa
Dõmin Mu sanya shi, gare ku abin tunãwa kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye
(shi).
|
Ayah 69:13 الأية
فَإِذَا نُفِخَ فِي الصُّورِ نَفْخَةٌ وَاحِدَةٌ
Fa-itha nufikha fee assoorinafkhatun wahida
Hausa
To, idan an yi bũsa a cikin ƙaho, bũsa ɗaya.
|
Ayah 69:14 الأية
وَحُمِلَتِ الْأَرْضُ وَالْجِبَالُ فَدُكَّتَا دَكَّةً وَاحِدَةً
Wahumilati al-ardu waljibalufadukkata dakkatan wahida
Hausa
Kuma aka ɗauki ƙasa da duwãtsu, kuma aka niƙa su niƙãwa ɗaya.
|
Ayah 69:15 الأية
فَيَوْمَئِذٍ وَقَعَتِ الْوَاقِعَةُ
Fayawma-ithin waqaAAati alwaqiAAa
Hausa
A ran nan, mai aukuwa zã ta auku.
|
Ayah 69:16 الأية
وَانشَقَّتِ السَّمَاءُ فَهِيَ يَوْمَئِذٍ وَاهِيَةٌ
Wanshaqqati assamaofahiya yawma-ithin wahiya
Hausa
Kuma sama zã ta tsãge, dõmin ita a ran nan, mai rauni ce.
|
Ayah 69:17 الأية
وَالْمَلَكُ عَلَىٰ أَرْجَائِهَا ۚ وَيَحْمِلُ عَرْشَ رَبِّكَ فَوْقَهُمْ
يَوْمَئِذٍ ثَمَانِيَةٌ
Walmalaku AAala arja-ihawayahmilu AAarsha rabbika fawqahum yawma-ithin thamaniya
Hausa
Kuma malã'iku (su bayyana) a kan sãsanninta, kuma wasu (malã'iku) takwas na
ɗauke da Al'arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan rãnar.
|
Ayah 69:18 الأية
يَوْمَئِذٍ تُعْرَضُونَ لَا تَخْفَىٰ مِنكُمْ خَافِيَةٌ
Yawma-ithin tuAAradoona latakhfa minkum khafiya
Hausa
A rãnar nan zã a bijirã ku (dõmin hisãbi), bãbu wani rai, mai ɓoyewa, daga
cikinku, wanda zai iya ɓõyẽwa.
|
Ayah 69:19 الأية
فَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَهُ بِيَمِينِهِ فَيَقُولُ هَاؤُمُ اقْرَءُوا
كِتَابِيَهْ
Faamma man ootiya kitabahubiyameenihi fayaqoolu haomu iqraoo kitabiyah
Hausa
To, amma wanda aka bai wa littãfinsa a dãmansa, sai ya ce wa (makusantansa), "Ku
karɓa, ku karanta littafina."
|
Ayah 69:20 الأية
إِنِّي ظَنَنتُ أَنِّي مُلَاقٍ حِسَابِيَهْ
Innee thanantu annee mulaqinhisabiyah
Hausa
"Lalle ne ni, nã tabbata cewa ni mai haɗuwa da hisãbina ne."
|
Ayah 69:21 الأية
فَهُوَ فِي عِيشَةٍ رَّاضِيَةٍ
Fahuwa fee AAeeshatin radiya
Hausa
Sabõda haka, shi yana cikin wata rãyuwa yardadda.
|
Ayah 69:22 الأية
فِي جَنَّةٍ عَالِيَةٍ
Fee jannatin AAaliya
Hausa
A cikin Aljanna maɗaukakiya.
|
Ayah 69:23 الأية
قُطُوفُهَا دَانِيَةٌ
Qutoofuha daniya
Hausa
Nunannun 'yã'yan itãcenta makusantã ne (ga mai son ɗĩba),
|
Ayah 69:24 الأية
كُلُوا وَاشْرَبُوا هَنِيئًا بِمَا أَسْلَفْتُمْ فِي الْأَيَّامِ الْخَالِيَةِ
Kuloo washraboo hanee-an bimaaslaftum fee al-ayyami alkhaliya
Hausa
(Ana ce musu) "Ku ci, kuma ku sha a cikin ni'ima, sabõda abin da kuka gabãtar a
cikin kwãnukan da suka shige."
|
Ayah 69:25 الأية
وَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَهُ بِشِمَالِهِ فَيَقُولُ يَا لَيْتَنِي لَمْ أُوتَ
كِتَابِيَهْ
Waamma man ootiya kitabahubishimalihi fayaqoolu ya laytanee lam oota kitabiyah
Hausa
Kuma wanda aka bai wa littãfinsa ga hagunsa, sai ya ce: "Kaitona, ba a kãwo mini
littãfina ba!"
|
Ayah 69:26 الأية
وَلَمْ أَدْرِ مَا حِسَابِيَهْ
Walam adri ma hisabiyah
Hausa
"Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisãbina ba!"
|
Ayah 69:27 الأية
يَا لَيْتَهَا كَانَتِ الْقَاضِيَةَ
Ya laytaha kanati alqadiya
Hausa
"In dã dai ita, tã kasance mai halakã ni gabã ɗaya ce!
|
Ayah 69:28 الأية
مَا أَغْنَىٰ عَنِّي مَالِيَهْ ۜ
Ma aghna AAannee maliyah
Hausa
"Dukiyãta ba ta wadatar da ni ba!"
|
Ayah 69:29 الأية
هَلَكَ عَنِّي سُلْطَانِيَهْ
Halaka AAannee sultaniyah
Hausa
"Ĩkona ya ɓace mini!"
|
Ayah 69:30 الأية
خُذُوهُ فَغُلُّوهُ
Khuthoohu faghullooh
Hausa
(Sai a ce wa malã'iku) "Ku kãmã shi, sa'an nan ku sanyã shi a cikin ƙuƙumi."
|
Ayah 69:31 الأية
ثُمَّ الْجَحِيمَ صَلُّوهُ
Thumma aljaheema sallooh
Hausa
"Sa'an nan, a cikin Jahĩm, ku ƙõna shi."
|
Ayah 69:32 الأية
ثُمَّ فِي سِلْسِلَةٍ ذَرْعُهَا سَبْعُونَ ذِرَاعًا فَاسْلُكُوهُ
Thumma fee silsilatin tharAAuhasabAAoona thiraAAan faslukooh
Hausa
"Sa'an nan, acikin sarƙa, tsawonta zirã'i saba'in, sai ku sanya shi."
|
Ayah 69:33 الأية
إِنَّهُ كَانَ لَا يُؤْمِنُ بِاللهِ الْعَظِيمِ
Innahu kana la yu/minu billahialAAatheem
Hausa
"Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin ĩmãni da Allah, Mai girma!"
|
Ayah 69:34 الأية
وَلَا يَحُضُّ عَلَىٰ طَعَامِ الْمِسْكِينِ
Wala yahuddu AAalataAAami almiskeen
Hausa
"Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci!"
|
Ayah 69:35 الأية
فَلَيْسَ لَهُ الْيَوْمَ هَاهُنَا حَمِيمٌ
Falaysa lahu alyawma hahuna hameem
Hausa
"Sabõda haka, a yau, a nan, bã ya da masõyi."
|
Ayah 69:36 الأية
وَلَا طَعَامٌ إِلَّا مِنْ غِسْلِينٍ
Wala taAAamun illamin ghisleen
Hausa
"Kuma bãbu wani abinci, sai daga (itãcen) gislĩn."
|
Ayah 69:37 الأية
لَّا يَأْكُلُهُ إِلَّا الْخَاطِئُونَ
La ya/kuluhu illa alkhati-oon
Hausa
"Bãbu mai cin sa sai mãsu ganganci."
|
Ayah 69:38 الأية
فَلَا أُقْسِمُ بِمَا تُبْصِرُونَ
Fala oqsimu bima tubsiroon
Hausa
To, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba,
|
Ayah 69:39 الأية
وَمَا لَا تُبْصِرُونَ
Wama la tubsiroon
Hausa
Da abin da bã ku iya gani.
|
Ayah 69:40 الأية
إِنَّهُ لَقَوْلُ رَسُولٍ كَرِيمٍ
Innahu laqawlu rasoolin kareem
Hausa
Lalle ne, shi (Alƙur'ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne.
|
Ayah 69:41 الأية
وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَاعِرٍ ۚ قَلِيلًا مَّا تُؤْمِنُونَ
Wama huwa biqawli shaAAirinqaleelan ma tu/minoon
Hausa
Kuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata.
|
Ayah 69:42 الأية
وَلَا بِقَوْلِ كَاهِنٍ ۚ قَلِيلًا مَّا تَذَكَّرُونَ
Wala biqawli kahinin qaleelanma tathakkaroon
Hausa
Kuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa.
|
Ayah 69:43 الأية
تَنزِيلٌ مِّن رَّبِّ الْعَالَمِينَ
Tanzeelun min rabbi alAAalameen
Hausa
Abin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka.
|
Ayah 69:44 الأية
وَلَوْ تَقَوَّلَ عَلَيْنَا بَعْضَ الْأَقَاوِيلِ
Walaw taqawwala AAalayna baAAdaal-aqaweel
Hausa
Kuma dã (Muhammadu) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu.
|
Ayah 69:45 الأية
لَأَخَذْنَا مِنْهُ بِالْيَمِينِ
Laakhathna minhu bilyameen
Hausa
Dã Mun kãma shi da dãma.
|
Ayah 69:46 الأية
ثُمَّ لَقَطَعْنَا مِنْهُ الْوَتِينَ
Thumma laqataAAna minhualwateen
Hausa
sa'an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã.
|
Ayah 69:47 الأية
فَمَا مِنكُم مِّنْ أَحَدٍ عَنْهُ حَاجِزِينَ
Fama minkum min ahadin AAanhu hajizeen
Hausa
Kuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre (azãbarMu) daga gare shi.
|
Ayah 69:48 الأية
وَإِنَّهُ لَتَذْكِرَةٌ لِّلْمُتَّقِينَ
Wa-innahu latathkiratun lilmuttaqeen
Hausa
Kuma lalle ne shi (Alƙur'ãni) tanãtarwa ce ga mãsu taƙawa.
|
Ayah 69:49 الأية
وَإِنَّا لَنَعْلَمُ أَنَّ مِنكُم مُّكَذِّبِينَ
Wa-inna lanaAAlamu anna minkum mukaththibeen
Hausa
Kuma lalle, ne Mũ, wallahi Munã sane da cẽwa daga cikinku alwwai mãsu ƙaryatãwa.
|
Ayah 69:50 الأية
وَإِنَّهُ لَحَسْرَةٌ عَلَى الْكَافِرِينَ
Wa-innahu lahasratun AAala alkafireen
Hausa
Kuma lalle ne shi (Alƙarãni) wallahi baƙin ciki ne ga kãfirai.
|
Ayah 69:51 الأية
وَإِنَّهُ لَحَقُّ الْيَقِينِ
Wa-innahu lahaqqu alyaqeen
Hausa
Kuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙshẽni.
|
Ayah 69:52 الأية
فَسَبِّحْ بِاسْمِ رَبِّكَ الْعَظِيمِ
Fasabbih bismi rabbika alAAatheem
Hausa
Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangjinka, mai girma.
|
|