1st Ayah 1 الأية ١الأوليبِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
يَا أَيُّهَا الْمُزَّمِّلُ
Ya ayyuha almuzzammil
Hausa
Yã wanda ya lulluɓe!
|
Ayah 73:2 الأية
قُمِ اللَّيْلَ إِلَّا قَلِيلًا
Qumi allayla illa qaleela
Hausa
Ka tsayu domin yin salla a cikin dare (duka) fãce kaɗan.
|
Ayah 73:3 الأية
نِّصْفَهُ أَوِ انقُصْ مِنْهُ قَلِيلًا
Nisfahu awi onqus minhu qaleela
Hausa
Rabinsa, ko ka rage abu kaɗan daga gare shi.
|
Ayah 73:4 الأية
أَوْ زِدْ عَلَيْهِ وَرَتِّلِ الْقُرْآنَ تَرْتِيلًا
Aw zid AAalayhi warattili alqur-anatarteela
Hausa
Ko ka ƙara kansa kuma ka kyautata karanta Alƙu'ãni, daki daki.
|
Ayah 73:5 الأية
إِنَّا سَنُلْقِي عَلَيْكَ قَوْلًا ثَقِيلًا
Inna sanulqee AAalayka qawlan thaqeela
Hausa
Lalle ne, Mũ, zã Mu jẽfa maka magana mai nauyi.
|
Ayah 73:6 الأية
إِنَّ نَاشِئَةَ اللَّيْلِ هِيَ أَشَدُّ وَطْئًا وَأَقْوَمُ قِيلًا
Inna nashi-ata allayli hiya ashaddu wat-anwaaqwamu qeela
Hausa
Lalle ne, tashin dare shi ne mafi tsananin natsuwa, kuma mafi daidaituwa ga
magana.
|
Ayah 73:7 الأية
إِنَّ لَكَ فِي النَّهَارِ سَبْحًا طَوِيلًا
Inna laka fee annahari sabhantaweela
Hausa
Lalle ne, kanã da, a cikin yini, wani tasĩhi mai tsawo.
|
Ayah 73:8 الأية
وَاذْكُرِ اسْمَ رَبِّكَ وَتَبَتَّلْ إِلَيْهِ تَبْتِيلًا
Wathkuri isma rabbikawatabattal ilayhi tabteela
Hausa
Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, kuma ka yanke (ƙauna daga kowa ka koma) zuwa
gare Shi, yankewa.
|
Ayah 73:9 الأية
رَّبُّ الْمَشْرِقِ وَالْمَغْرِبِ لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ فَاتَّخِذْهُ وَكِيلًا
Rabbu almashriqi walmaghribi lailaha illa huwa fattakhithhu wakeela
Hausa
Shi ne Ubangijin mafitar rãnã da mafãɗarta, bãbu abin bautawa fãce Shi. Sabõda
haka ka riƙe Shi wakili.
|
Ayah 73:10 الأية
وَاصْبِرْ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَاهْجُرْهُمْ هَجْرًا جَمِيلًا
Wasbir AAala mayaqooloona wahjurhum hajran jameela
Hausa
Kuma ka yi haƙuri ga abin da suke faɗã, kuma ka ƙaurace musu, ƙauracẽwa mai
kyãwo.
|
Ayah 73:11 الأية
وَذَرْنِي وَالْمُكَذِّبِينَ أُولِي النَّعْمَةِ وَمَهِّلْهُمْ قَلِيلًا
Watharnee walmukaththibeenaolee annaAAmati wamahhilhum qaleela
Hausa
Kuma ka bar Ni da mãsu ƙaryatãwa, mawadãta, kuma ka jinkirta musu kaɗan.
|
Ayah 73:12 الأية
إِنَّ لَدَيْنَا أَنكَالًا وَجَحِيمًا
Inna ladayna ankalan wajaheema
Hausa
Lalle ne, a wurinMu, akwai wasu marũruwa mãsu nauyi da Jahĩm.
|
Ayah 73:13 الأية
وَطَعَامًا ذَا غُصَّةٍ وَعَذَابًا أَلِيمًا
WataAAaman tha ghussatinwaAAathaban aleema
Hausa
Da wani abinci mai mãƙara da azãba mai raɗaɗi.
|
Ayah 73:14 الأية
يَوْمَ تَرْجُفُ الْأَرْضُ وَالْجِبَالُ وَكَانَتِ الْجِبَالُ كَثِيبًا مَّهِيلًا
Yawma tarjufu al-ardu waljibaluwakanati aljibalu katheeban maheela
Hausa
Rãnar da ƙasa ke raurawa, da duwãtsu kuma duwãtsu su kasance tudun rairayi mai
malãlã.
|
Ayah 73:15 الأية
إِنَّا أَرْسَلْنَا إِلَيْكُمْ رَسُولًا شَاهِدًا عَلَيْكُمْ كَمَا أَرْسَلْنَا
إِلَىٰ فِرْعَوْنَ رَسُولًا
Inna arsalna ilaykum rasoolanshahidan AAalaykum kama arsalna ilafirAAawna
rasoola
Hausa
Lalle ne, Mũ. Mun aika zuwa gare ku, wani Manzo mai shaida a kanku, kamar yadda
Muka aika wani Manzo zuwaga Fir'auna,
|
Ayah 73:16 الأية
فَعَصَىٰ فِرْعَوْنُ الرَّسُولَ فَأَخَذْنَاهُ أَخْذًا وَبِيلًا
FaAAasa firAAawnu arrasoolafaakhathnahu akhthan wabeela
Hausa
Sai Fir'auna ya saɓa wa Manzon, saboda haka Muka kãma shi kãmu mai tsanani.
|
Ayah 73:17 الأية
فَكَيْفَ تَتَّقُونَ إِن كَفَرْتُمْ يَوْمًا يَجْعَلُ الْوِلْدَانَ شِيبًا
Fakayfa tattaqoona in kafartum yawmanyajAAalu alwildana sheeba
Hausa
To, yãya, idan kun kãfirta, zã ku kãre (azabar) wani yini mai mayar da yãra
(tsofaffi) mãsu hurhura.
|
Ayah 73:18 الأية
السَّمَاءُ مُنفَطِرٌ بِهِ ۚ كَانَ وَعْدُهُ مَفْعُولًا
Assamao munfatirunbihi kana waAAduhu mafAAoola
Hausa
Sama za ta tsãge a cikinsa, wa'adinsa yã kasance mai aukuwa.
|
Ayah 73:19 الأية
إِنَّ هَٰذِهِ تَذْكِرَةٌ ۖ فَمَن شَاءَ اتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِ سَبِيلًا
Inna hathihi tathkiratun famanshaa ittakhatha ila rabbihi sabeela
Hausa
Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, sai dai wanda ya so, ya kãma hanyar ƙwarai
zuwa ga Ubangijinsa.
|
Ayah 73:20 الأية
إِنَّ رَبَّكَ يَعْلَمُ أَنَّكَ تَقُومُ أَدْنَىٰ مِن ثُلُثَيِ اللَّيْلِ
وَنِصْفَهُ وَثُلُثَهُ وَطَائِفَةٌ مِّنَ الَّذِينَ مَعَكَ ۚ وَاللهُ يُقَدِّرُ
اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ ۚ عَلِمَ أَن لَّن تُحْصُوهُ فَتَابَ عَلَيْكُمْ ۖ
فَاقْرَءُوا مَا تَيَسَّرَ مِنَ الْقُرْآنِ ۚ عَلِمَ أَن سَيَكُونُ مِنكُم
مَّرْضَىٰ ۙ وَآخَرُونَ يَضْرِبُونَ فِي الْأَرْضِ يَبْتَغُونَ مِن فَضْلِ اللهِ
ۙ وَآخَرُونَ يُقَاتِلُونَ فِي سَبِيلِ اللهِ ۖ فَاقْرَءُوا مَا تَيَسَّرَ مِنْهُ
ۚ وَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ وَآتُوا الزَّكَاةَ وَأَقْرِضُوا اللهَ قَرْضًا حَسَنًا
ۚ وَمَا تُقَدِّمُوا لِأَنفُسِكُم مِّنْ خَيْرٍ تَجِدُوهُ عِندَ اللهِ هُوَ
خَيْرًا وَأَعْظَمَ أَجْرًا ۚ وَاسْتَغْفِرُوا اللهَ ۖ إِنَّ اللهَ غَفُورٌ
رَّحِيمٌ
Inna rabbaka yaAAlamu annaka taqoomu adnamin thuluthayi allayli wanisfahu
wathuluthahu wata-ifatunmina allatheena maAAaka wallahu yuqaddiruallayla
wannahara AAalima an lan tuhsoohufataba AAalaykum faqraoo ma tayassara
minaalqur-ani AAalima an sayakoonu minkum marda waakharoonayadriboona fee
al-ardi yabtaghoona min fadliAllahi waakharoona yuqatiloona fee sabeeliAllahi
faqraoo ma tayassara minhu waaqeemooassalata waatoo azzakatawaaqridoo Allaha
qardan hasanan wamatuqaddimoo li-anfusikum min khayrin tajidoohu AAinda
Allahihuwa khayran waaAAthama ajran wastaghfirooAllaha inna Allaha ghafoorun
raheem
Hausa
Lalle ne, Ubangijinka Yã sani cẽwa, kai kana tsayuwa a kusan kashi biyu daga uku
na dare, da rabinsa, da sulusinsa, tãre da wani ɓangare na waɗanda ke tãre da
kai. Allah Yake iya ƙaddara dare da yini, Ya san bã zã ku iya lissafa shi ba,
sabõda haka Ya karɓi tubarku sai, ku karanta abin da ya sauƙaƙa na Alƙur'ãni. Ya
san wasu daga cikinku, zã su yi cĩwo, kuma wasu zã su yi tafiya cikin ƙasa suna
nẽman falalar Allah da fatauci, kuma wasu zã su yi yãƙi a cikin banyar Allah.
Sabõda haka ku karanta abin da ya sauƙaƙa daga gare shi, kuma ku tsai da salla
kuma ku bãyar da zakka, kumaa ku bai wa Allah rance, rance mai kyãwo. Kuma abin
da kuka gabatar dõmin kanku, na alhẽri, zã ku sãme shi a wurin Allah zai kasance
mafifici (daga wanda kuka ajiye) kuma zai fi girma ga sakamako, kuma ku rõƙi
Allah gãfara; lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|