Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku ɗaukaka saututtukanku bisa sautin Annabi,
kuma kada ku bayyana sauti gare shi a magana, kamar bayyanãwar sãshenku ga
sãshe, dõmin kada ayyukanku su ɓãci, alhãli kuwa kũ ba ku sani ba.
Lalle waɗanda ke runtsẽwar saututtukansu a wurin Manzon Allah waɗannan ne
waɗanda Allah Yã, jarrabi zukãtansu ga taƙawa. Sunã da wata irin gãfara da ijãra
mai girma.
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan fãsiƙi Yã zo muku da wani babban lãbãri, to,
ku nẽmi bayãni, dõmin kada ku cũci waɗansu mutãne a cikin jãhilci, sabõda haka
ku wãyi gari a kan abin da kuka aikata kunã mãsu nadãma.
Kuma ku sani (cẽwa) lalle ne, a cikinku akwai Manzon Allah. Dã Yana bin ku ga
(hãlãye) mãsu Yawa na al'amarin, dã kun auku a cikin zunubi, kuma amma Allah Yã
sõyar da ĩmãni a gare ku, kuma Yã ƙawãta shi a cikin zukãtanku kuma Yã ƙyãmantar
da kãfirci da fãsicci da sãɓo zuwa gare ku. Waɗannan (da suka lazimci sifõfin
nan) su ne shiryayyu.
Kuma idan jama'a biyu ta mũminai suka yi yãki, to, kuyi sulhu, a tsakãninsu. Sai
idan ɗayansu ta yi zãlunci a kan gudar, to, sai ku yãƙi wadda ke yin zãlunci har
ta kõma, zuwa ga umurnin Allah. To, idan ta kõma, sai ku yi sulhu a tsakãninsu
da ãdalci kuma ku daidaita. Lalle Allah na son mãsu daidaitãwa.
"Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada waɗansu mutãne su yi izgili game da waɗansu
mutãne, mai yiwuwa ne (abin yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su
(mãsu izgilin), kuma waɗansu mãtã kada su yi izgili game da waɗansu mãtã mai
yiwuwa ne su kasancc mafĩfĩta daga gare su. Kuma kada ku aibanta kanku, kuma
kada ku jẽfi jũna da miyãgun sunãye na laƙabõbĩ.Tir da sũna na fãsicci a bãyãn
ĩmãni. Kuma wanda bai tũba ba, to, waɗannan sũ ne azzãlumai."
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku nĩsanci abu mai yãwa na zato. Lalle sãshen zato
laifi ne. Kuma kada ku yi rahõto, kuma kada sãshenku yã yi gulmar sãshe. Shin,
ɗayanku nã son yã ci naman ɗan'uwansa yanã matacce? To, kun ƙĩ shi (cin nãman).
Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai karɓar tũba ne, Mai jin ƙai.
Yã kũ mutãne! Lalle ne Mũ, Mun halitta ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya
ku dangõgi da kabĩlõli, dõmin ku san jũna. Lalle mafĩfĩcinku daraja a wurin
Allah, (shĩ ne) wanda yake mafĩfĩcinku a taƙawa. Lalle nẽ Allah Masani ne, Mai
ƙididdigẽwa.
¡auyãwa suka ce: "Mun yi ĩmãni." Ka ce: "Ba ku yi ĩmãni ba, amma dai ku ce, 'Mun
mĩƙawuya, ĩmani bai gama shiga a cikinzukãtanku ba. Kuma idan kun yi ɗã'a ga
Allah da ManzonSa, to, bã zai rage muku kõme daga ayyukanku ba. Lalle Allah Mai
gãfara ne, Mai jin ƙai."
Mũminan gaskiya kawai, sũ ne waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, sa'an
nan ba su yi shakka ba, kuma suka yi jihãdi da dũkiyarsu da kuma rãyukansu,
cikin tafarkin Allah. Waɗannan sũ ne mãsu gaskiya.
Ka ce: "Kuna sanar da Allah ne game da addininku, alhãli kuwa Allah Yã san abin
da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa, kuma Allah Masani ne ga dukan
kõme?"
Suna yin gõri a kanka wai sun musulunta. Ka ce: "Kada ku yi gõrin kun musulunta
a kaina. Ã'a, Allah ne ke yi muku gõri dõmin Ya shiryar da ku ga ĩmãni, idan kun
kasance mãsu gaskiya."