Dõmin Allah Ya shãfe abin da ya gabãta na laifinka da abin da ya jinkirta, kuma
Ya cika ni'imarSa a kanka, kuma Ya shiryar da kai ga hanya madaidaiciya.
Shĩ ne wanda Ya saukar da natsuwa a cikin zukãtan mũminai dõmin su ƙãra wani
ĩmãni tãre da imãninsu, alhãli kuwa rundunõnin sammai da ƙasa, na Allah kawai
ne, kuma Allah Ya kasance Masani, Mai hikima.
Dõmin Ya shigar da mũminai maza da mũminai mãtã gidãjen Aljanna, kõgunan ruwa na
gudãna daga ƙarƙashin gidãjen, sunã madawwama a cikinsu kuma Ya kankare musu
mũnãnan ayyukansu. wannan abu ya kasance a wurin Allah babban rabo, mai gimia.
Kuma Ya yi azãba ga munãfikai maza da munãfikai mãtã da mushirikai maza da
musbirikai mãtã, mãsu zaton mugun zato game da Allah, mugunyar masĩfa mai
kẽwayẽwa ta tabbata a kansu, kuma Allah Ya yi hushi da su, kuma Ya la'ane su,
kuma Ya yi musu tattlain Jahannama kuma ta mũnana ta zama makõma (gare su).
Lalle waɗanda ke yi maka mubãya'a, Allah kawai ne suke yi wa mubãya'a, Hannun
Allah nã bisa hannayensu, sabõda haka wanda ya warware, to, yanã warwarẽwa ne a
kan kansa kawai, kuma wanda ya cika ga alkawarin da ya yi wa Allah a kansa, to,
(Allah) zai kãwo masa ijãra mai girma.
Waɗanda aka bari daga ƙauyãwa zã su ce maka, "Dũkiyõyinmu da iyãlanmu sun
shagaltar da mu, sai ka nẽma mana gãfara." Sunã faɗã, da harsunansu, abin da bã
shĩ ne a cikin zukãtansu ba. Kace: "To, wãne ne ke mallakar wani abu daga Allah
sabõda kũ, idan Yã yi nufin wata cũta agare ku kõ kuma (idan) Ya yi nufin wani
amfãni a gare ku? Ã'a, Allah Ya kasance Mai labartawa ne ga abin da kuke
aikatãwa."
Ã'a kun yi zaton Annabi da mũminai, bã za su kõmo zuwa ga iyãlansu ba, har
abada. Kuma an ƙawãta wannan (tunãni) a cikin zukãtanku, kuma kun yi zato, zaton
mugunta, kuma kun kasance mutãne halakakku.
Mulkin sammai da ƙasã na Allah kawai ne, Yanã gãfartawa ga wanda Yake so, kuma
Yanã azabta wanda Yake so alhãli kuwa Allah Ya kasance Mai gãfara ne, Mai jin
ƙai.
Waɗanda aka bari zã su ce idan kun tafi zuwa ga waɗansu ganĩmõmi dõmin ku karɓo
su, "Ku bar mu, mu bĩ ku." Sunã son su musanya maganar Allah ne. Ka ce: "Bã zã
ku bĩ mu ba. Kamar wannan ne Allah Ya ce, a gabãnin haka." Sa'an nan zã su ce:
"Ã'a, kunã dai hãssadar mu ne." Ã'a, sun kasance bã su fahimtar (abũbuwa) sai
kaɗan.
Ka ce wa waɗanda aka bari daga ƙauyãwa: "Za a kira ku zuwa ga waɗansu mutãne
mãsu tsananin yãƙi (dõmin) ku yãƙe su kõ kuwa su musulunta. To, idan kun yi
ɗã'a, Allah zai kãwo muku wata ijãra mai kyau, kuma idan kuka jũya bãya kamar
yadda kuka jũya a gabãnin wancan, zai azãbtã ku, azãba mai raɗadi."
Bãbu laifi a kan makãho, kuma bãbu laifi a kan gurgu, kuma bãbu laifi a kan
majiyyaci. Kuma wanda ya yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, (Allah) zai shigar da shi
a gidãjen Aljanna, kõguna na gudãna daga ƙarƙashinsu. Kuma wanda ya jũya bãya, (
Allah) zai azabtãshi, azãba mai raɗãɗi.
Lalle ne haƙĩƙa, Allah Ya yarda da muminai a lõkacin da suke yi maka mubãya, a a
ƙarƙashin itãciyar nan dõmin Yã san abin da ke cikin zukãtansu sai Yã saukar da
natsuwa a kansu, kuma Ya sãka musu da wani cin nasara makusanci.
Kuma Allah Yã yi muku wa'adin waɗansu ganĩmõmi mãsu yawa, waɗanda zã ku karɓo
su, kuma Ya gaggauta muku wannan. Kuma Ya kange hannãyen mutãne daga gare ku,
kuma dõmin ta kasance wata ãyã ce ga mũminai, kuma Yã shiryar da ku ga hanya
madaidaiciya.
Kuma Shĩ ne Ya kange hannayensu daga gare ku, kuma da hannayenku daga gare su, a
cikin Makka, bãyan Ya rinjãyar da ku a kansu. Kuma Allah Ya kasance Mai gani ga
abin da kuke aikatãwa.
Sũ ne waɗanda suka kãfirta kuma suka kange ku daga Masallacin Harami, da hadaya
tanã tsare (sun hana ta) ta isa ga wurinta. Kuma bã dõmin waɗansu maza mũminai
da waɗansu mãtã mũminai ba ba ku sansu ba ku tãkã su har wani aibi ya sãme ku
daga gare su, bã da sani ba, (dã Allah Yã yi muku iznin yãƙi), dõmin Allah Ya
shigar da wanda Yake so a cikin rahamarSa. Da (mũminai) sun tsabbace dã Mun
azabtar da waɗanda suka kãfirta daga gare su da azãba mai raɗiɗi.
A lõkacin da waɗanda suka kãfirta suka sanya hanãnar ƙabĩ lanci a cikin
zukãtansu hanãnar ƙabĩlanci irin na Jãhiliyya sai Allah Ya saukar da natsuwarSa
a kan ManzonSa, kuma da a kan mũminai kuma Ya lazimta musu kalmar taƙawa alhãli
kuwa sun kasance mafi dãcẽwa da ita kuma ma'abutanta. Kuma Allah ya kasance
Masani game da dukan kõme.
Lalle ne haƙĩƙa Allah Ya gaskata wa ManzonSa mafarkinsa da gaskiya: Lalle zã ku
shiga Masallacin Harami, in Allah Ya so, kunã mãsu natsuwa, mãsu aske kawunanku
da mãsu suisuye, bã ku jin tsõro, dõmin (Allah) Ya san abin da ba ku sani ba,
sa'an nan Ya sanya wani cin nasara makusanci a bãyan wannan.
Muhammadu Manron Allah ne. Kuma waɗannan da ke tãre da shi mãsu tsanani ne a kan
kãfirai, mãsu rahama ne a tsakãninsu, kanã ganin su sunã mãsu rukũ'i mãsu
sujada, sunã nẽman falala daga Ubangijinsu, da yardarSa. Alãmarsu tanã a cikin
fuskõkinsu, daga kufan sujuda. Wannan shĩ ne siffarsu a cikin Attaura. Kuma
siffarsu,a cikin Injĩla ita ce kamar tsiron shũka wanda ya fitar da rẽshensa,
sa'an nan ya ƙarfafa shi, ya yi kauri, sa'an nan ya daidaita a kan ƙafãfunsa,
yanã bãyar da sha'awa ga mãsu shũkar' dõmin (Allah) Ya fusãtar da kãfirai game
da su. Kuma Allah Ya yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata
ayyukan ƙwarai, daga cikinsu, da gãfara da ijãra mai girma.