Prev  

62. Surah Al-Jumu'ah سورة الجمعة

  Next  




Ayah  62:1  الأية
    +/- -/+  
بِسْم ِ اللهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
يُسَبِّحُ لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ الْمَلِكِ الْقُدُّوسِ الْعَزِيزِ الْحَكِيمِ
Hausa
 
Abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin kasã sunã tasbĩhi ga Allah, Mamallaki,Mai tsarki' Mabuwãyi, Mai hikima.

Ayah  62:2  الأية
    +/- -/+  
هُوَ الَّذِي بَعَثَ فِي الْأُمِّيِّينَ رَسُولًا مِّنْهُمْ يَتْلُو عَلَيْهِمْ آيَاتِهِ وَيُزَكِّيهِمْ وَيُعَلِّمُهُمُ الْكِتَابَ وَالْحِكْمَةَ وَإِن كَانُوا مِن قَبْلُ لَفِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ
Hausa
 
Shĩ ne wanda Ya aika, a cikin mabiya al'ãdu, wani Manzo daga gare su yanã karanta ãyõyinSa a kansu, kuma yanã tsarkake su, kuma yanã sanar da su littafin da hikimarsa kõ da yake sun kasance daga gabãninsa lalle sunã a cikin ɓata bayyanãnna.

Ayah  62:3  الأية
    +/- -/+  
وَآخَرِينَ مِنْهُمْ لَمَّا يَلْحَقُوا بِهِمْ ۚ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Hausa
 
Da waɗansu mutãne daga gare su, ba su i da riskuwa da sũ ba, alhãli kuwa shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.

Ayah  62:4  الأية
    +/- -/+  
ذَٰلِكَ فَضْلُ اللهِ يُؤْتِيهِ مَن يَشَاءُ ۚ وَاللهُ ذُو الْفَضْلِ الْعَظِيمِ
Hausa
 
Waccan wata falalar Allah ce Yanã bãyar da ita ga wanda Yake so. Kuma Allah ne Ma'abũcin dukan falala mai girma.

Ayah  62:5  الأية
    +/- -/+  
مَثَلُ الَّذِينَ حُمِّلُوا التَّوْرَاةَ ثُمَّ لَمْ يَحْمِلُوهَا كَمَثَلِ الْحِمَارِ يَحْمِلُ أَسْفَارًا ۚ بِئْسَ مَثَلُ الْقَوْمِ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِ اللهِ ۚ وَاللهُ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ
Hausa
 
Misãlin waɗanda aka ɗõra wa ɗaukar Attaura sa'an nan ba su ɗauke ta ba, kamar misãlin jãki ne Yanã ɗaukar littattafai. Tir da misãlin mutãnen nan da suka ƙaryatã game da ãyõyin Allah! Kuma Allah bã Yã shiryar da mutãnẽ azzãlumai.

Ayah  62:6  الأية
    +/- -/+  
قُلْ يَا أَيُّهَا الَّذِينَ هَادُوا إِن زَعَمْتُمْ أَنَّكُمْ أَوْلِيَاءُ لِلَّهِ مِن دُونِ النَّاسِ فَتَمَنَّوُا الْمَوْتَ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ
Hausa
 
Ka ce: "Yã kũ waɗandasuka tũba (Yahũdu)! Idan kun riya cẽwa kũ ne zãɓaɓɓun Allah bã sauran mutanẽ ba, sai ku yi gũrin mutuwa idan kun kasance mãsu gaskiya."

Ayah  62:7  الأية
    +/- -/+  
وَلَا يَتَمَنَّوْنَهُ أَبَدًا بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيهِمْ ۚ وَاللهُ عَلِيمٌ بِالظَّالِمِينَ
Hausa
 
Kuma bã zã su yi gũrinta ba har abadã sabõda abin da hannãyen su suka gabãtar. Kuma Allah ne masani ga azzãlumai

Ayah  62:8  الأية
    +/- -/+  
قُلْ إِنَّ الْمَوْتَ الَّذِي تَفِرُّونَ مِنْهُ فَإِنَّهُ مُلَاقِيكُمْ ۖ ثُمَّ تُرَدُّونَ إِلَىٰ عَالِمِ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Hausa
 
Ka ce "Lalle mutuwar nan da kuke gudũ daga gareta,to, lalle ita mai haɗuwa da ku ce sa'an nan kuma anã mayar da kũ zuwa ga masanin fake da bayyane, dõmin Ya bãku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa."

Ayah  62:9  الأية
    +/- -/+  
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نُودِيَ لِلصَّلَاةِ مِن يَوْمِ الْجُمُعَةِ فَاسْعَوْا إِلَىٰ ذِكْرِ اللهِ وَذَرُوا الْبَيْعَ ۚ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ
Hausa
 
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni ! Idan anyi kirã zuwã ga salla a rãnar Jumu'a, sai ku yi aiki zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar ciniki. Wancan ɗinku ne mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance kunã sani.

Ayah  62:10  الأية
    +/- -/+  
فَإِذَا قُضِيَتِ الصَّلَاةُ فَانتَشِرُوا فِي الْأَرْضِ وَابْتَغُوا مِن فَضْلِ اللهِ وَاذْكُرُوا اللهَ كَثِيرًا لَّعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
Hausa
 
Sa'an nan idan an ƙarẽ salla, Sai ku wãtsu a cikin ƙasã kuma ku nẽma daga falalar Allah, kuma ku ambaci sũnan Allah da yawa ɗammãninku, ku sãmi babban rabo.

Ayah  62:11  الأية
    +/- -/+  
وَإِذَا رَأَوْا تِجَارَةً أَوْ لَهْوًا انفَضُّوا إِلَيْهَا وَتَرَكُوكَ قَائِمًا ۚ قُلْ مَا عِندَ اللهِ خَيْرٌ مِّنَ اللهْوِ وَمِنَ التِّجَارَةِ ۚ وَاللهُ خَيْرُ الرَّازِقِينَ
Hausa
 
Kuma idan suka ga wani fatauci kõ kuma wani wasan shagala, sai su yi rũgũguwar fita zuwa gare su, kuma su bar ka kanã tsaye. Ka ce: "Abin da yake a wurin Allah ne mafi alhẽri daga fataucin, alhãli kuwa Allah ne Mafi alhẽrinmãsu arzũtãwa."





© EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us