First Ayah 1 الأية الأولي |
| بِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
يُسَبِّحُ لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ الْمَلِكِ
الْقُدُّوسِ الْعَزِيزِ الْحَكِيمِ
Hausa
Abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin kasã sunã tasbĩhi ga Allah,
Mamallaki,Mai tsarki' Mabuwãyi, Mai hikima.
|
Ayah 62:2 الأية
هُوَ الَّذِي بَعَثَ فِي الْأُمِّيِّينَ رَسُولًا مِّنْهُمْ يَتْلُو عَلَيْهِمْ
آيَاتِهِ وَيُزَكِّيهِمْ وَيُعَلِّمُهُمُ الْكِتَابَ وَالْحِكْمَةَ وَإِن كَانُوا
مِن قَبْلُ لَفِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ
Hausa
Shĩ ne wanda Ya aika, a cikin mabiya al'ãdu, wani Manzo daga gare su yanã
karanta ãyõyinSa a kansu, kuma yanã tsarkake su, kuma yanã sanar da su littafin
da hikimarsa kõ da yake sun kasance daga gabãninsa lalle sunã a cikin ɓata
bayyanãnna.
|
Ayah 62:3 الأية
وَآخَرِينَ مِنْهُمْ لَمَّا يَلْحَقُوا بِهِمْ ۚ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Hausa
Da waɗansu mutãne daga gare su, ba su i da riskuwa da sũ ba, alhãli kuwa shĩ ne
Mabuwãyi, Mai hikima.
|
Ayah 62:4 الأية
ذَٰلِكَ فَضْلُ اللَّهِ يُؤْتِيهِ مَن يَشَاءُ ۚ وَاللَّهُ ذُو الْفَضْلِ
الْعَظِيمِ
Hausa
Waccan wata falalar Allah ce Yanã bãyar da ita ga wanda Yake so. Kuma Allah ne
Ma'abũcin dukan falala mai girma.
|
Ayah 62:5 الأية
مَثَلُ الَّذِينَ حُمِّلُوا التَّوْرَاةَ ثُمَّ لَمْ يَحْمِلُوهَا كَمَثَلِ
الْحِمَارِ يَحْمِلُ أَسْفَارًا ۚ بِئْسَ مَثَلُ الْقَوْمِ الَّذِينَ كَذَّبُوا
بِآيَاتِ اللَّهِ ۚ وَاللَّهُ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ
Hausa
Misãlin waɗanda aka ɗõra wa ɗaukar Attaura sa'an nan ba su ɗauke ta ba, kamar
misãlin jãki ne Yanã ɗaukar littattafai. Tir da misãlin mutãnen nan da suka
ƙaryatã game da ãyõyin Allah! Kuma Allah bã Yã shiryar da mutãnẽ azzãlumai.
|
Ayah 62:6 الأية
قُلْ يَا أَيُّهَا الَّذِينَ هَادُوا إِن زَعَمْتُمْ أَنَّكُمْ أَوْلِيَاءُ لِلَّهِ
مِن دُونِ النَّاسِ فَتَمَنَّوُا الْمَوْتَ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ
Hausa
Ka ce: "Yã kũ waɗandasuka tũba (Yahũdu)! Idan kun riya cẽwa kũ ne zãɓaɓɓun Allah
bã sauran mutanẽ ba, sai ku yi gũrin mutuwa idan kun kasance mãsu gaskiya."
|
Ayah 62:7 الأية
وَلَا يَتَمَنَّوْنَهُ أَبَدًا بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيهِمْ ۚ وَاللَّهُ عَلِيمٌ
بِالظَّالِمِينَ
Hausa
Kuma bã zã su yi gũrinta ba har abadã sabõda abin da hannãyen su suka gabãtar.
Kuma Allah ne masani ga azzãlumai
|
Ayah 62:8 الأية
قُلْ إِنَّ الْمَوْتَ الَّذِي تَفِرُّونَ مِنْهُ فَإِنَّهُ مُلَاقِيكُمْ ۖ ثُمَّ
تُرَدُّونَ إِلَىٰ عَالِمِ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ
تَعْمَلُونَ
Hausa
Ka ce "Lalle mutuwar nan da kuke gudũ daga gareta,to, lalle ita mai haɗuwa da ku
ce sa'an nan kuma anã mayar da kũ zuwa ga masanin fake da bayyane, dõmin Ya bãku
lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
|
Ayah 62:9 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نُودِيَ لِلصَّلَاةِ مِن يَوْمِ الْجُمُعَةِ
فَاسْعَوْا إِلَىٰ ذِكْرِ اللَّهِ وَذَرُوا الْبَيْعَ ۚ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ
إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ
Hausa
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni ! Idan anyi kirã zuwã ga salla a rãnar Jumu'a, sai
ku yi aiki zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar ciniki. Wancan ɗinku ne mafi
alhẽri a gare ku idan kun kasance kunã sani.
|
Ayah 62:10 الأية
فَإِذَا قُضِيَتِ الصَّلَاةُ فَانتَشِرُوا فِي الْأَرْضِ وَابْتَغُوا مِن فَضْلِ
اللَّهِ وَاذْكُرُوا اللَّهَ كَثِيرًا لَّعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
Hausa
Sa'an nan idan an ƙarẽ salla, Sai ku wãtsu a cikin ƙasã kuma ku nẽma daga
falalar Allah, kuma ku ambaci sũnan Allah da yawa ɗammãninku, ku sãmi babban
rabo.
|
Ayah 62:11 الأية
وَإِذَا رَأَوْا تِجَارَةً أَوْ لَهْوًا انفَضُّوا إِلَيْهَا وَتَرَكُوكَ قَائِمًا
ۚ قُلْ مَا عِندَ اللَّهِ خَيْرٌ مِّنَ اللَّهْوِ وَمِنَ التِّجَارَةِ ۚ وَاللَّهُ
خَيْرُ الرَّازِقِينَ
Hausa
Kuma idan suka ga wani fatauci kõ kuma wani wasan shagala, sai su yi rũgũguwar
fita zuwa gare su, kuma su bar ka kanã tsaye. Ka ce: "Abin da yake a wurin Allah
ne mafi alhẽri daga fataucin, alhãli kuwa Allah ne Mafi alhẽrinmãsu arzũtãwa."
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|