« Prev

77. Surah Al-Mursalât سورة المرسلات

Next »
First Ayah   1   الأية الأولي
بِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
وَالْمُرْسَلَاتِ عُرْفًا
Hausa
 
Ina rantsuwa da iskőkin da ake sakőwa jẽre, sună bin jũna.

Ayah   77:2   الأية
فَالْعَاصِفَاتِ عَصْفًا
Hausa
 
Sa'an nan, su zamă iskőki măsu ƙarfi suna kaɗăwa da ƙarfi.

Ayah   77:3   الأية
وَالنَّاشِرَاتِ نَشْرًا
Hausa
 
Kuma, măsu watsa rahama wătsăwa.

Ayah   77:4   الأية
فَالْفَارِقَاتِ فَرْقًا
Hausa
 
sa'an nan, da ăyőyi măsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa.

Ayah   77:5   الأية
فَالْمُلْقِيَاتِ ذِكْرًا
Hausa
 
Sa'an nan da mală'iku măsu jẽfa tunătarwa ga Manzanni.

Ayah   77:6   الأية
عُذْرًا أَوْ نُذْرًا
Hausa
 
Domin yanke hamzari ko dőmin gargadi.

Ayah   77:7   الأية
إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَوَاقِعٌ
Hausa
 
Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne

Ayah   77:8   الأية
فَإِذَا النُّجُومُ طُمِسَتْ
Hausa
 
To, idan taurări aka shăfe haskensu.

Ayah   77:9   الأية
وَإِذَا السَّمَاءُ فُرِجَتْ
Hausa
 
Kuma, idan sama aka tsăge ta.

Ayah   77:10   الأية
وَإِذَا الْجِبَالُ نُسِفَتْ
Hausa
 
Kuma, idan duwătsu aka nike su.

Ayah   77:11   الأية
وَإِذَا الرُّسُلُ أُقِّتَتْ
Hausa
 
Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lőkacin tăra su.

Ayah   77:12   الأية
لِأَيِّ يَوْمٍ أُجِّلَتْ
Hausa
 
Domin babbar rănar da aka yi wa ajali.

Ayah   77:13   الأية
لِيَوْمِ الْفَصْلِ
Hausa
 
Domin rănar rarrabẽwa .

Ayah   77:14   الأية
وَمَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الْفَصْلِ
Hausa
 
Kuma, me ya sanar da kai rănar rarrabẽwa?

Ayah   77:15   الأية
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Hausa
 
Bone yă tabbata a rănar nan, ga măsu ƙaryatăwa!

Ayah   77:16   الأية
أَلَمْ نُهْلِكِ الْأَوَّلِينَ
Hausa
 
Ashe, ba Mu halakar da (măsu ƙaryatăw) na farko ba.

Ayah   77:17   الأية
ثُمَّ نُتْبِعُهُمُ الْآخِرِينَ
Hausa
 
Sa'an nan, kuma ză Mu biyar musu da na ƙarshe?

Ayah   77:18   الأية
كَذَٰلِكَ نَفْعَلُ بِالْمُجْرِمِينَ
Hausa
 
Haka nan, Muke aikatăwa da măsu yin laifi.

Ayah   77:19   الأية
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Hausa
 
Bone yă tabbata a rănar nan ga măsu ƙaryatăwa!

Ayah   77:20   الأية
أَلَمْ نَخْلُقكُّم مِّن مَّاءٍ مَّهِينٍ
Hausa
 
Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba.

Ayah   77:21   الأية
فَجَعَلْنَاهُ فِي قَرَارٍ مَّكِينٍ
Hausa
 
Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce.

Ayah   77:22   الأية
إِلَىٰ قَدَرٍ مَّعْلُومٍ
Hausa
 
Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna.

Ayah   77:23   الأية
فَقَدَرْنَا فَنِعْمَ الْقَادِرُونَ
Hausa
 
Sa'an nan, Muka nũna iyăwarMu? Madalla da Mu, Măsu nũna iyăwa.

Ayah   77:24   الأية
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Hausa
 
Bone ya tabbata a rănar nan ga măsu ƙaryatăwa!

Ayah   77:25   الأية
أَلَمْ نَجْعَلِ الْأَرْضَ كِفَاتًا
Hausa
 
Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattară ba.

Ayah   77:26   الأية
أَحْيَاءً وَأَمْوَاتًا
Hausa
 
Ga răyayyu da matattu,

Ayah   77:27   الأية
وَجَعَلْنَا فِيهَا رَوَاسِيَ شَامِخَاتٍ وَأَسْقَيْنَاكُم مَّاءً فُرَاتًا
Hausa
 
Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwătsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dăɗi?

Ayah   77:28   الأية
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Hausa
 
Bone ya tabbata, a rănar nan, ga măsu ƙaryatăwa!

Ayah   77:29   الأية
انطَلِقُوا إِلَىٰ مَا كُنتُم بِهِ تُكَذِّبُونَ
Hausa
 
Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatăwa game da shi!

Ayah   77:30   الأية
انطَلِقُوا إِلَىٰ ظِلٍّ ذِي ثَلَاثِ شُعَبٍ
Hausa
 
Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku.

Ayah   77:31   الأية
لَّا ظَلِيلٍ وَلَا يُغْنِي مِنَ اللَّهَبِ
Hausa
 
Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadătarwa daga harshen wuta.

Ayah   77:32   الأية
إِنَّهَا تَرْمِي بِشَرَرٍ كَالْقَصْرِ
Hausa
 
Lalle ne, ita, tană jifă da tartsatsi kamar sőraye.

Ayah   77:33   الأية
كَأَنَّهُ جِمَالَتٌ صُفْرٌ
Hausa
 
Kamar dai su raƙumma ne baƙăƙe.

Ayah   77:34   الأية
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Hausa
 
Bone ya tabbata, a rănar nan, ga măsu ƙaryatăwa!

Ayah   77:35   الأية
هَٰذَا يَوْمُ لَا يَنطِقُونَ
Hausa
 
Wannan, yini ne da bă ză su iya yin magana ba.

Ayah   77:36   الأية
وَلَا يُؤْذَنُ لَهُمْ فَيَعْتَذِرُونَ
Hausa
 
Bă ză a yi musu izni ba, balle su kăwo hanzari.

Ayah   77:37   الأية
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Hausa
 
Bone ya tabbata, a rănar nan, ga măsu ƙaryatăwa!

Ayah   77:38   الأية
هَٰذَا يَوْمُ الْفَصْلِ ۖ جَمَعْنَاكُمْ وَالْأَوَّلِينَ
Hausa
 
Wannan rănar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutănen farko.

Ayah   77:39   الأية
فَإِن كَانَ لَكُمْ كَيْدٌ فَكِيدُونِ
Hausa
 
To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita.

Ayah   77:40   الأية
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Hausa
 
Bone ya tabbata, a rănar nan, ga măsu ƙaryatăwa!

Ayah   77:41   الأية
إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي ظِلَالٍ وَعُيُونٍ
Hausa
 
Lalle ne, măsu taƙawa suna a cikin inuwőwi da marẽmari.

Ayah   77:42   الأية
وَفَوَاكِهَ مِمَّا يَشْتَهُونَ
Hausa
 
Da wasu 'ya'yan ităce irin waɗanda suke marmari.

Ayah   77:43   الأية
كُلُوا وَاشْرَبُوا هَنِيئًا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Hausa
 
(A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni'ima sabőda abin da kuka kasance kuna aikatăwa."

Ayah   77:44   الأية
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ
Hausa
 
Lalle ne, Mũ haka Muke săka wa măsu kyautatăwa.

Ayah   77:45   الأية
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Hausa
 
Bone ya tabbata, a rănar nan, ga măsu ƙaryatăwa!

Ayah   77:46   الأية
كُلُوا وَتَمَتَّعُوا قَلِيلًا إِنَّكُم مُّجْرِمُونَ
Hausa
 
(Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dădi kaɗan, lalle ne dai ku măsu laifi ne."

Ayah   77:47   الأية
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Hausa
 
Bone ya tabbata, a rănar nan, ga măsu ƙaryatăwa!

Ayah   77:48   الأية
وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ارْكَعُوا لَا يَرْكَعُونَ
Hausa
 
Kuma, idan an ce musu: "Ku yi rukũ'i; bă ză su yi rukũ'in (salla) ba."

Ayah   77:49   الأية
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Hausa
 
Bone ya tabbata, a rănar nan, ga măsu ƙaryatăwa!

Ayah   77:50   الأية
فَبِأَيِّ حَدِيثٍ بَعْدَهُ يُؤْمِنُونَ
Hausa
 
To, da wane lăbări (Littăfi), waninsa (Alƙur'ăni) ză su yi ĩmăni 

© EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us