wanda Yake da mulkin sammai da ƙasa kuma bai riƙi abin haihuwa ba, kuma abõkin
tãrayya bai kasance a gare Shi ba a cikin mulkinSa kuma Ya halitta dukan kowane
abu, sa'an nan Ya ƙaddara shi ƙaddarãwa.
Kuma suka riƙi abũbuwan bautawa, baicin Shi, bã su yin halittar kõme alhãli sũ
ne ake halittãwa kuma bã su mallakar wa kansu wata cũta ko wani amfãni, kuma bã
su mallakar mutuwa kuma bã su mallakar rãyarwa, kuma bã su mallakar tãyarwa.
Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Wannan bã kõme ba ne fãce ƙiron ƙarya da
(Muhammadu) ya ƙirƙira shi, kuma waɗansu mutãne na dabam suka taimake shi a
kansa." To, lalle ne sun jẽ wa zãlunci da karkacẽwar magana.
Kuma suka ce: "Mẽne ne ga wannan Manzo, yanã cin abinci, kuma yanã tafiya a
cikin kãsuwanni! Don me ba a saukar da malã'ika zuwa gare shi ba, dõmin ya
kasance mai gargaɗi tãre da shi?
"Kõ kuwa a jẽfo wata taska zuwa gare shi, kõ kuwa wata gõna ta kasance a gare
shi, yanã ci daga gare ta?" Kuma azzãlumai suka ce: "Bã ku bin kõwa, fãce mutum
sihirtacce:"
Albarka ta tabbata ga wanda idan Ya so, Yã sanya maka mafi alhẽri daga wannan
(abu): gõnaki, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, kuma Ya sanya maka manyan
gidãje.
Kuma rãnar da Yake tãra su da abin da suke bauta wa, baicin Allah sai Ya ce:
"Shin kũ nekuka ɓatar, da bãyiNa, waɗannan, ko kuwa su ne suka ɓata daga hanya?"
suka ce: "Tsarki ya tabbata a gare Ka, bã ya kasancẽwa agare mu, mu riƙi waɗansu
majiɓinta, baicin Kai, kuma amma Kã jiyar da su dãɗi sũ da ubanninsu har suka
manta da Tunãtarwa, kuma sun kasance mutãne ne halakakku."
To, lalle ne, sun ƙaryata game da abin da kuke cẽwa,sabõda haka bã ku iya
karkatarwa ga (maganarsu), kuma ba ku iya taimako (ga hana azãba), kuma wanda ya
yi zãlunci a cikinku zã Mu ɗanɗana masa azãba mai girma.
Kuma ba Mu aika ba, a gabãninka daga Manzanni, fãce lalle sũ haƙĩƙa sunã cin
abinci kuma sunã tafiya a cikin kasuwõyi. Kuma Mun sanya sãshen mutãne fitina ga
sãshe. Shin kunã yin haƙuri? Kuma Ubangijia Ya kasance Mai gani.
Kuma waɗanda bã su fatan haɗuwa da Mu suka ce: "Don me ba a saukar da malã'ĩku
ba a kanmu, kõ kuwa mu ga Ubangijinmu?" Lalle ne sun kangara a cikin rãyukansu,
kuma suka yi tsaurin kai, tsaurin kai mai girma.
Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Don me ba a saukar da Alƙur'ãni a kansa ba,
jimla guda?" kamar wancan! Dõmin Mu ƙarfafa zũciyarka game da shi, kuma Mun
jẽranta karanta shi da hankali jẽrantawa.
Kuma mutãnen Nũhu, a lõkacin da suka ƙaryata Manzanni, Muka nutsar da su, kuma
Muka sanya su wata ãya ga mutãne, kuma Muka yi tattalin azãba mai raɗaɗi ga
azzãlumai.
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, (¡uraishi) sun jẽ a kan alƙaryar nan wadda aka yi wa
ruwa, ruwan azãba. Shin, ba su kasance sun gan ta ba? Ã'a, sun kasance bã su
ƙaunar tãyarwa (a ¡iyãma).
"Lalle ne, yã yi kusa ya ɓatar da mu daga Ubangijinmu, in bã dõmin da muka yi
haƙuri a kansu ba."Kuma zã su sani a lõkacin da suke ganin azãba, wãne ne mafi
ɓacẽwa ga hanya!
Kuma shĩ ne Ya garwaya tẽkuna biyu, wannan mai dãdi, mai sauƙin haɗiya, kuma
wannan gishiri gurɓatacce, kuma Ya sanya wani shãmaki a tsakãninsu da kãriya mai
shãmakacẽwa.
Wanda Ya halitta sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, a cikin kwãnuka
shida sa'an nan Yã daidaitu a kan Al'arshi Mai rahama, sai ka tambayi mai bãyar
da lãbãri game da Shi.
Idan aka ce musu, "Ku yi sujada ga Mai rahama." Sai su ce: "Mene ne Mai rahama?
Ashe zã mu yi sujada ga abin da kuke umurnin mu?"Kuma wannan (magana ta ƙãra
musu gudu.
Kuma waɗanda bã su kiran wani ubangiji tãre da Allah, kuma bã su kashe rai wanda
Allah Ya haramta fãce da hakki kuma bã su yin zina. Kuma wanda ya aikata wancan,
zai gamu da laifuffuka,
Sai wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai to, waɗancan
Allah Yanã musanya miyãgun ayyukansu da mãsu kyau. Allah Ya kasance Mai gãfara
Mai jin ƙai.