First Ayah 1 الأية الأوليبِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
سَأَلَ سَائِلٌ بِعَذَابٍ وَاقِعٍ
Hausa
Wani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa.
|
Ayah 70:2 الأية
لِّلْكَافِرِينَ لَيْسَ لَهُ دَافِعٌ
Hausa
Ga kãfirai, bã ta da mai tunkuɗẽwa.
|
Ayah 70:3 الأية
مِّنَ اللَّهِ ذِي الْمَعَارِجِ
Hausa
Daga Allah Mai matãkala.
|
Ayah 70:4 الأية
تَعْرُجُ الْمَلَائِكَةُ وَالرُّوحُ إِلَيْهِ فِي يَوْمٍ كَانَ مِقْدَارُهُ
خَمْسِينَ أَلْفَ سَنَةٍ
Hausa
Malã'iku da Ruhi (Jibrila) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda
gwargwadonsa, shẽkara dubu hamsin ne.
|
Ayah 70:5 الأية
فَاصْبِرْ صَبْرًا جَمِيلًا
Hausa
Sabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo.
|
Ayah 70:6 الأية
إِنَّهُمْ يَرَوْنَهُ بَعِيدًا
Hausa
Lalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa.
|
Ayah 70:7 الأية
وَنَرَاهُ قَرِيبًا
Hausa
Kuma Mu, Muna ganin ta a kusa.
|
Ayah 70:8 الأية
يَوْمَ تَكُونُ السَّمَاءُ كَالْمُهْلِ
Hausa
Rãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa.
|
Ayah 70:9 الأية
وَتَكُونُ الْجِبَالُ كَالْعِهْنِ
Hausa
Kuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi.
|
Ayah 70:10 الأية
وَلَا يَسْأَلُ حَمِيمٌ حَمِيمًا
Hausa
Kuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake.
|
Ayah 70:11 الأية
يُبَصَّرُونَهُمْ ۚ يَوَدُّ الْمُجْرِمُ لَوْ يَفْتَدِي مِنْ عَذَابِ يَوْمِئِذٍ
بِبَنِيهِ
Hausa
Ana sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar
rãnar nan, da ɗiyansa,
|
Ayah 70:12 الأية
وَصَاحِبَتِهِ وَأَخِيهِ
Hausa
Da matarsa da ɗan'uwansa.
|
Ayah 70:13 الأية
وَفَصِيلَتِهِ الَّتِي تُؤْوِيهِ
Hausa
Da danginsa, mãsu tattarã shi.
|
Ayah 70:14 الأية
وَمَن فِي الْأَرْضِ جَمِيعًا ثُمَّ يُنجِيهِ
Hausa
Da wanda ke a cikin dũniya duka gabã ɗaya, sa'an nan fansar, ta tsĩrar da shi.
|
Ayah 70:15 الأية
كَلَّا ۖ إِنَّهَا لَظَىٰ
Hausa
A'aha! Lalle ne fa, ita ce Lazã,
|
Ayah 70:16 الأية
نَزَّاعَةً لِّلشَّوَىٰ
Hausa
Mai twãle fãtar goshi.
|
Ayah 70:17 الأية
تَدْعُو مَنْ أَدْبَرَ وَتَوَلَّىٰ
Hausa
Tanã kiran wanda ya jũya bãya (daga addini) kuma ya kau da kai.
|
Ayah 70:18 الأية
وَجَمَعَ فَأَوْعَىٰ
Hausa
Ya tãra (dũkiya), kuma ya sanya ta a cikin jaka.
|
Ayah 70:19 الأية
إِنَّ الْإِنسَانَ خُلِقَ هَلُوعًا
Hausa
Lalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi.
|
Ayah 70:20 الأية
إِذَا مَسَّهُ الشَّرُّ جَزُوعًا
Hausa
Idan sharri ya shãfe shi, ya kãsa haƙuri.
|
Ayah 70:21 الأية
وَإِذَا مَسَّهُ الْخَيْرُ مَنُوعًا
Hausa
Kuma idan alhẽri ya shãfe shi, ya yi rõwa.
|
Ayah 70:22 الأية
إِلَّا الْمُصَلِّينَ
Hausa
Sai mãsu yin salla,
|
Ayah 70:23 الأية
الَّذِينَ هُمْ عَلَىٰ صَلَاتِهِمْ دَائِمُونَ
Hausa
Waɗanda suke, a kan sallarsu, su, mãsu dawwama ne.
|
Ayah 70:24 الأية
وَالَّذِينَ فِي أَمْوَالِهِمْ حَقٌّ مَّعْلُومٌ
Hausa
Kuma waɗanda a cikin dũkiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne.
|
Ayah 70:25 الأية
لِّلسَّائِلِ وَالْمَحْرُومِ
Hausa
Ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hanã wa roƙon.
|
Ayah 70:26 الأية
وَالَّذِينَ يُصَدِّقُونَ بِيَوْمِ الدِّينِ
Hausa
Da waɗannan da ke gaskata rãnar sakamako.
|
Ayah 70:27 الأية
وَالَّذِينَ هُم مِّنْ عَذَابِ رَبِّهِم مُّشْفِقُونَ
Hausa
Da waɗannan sabõda azãbar Ubangijinsu, suna jin tsõro.
|
Ayah 70:28 الأية
إِنَّ عَذَابَ رَبِّهِمْ غَيْرُ مَأْمُونٍ
Hausa
Lalle ne, azãbar Ubangijinsu bã wadda ake iya amincẽwaba ce.
|
Ayah 70:29 الأية
وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ
Hausa
Da waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne.
|
Ayah 70:30 الأية
إِلَّا عَلَىٰ أَزْوَاجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ
مَلُومِينَ
Hausa
Sai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka. To lalle
ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne.
|
Ayah 70:31 الأية
فَمَنِ ابْتَغَىٰ وَرَاءَ ذَٰلِكَ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْعَادُونَ
Hausa
To, duk wanda ya nẽmi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu
ƙetare iyãka.
|
Ayah 70:32 الأية
وَالَّذِينَ هُمْ لِأَمَانَاتِهِمْ وَعَهْدِهِمْ رَاعُونَ
Hausa
Kuma da waɗannan da suke ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne.
|
Ayah 70:33 الأية
وَالَّذِينَ هُم بِشَهَادَاتِهِمْ قَائِمُونَ
Hausa
Kuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, mãsu dãgẽwa ne.
|
Ayah 70:34 الأية
وَالَّذِينَ هُمْ عَلَىٰ صَلَاتِهِمْ يُحَافِظُونَ
Hausa
Kuma waɗanda suke, a kan sallarsu, mãsu tsarẽwa ne.
|
Ayah 70:35 الأية
أُولَٰئِكَ فِي جَنَّاتٍ مُّكْرَمُونَ
Hausa
Waɗannan, a cikin gidãjen Aljanna, waɗanda ake girmamãwa ne
|
Ayah 70:36 الأية
فَمَالِ الَّذِينَ كَفَرُوا قِبَلَكَ مُهْطِعِينَ
Hausa
Mẽ yã sãmi waɗanda suka kãfirta, a wajenka, sunã gaugãwar (gudu).
|
Ayah 70:37 الأية
عَنِ الْيَمِينِ وَعَنِ الشِّمَالِ عِزِينَ
Hausa
Daga jihar dãma, kuma daga jihar hagu, jama'a-jama'a!
|
Ayah 70:38 الأية
أَيَطْمَعُ كُلُّ امْرِئٍ مِّنْهُمْ أَن يُدْخَلَ جَنَّةَ نَعِيمٍ
Hausa
Shin kõwane mutum daga cikinsu yana nẽman a shigar da shi a Aljannar ni'ima ne
(ba da wani aiki ba)?
|
Ayah 70:39 الأية
كَلَّا ۖ إِنَّا خَلَقْنَاهُم مِّمَّا يَعْلَمُونَ
Hausa
A'aha! Lalle Mũ, Mun halitta su, daga abin da suka sani.
|
Ayah 70:40 الأية
فَلَا أُقْسِمُ بِرَبِّ الْمَشَارِقِ وَالْمَغَارِبِ إِنَّا لَقَادِرُونَ
Hausa
Sabõda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wurãren ɓullõwar rãna da wurãren
fãɗuwarta ba, lalle Mũ, Mãsu iyãwa ne.
|
Ayah 70:41 الأية
عَلَىٰ أَن نُّبَدِّلَ خَيْرًا مِّنْهُمْ وَمَا نَحْنُ بِمَسْبُوقِينَ
Hausa
Ga Mu musanya waɗanda suke mafi alhẽri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda
ake rinjãya ba.
|
Ayah 70:42 الأية
فَذَرْهُمْ يَخُوضُوا وَيَلْعَبُوا حَتَّىٰ يُلَاقُوا يَوْمَهُمُ الَّذِي
يُوعَدُونَ
Hausa
Sabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda
ake yi musu alkawari (da ita) .
|
Ayah 70:43 الأية
يَوْمَ يَخْرُجُونَ مِنَ الْأَجْدَاثِ سِرَاعًا كَأَنَّهُمْ إِلَىٰ نُصُبٍ
يُوفِضُونَ
Hausa
Rãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata
kafaffiyar (tuta), suke yin gaugãwa.
|
Ayah 70:44 الأية
خَاشِعَةً أَبْصَارُهُمْ تَرْهَقُهُمْ ذِلَّةٌ ۚ ذَٰلِكَ الْيَوْمُ الَّذِي كَانُوا
يُوعَدُونَ
Hausa
Maƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka
kasance ana yi musa alkawari (a kansa.)
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|