First Ayah 1 الأية الأوليبِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
قُلْ أُوحِيَ إِلَيَّ أَنَّهُ اسْتَمَعَ نَفَرٌ مِّنَ الْجِنِّ فَقَالُوا إِنَّا
سَمِعْنَا قُرْآنًا عَجَبًا
Hausa
Ka ce: "An yi wahayi zuwa gare ni cewa wasu jama'a na aljannu sun saurũri
(karatuna), sai suka ce: Lalle ne mũ mun ji wani abin karantãwa (Alƙui'ãni), mai
ban mãmãki."
|
Ayah 72:2 الأية
يَهْدِي إِلَى الرُّشْدِ فَآمَنَّا بِهِ ۖ وَلَن نُّشْرِكَ بِرَبِّنَا أَحَدًا
Hausa
"Yana nũni zuwa ga hanyar ƙwarai, sabõda haka mun yi ĩmãni da shi bã zã mu kõma
bautã wa Ubangijinmu tãre da kõwa ba."
|
Ayah 72:3 الأية
وَأَنَّهُ تَعَالَىٰ جَدُّ رَبِّنَا مَا اتَّخَذَ صَاحِبَةً وَلَا وَلَدًا
Hausa
"Kuma lalle ne shĩ girman Ubangijinmu, Ya ɗaukaka, bai riƙi mãta ba, kuma bai
riƙi ɗã ba."
|
Ayah 72:4 الأية
وَأَنَّهُ كَانَ يَقُولُ سَفِيهُنَا عَلَى اللَّهِ شَطَطًا
Hausa
"Kuma lalle ne shi, wãwanmu ya kasance yana faɗar abin da ya ƙetare haddi ga
Allah."
|
Ayah 72:5 الأية
وَأَنَّا ظَنَنَّا أَن لَّن تَقُولَ الْإِنسُ وَالْجِنُّ عَلَى اللَّهِ كَذِبًا
Hausa
"Kuma lalle ne mũ, mun yi zaton mutum da aljani bã zã su iya faɗar ƙarya ba ga
Allah."
|
Ayah 72:6 الأية
وَأَنَّهُ كَانَ رِجَالٌ مِّنَ الْإِنسِ يَعُوذُونَ بِرِجَالٍ مِّنَ الْجِنِّ
فَزَادُوهُمْ رَهَقًا
Hausa
"Kuma lalle ne shi wasu maza daga cikin mutãne, sun kasance sunã nẽman tsari da
wasu maza daga cikin aljannu, sabõda haka suka ƙara musu girman kai."
|
Ayah 72:7 الأية
وَأَنَّهُمْ ظَنُّوا كَمَا ظَنَنتُمْ أَن لَّن يَبْعَثَ اللَّهُ أَحَدًا
Hausa
"Kuma lalle ne sũ, sun yi zato, kamar yadda kuka yi zato, cewa Allah bã zai aiko
kowa ba."
|
Ayah 72:8 الأية
وَأَنَّا لَمَسْنَا السَّمَاءَ فَوَجَدْنَاهَا مُلِئَتْ حَرَسًا شَدِيدًا وَشُهُبًا
Hausa
"Kuma lalle ne mũ mun nẽmi (hawan) sama, sai muka, sãme ta an cika ta da tsaro
mai tsanani da kuma yũlãye."
|
Ayah 72:9 الأية
وَأَنَّا كُنَّا نَقْعُدُ مِنْهَا مَقَاعِدَ لِلسَّمْعِ ۖ فَمَن يَسْتَمِعِ الْآنَ
يَجِدْ لَهُ شِهَابًا رَّصَدًا
Hausa
"Kuma lalle ne mũ, mun kasance muna zama daga garẽta, a wurãren zama dõmin
saurare. To wanda ya yi saurãre a yanzu, zai sãmi yũla, mai dãko dõminsa."
|
Ayah 72:10 الأية
وَأَنَّا لَا نَدْرِي أَشَرٌّ أُرِيدَ بِمَن فِي الْأَرْضِ أَمْ أَرَادَ بِهِمْ
رَبُّهُمْ رَشَدًا
Hausa
"Kuma lalle ne mũ ba mu sani ba, shin, sharri ne aka yi nufi ga waɗanda ke cikin
ƙasa, ko Ubangijinsu Yã yi nufin shiriya a gare su ne?"
|
Ayah 72:11 الأية
وَأَنَّا مِنَّا الصَّالِحُونَ وَمِنَّا دُونَ ذَٰلِكَ ۖ كُنَّا طَرَائِقَ قِدَدًا
Hausa
"Kuma lalle ne mũ, akwai sãlaihai a cikinmu, kuma akwai a cikinmu waɗanda ba
haka bã mun kasance ƙungiyõyi dabam-dabam."
|
Ayah 72:12 الأية
وَأَنَّا ظَنَنَّا أَن لَّن نُّعْجِزَ اللَّهَ فِي الْأَرْضِ وَلَن نُّعْجِزَهُ
هَرَبًا
Hausa
"Kuma lalle ne mũ mun tabbatã bã zã mu buwãyi Allah ba, a cikin ƙasa, kuma bã zã
mu buwãye Shi da gudu ba."
|
Ayah 72:13 الأية
وَأَنَّا لَمَّا سَمِعْنَا الْهُدَىٰ آمَنَّا بِهِ ۖ فَمَن يُؤْمِن بِرَبِّهِ فَلَا
يَخَافُ بَخْسًا وَلَا رَهَقًا
Hausa
"Kuma lalle ne mũ, a lõkacin da muka ji shiriya, mun yi ĩmãni da ita. To wanda
ya yi ĩimãni da Uhangijinsa, bã zai ji tsõron nakkasa ba, kuma bã zai ji tsõron
zãlunci ba."
|
Ayah 72:14 الأية
وَأَنَّا مِنَّا الْمُسْلِمُونَ وَمِنَّا الْقَاسِطُونَ ۖ فَمَنْ أَسْلَمَ
فَأُولَٰئِكَ تَحَرَّوْا رَشَدًا
Hausa
"Kuma lalle ne mũ akwai a cikinmu, waɗanda suka mĩƙa wuya, kuma akwai a cikinmu
karkatattu. to, wanda ya mĩƙa wuya waɗancan kam sun nufi shiryuwa."
|
Ayah 72:15 الأية
وَأَمَّا الْقَاسِطُونَ فَكَانُوا لِجَهَنَّمَ حَطَبًا
Hausa
"Kuma amma karkatattu sai suka kasance makãmashi ga Jahannama."
|
Ayah 72:16 الأية
وَأَن لَّوِ اسْتَقَامُوا عَلَى الطَّرِيقَةِ لَأَسْقَيْنَاهُم مَّاءً غَدَقًا
Hausa
"Kuma dã sun tsayu sõsai a kan hanya, dã lalle Mun shãyar da su ruwa mai yawa."
|
Ayah 72:17 الأية
لِّنَفْتِنَهُمْ فِيهِ ۚ وَمَن يُعْرِضْ عَن ذِكْرِ رَبِّهِ يَسْلُكْهُ عَذَابًا
صَعَدًا
Hausa
"Domin Mu jarraba su a ciki, kuma wanda ya kau da kai daga tuna Ubangijinsa,
Ubangijinsa zai shigar da shi azãba mai hauhawa."
|
Ayah 72:18 الأية
وَأَنَّ الْمَسَاجِدَ لِلَّهِ فَلَا تَدْعُوا مَعَ اللَّهِ أَحَدًا
Hausa
"Kuma lalle ne wurãren sujada na Allah ne, saboda haka kada ku kira kõwa tãre da
Allah (da su, a cikinsu)."
|
Ayah 72:19 الأية
وَأَنَّهُ لَمَّا قَامَ عَبْدُ اللَّهِ يَدْعُوهُ كَادُوا يَكُونُونَ عَلَيْهِ
لِبَدًا
Hausa
"Kuma, lalle ne shi, a lõkacin da bãwan Allah ke kiran Sa sun yi kusa su zama
kamar shirgi a kansa."
|
Ayah 72:20 الأية
قُلْ إِنَّمَا أَدْعُو رَبِّي وَلَا أُشْرِكُ بِهِ أَحَدًا
Hausa
Ka ce: "lna kiran Ubangijina ne kawai, kuma bã zan tãra kowa da Shi ba."
|
Ayah 72:21 الأية
قُلْ إِنِّي لَا أَمْلِكُ لَكُمْ ضَرًّا وَلَا رَشَدًا
Hausa
Ka ce: "Lalle ne, nĩ bã ni mallakar wata cũta gare ku, kuma bã ni mallakar wani
alhẽri."
|
Ayah 72:22 الأية
قُلْ إِنِّي لَن يُجِيرَنِي مِنَ اللَّهِ أَحَدٌ وَلَنْ أَجِدَ مِن دُونِهِ
مُلْتَحَدًا
Hausa
Ka ce: "Lalle ne, nĩ kõwa bã ya iya cẽtona daga Allah, kuma bã zan iya sãmun
mafaka ba daga gare Shi."
|
Ayah 72:23 الأية
إِلَّا بَلَاغًا مِّنَ اللَّهِ وَرِسَالَاتِهِ ۚ وَمَن يَعْصِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ
فَإِنَّ لَهُ نَارَ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا
Hausa
"Fãce iyarwa, daga Allah, da manzancinsa. To, wanda ya sãɓa wa Allah da
ManzonSa, to, lalle yana da wutar Jahannama suna mãsu dawwama a cikinta, har
abada."
|
Ayah 72:24 الأية
حَتَّىٰ إِذَا رَأَوْا مَا يُوعَدُونَ فَسَيَعْلَمُونَ مَنْ أَضْعَفُ نَاصِرًا
وَأَقَلُّ عَدَدًا
Hausa
Har idan sun ga abin da ake yi musu gargaɗi da shi, to, zã su san wanda ya zama
mafi raunin mataimaki da mafi ƙarancin adadi.
|
Ayah 72:25 الأية
قُلْ إِنْ أَدْرِي أَقَرِيبٌ مَّا تُوعَدُونَ أَمْ يَجْعَلُ لَهُ رَبِّي أَمَدًا
Hausa
Ka ce: "Ban sani ba a kusa ne abin da ake yi muku gargaɗi da shi, ko Ubangijina
Ya sanya maSa dõgon ajali!"
|
Ayah 72:26 الأية
عَالِمُ الْغَيْبِ فَلَا يُظْهِرُ عَلَىٰ غَيْبِهِ أَحَدًا
Hausa
"Shi ɗai ne Masanin fake sabõda haka, bã Ya bayyana gaibinSa ga kowa."
|
Ayah 72:27 الأية
إِلَّا مَنِ ارْتَضَىٰ مِن رَّسُولٍ فَإِنَّهُ يَسْلُكُ مِن بَيْنِ يَدَيْهِ وَمِنْ
خَلْفِهِ رَصَدًا
Hausa
"Fãce ga wanda Yã yarda da shi, wato wani manzo sa'an nan lalle ne, zai sanya
gãdi a gaba gare shi da bãya gare shi."
|
Ayah 72:28 الأية
لِّيَعْلَمَ أَن قَدْ أَبْلَغُوا رِسَالَاتِ رَبِّهِمْ وَأَحَاطَ بِمَا لَدَيْهِمْ
وَأَحْصَىٰ كُلَّ شَيْءٍ عَدَدًا
Hausa
"Dõmin Ya san lalle, sun iyar da sãƙonnin Ubangijinsu, kuma (Shi Ubangijin) Yã
kẽwaye su da sani, kuma Yã lissafe dukan kõme da ƙididdiga."
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|