Shĩ ne wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin wasu kwãnuka shida, sa'an nan Ya
daidaitu a kan Al'arshi, Yanã sanin abin da ke shiga cikin ƙasa da abin da ke
fita daga gare ta, da abin da ke sauka daga sama da abin da ke hawa cikinta,
kuma Shĩ yanã tareda ku duk inda kuka kasance. Kuma Allah Mai gani ne ga abin da
kuke aikatãwa.
Ku yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, kuma ku ciyar daga abin da Allah Ya wakilta ku
a cikinsa (na dũkiya). To, waɗannan da suka yi ĩmãni daga cikinku, kuma suka
ciyar, sunã da wani sakamako mai girma.
kuma me ya same ku, bã zã ku yi ĩmãni ba da Allah, alhãli kuwa manzonSa na kiran
ku dõmin ku yi ĩmãni da Ubangijinku, kuma lalle Allah Ya karɓi alkawarinku (cẽwa
zã ku bauta Masa)? (Ku bauta Masa) idan kun kasance mãsu ĩmãni.
Shĩ ne wanda ke sassaukar da ãyõyi bayyanannu ga BãwanSa, dõmin Ya fitar da ku
daga duffai zuwa ga haske, kuma lalle Allah haƙĩƙa Mai tausayi ne gare ku, Mai
jin ƙai.
Kuma me ya sãme ku, bã zã ku ciyar ba dõmin ɗaukaka kalmar Allah, alhãli kuwa
gãdon sammai da ƙasã na Allah ne? Wanda ya ciyar a gabãnin cin nasara, kuma ya
yi yãƙi daga cikinku, bã ya zama daidai (da wanda bai yi haka ba). waɗancan ne
mafĩfĩta girman daraja bisa ga waɗanda suka ciyar daga bãya kuma suka yi yãƙi.
Kuma dukansu Allah Ya yi musu wa'adi da (sakamako) mai kyau, kuma Allah Masani
ne ga abin da kuke aikatãwa.
Rãnar da zã ka ga mũminai maza da mũminai mãtã haskensu nã tafiya a gaba gare
su, da kuma dãma gare su. (Anã ce musu) "Bushãrarku a yau, ita ce gidajen
Aljanna." Ruwa na gudãna daga ƙarƙashinsu sunã mãsu dawwama a cikinsu. Wannan,
shĩ ne babban rabo mai girma.
Rãnar da munafikai maza da munãfikai mãtã ke cẽwa waɗanda suka yi ĩmãni: "Ku
dũbẽ mu, mu yi makãmashi daga haskenku!" A ce (musu): "Ku kõma a bãyanku, dõmin
ku nẽmo wani haske." Sai a danne a tsakãninsu da wani gãru yanã da wani ƙyaure,
a cikinsa nan rahama take, kuma a bãyansa daga wajensa azaba take.
Sunã kiran su, "Ashe, bã tãre muke da ku ba?" Su ce: "Ĩ, amma kũ, kun fitini
kanku, kuma kun yi jiran wata masĩfa, kuma kunyi shakka, kuma waɗansu
gũrace-gũrace sun rũɗe ku, har umurnin Allah ya jẽ muku, kumamarũɗi ya rũɗe ku
game da Allah."
"To, a yau bã zã a karɓi fansa daga gare ku ba. Kuma bã zã a karɓa daga waɗanda
suka kãfirta ba. Makõmarku wutã ce, ita ce mai dacẽwa da ku, kuma makõmarku ɗin
nan tã mũnana."
Shin, lõkaci bai yi ba ga wa ɗanda suka yi ĩmãnĩ zukãtansu su yi tawãlu'i ga
ambaton Allah da abin da ya sauka daga gaskiya? Kada su kasance kamar waɗanda
aka bai wa littãfi a gabãnin haka, sai zãmani ya yi tsawo a kansu, sabõda haka
zukãtansu suka ƙẽƙashe, kuma masu yawa daga cikinsu fãsiƙai ne.
Kuma waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da MazanninSa waɗannan sũ ne kamãlar
gaskatãwa kuma su ne mãsu shahãda awurin Ubangjinsu. sunã da sakamakonsu da
haskensu. waɗanda suka kafirta kuma suka ƙaryata game da ãyõyinMu, waɗannan su
ne'yan Jahĩm.
Ku sani cẽwa rãyuwar dũniya wãsã ɗai ce da shagala da ƙawa da alafahri a
tsakãninku da gãsar wadãta ta dũkiya da ɗiya, kamar misãlin shũka wadda
yabanyarta ta bãyar da sha'awa ga manõma, sa'an nan ta ƙẽƙashe, har ka ganta tã
zama rawaya sa'an nan ta kõma rauno. Kuma, alãmra akwai azãba mai tsanani da
gãfara daga Allah da yarda. Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba fãce ɗan jin dãɗin
rũɗi kawai.
Ku yi tsẽre zuwa ga (nẽman) gãfara daga Ubangjinku, da Aljanna fãɗinta kamar
fãɗin samã da ƙasã ne, an yi tattalinta dõmin waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da
ManzanninSa. Wannan falalar Allah ce, Yanã bãyar da ita ga wanda Ya so. Kuma
Allah Mai falala ne Mai girma.
Wata masifa bã zã ta auku ba a cikin ƙasã kõ a cikin rayukanku fãce tanã a cikin
littãfi a gabãnin Mu halitta ta. Lalle wannan, ga Allah, mai sauƙi ne.
Dõmin kada ku yi baƙin ciki a kan abin da ya kuɓuce muku, kuma kada ku yi mumar
alfahari da abin da Ya bã ku. Kuma Allah bã Ya son dukkan mai tãƙama, mai
alfahari.
Haƙĩƙa, lalle Mun aiko ManzanninMu da hujjõji bayyanannu, kuma Muka saukar da
Littãfi da sikẽli tãre da su dõmin mutãne su tsayu da ãdalci, kuma Mun saukar da
baƙin ƙarfe, a cikinsa akwai cutarwa mai tsanani da amfãni ga mutãne, kuma dõmin
Allah Ya san mai taimakonSa da ManzanninSa a fake. Lalle ne Allah Mai ƙarfi ne,
Mabuwãyi.
Kuma haƙĩƙa, lalle, Mun aiki Nũhu da Ibrahĩm, kuma Muka sanya Annabci da Littĩfi
a cikin zuriyarsu; daga cikinsu akwai mai nẽman shiryuwa, kuma mãsu yawa daga
cikinsu fasiƙai ne.
Sa'an nan Muka biyar a bãyansu da ManzanninMu; kuma Muka biyar da ĩsã ɗan
Maryama, kuma Muka ba shi Linjila kuma Muka sanya tausayi da rahama a cikin
zukãtan waɗanda suka bĩ shi, da ruhbãnanci wanda suka ƙãga, shi, ba Mu rubũta
shi ba a kansu, fãce dai (Mun rubũta musu nẽman yardar Allah, sa'an nan ba su
tsare shi haƙƙin tsarẽwarsa ba, sabõda haka Muka bai wa waɗanda suka yi ĩmãni
daga cikinsu sakamakonsu kuma mãsu yawa daga cikinsu fãsiƙai ne.
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, ku yi ĩmãni da ManzonSa Ya
bã ku rabo biyu daga rahamarSa, kuma Ya sanya muku wani haske wanda kuke yin
tafiya da shi, kuma Ya gãfarta muku. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai rahama.
Dõmin kada mutãnen Littãfi su san cẽwa lalle bã su da ikon yi ga kõme na falalar
Allah, kuma ita falalar ga hannun Allah kawai take, Yanã bãyar da ita ga wanda
Ya so (wannan jãhilci yã hana su ĩmani). Kuma Al1ah Mai falala ne mai girma.