First Ayah 1 الأية الأوليبِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
Ayah 20:2 الأية
مَا أَنزَلْنَا عَلَيْكَ الْقُرْآنَ لِتَشْقَىٰ
Hausa
Ba Mu saukar da Alƙur'ãni a gare ka dõmin ka wahala ba.
|
Ayah 20:3 الأية
إِلَّا تَذْكِرَةً لِّمَن يَخْشَىٰ
Hausa
Fãce dõmin tunãtarwa ga wanda ke tsõron Allah.
|
Ayah 20:4 الأية
تَنزِيلًا مِّمَّنْ خَلَقَ الْأَرْضَ وَالسَّمَاوَاتِ الْعُلَى
Hausa
(An saukar da shi) saukarwa daga wanda Ya halitta ƙasa da sammai maɗaukaka.
|
Ayah 20:5 الأية
الرَّحْمَٰنُ عَلَى الْعَرْشِ اسْتَوَىٰ
Hausa
Mai rahama, Ya daidaita a kan Al'arshi.
|
Ayah 20:6 الأية
لَهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا وَمَا تَحْتَ
الثَّرَىٰ
Hausa
Abin da yake a cikin sammai nãSa ne, da abin da yake a cikin ƙasa da abin da
yake a tsakãninsu da abin da ke ƙarƙashin turɓãya.
|
Ayah 20:7 الأية
وَإِن تَجْهَرْ بِالْقَوْلِ فَإِنَّهُ يَعْلَمُ السِّرَّ وَأَخْفَى
Hausa
Kuma idan ka bayyana da magana, to, lalle Shi, Yanã sanin asĩri da mafi bõyuwa.
|
Ayah 20:8 الأية
اللَّهُ لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ۖ لَهُ الْأَسْمَاءُ الْحُسْنَىٰ
Hausa
Allah bãbu abin bautãwa fãce Shi. Yanã da sunãye mafiya kyau.
|
Ayah 20:9 الأية
وَهَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ مُوسَىٰ
Hausa
Kuma shin, lãbarin Mũsã yãje maka?
|
Ayah 20:10 الأية
إِذْ رَأَىٰ نَارًا فَقَالَ لِأَهْلِهِ امْكُثُوا إِنِّي آنَسْتُ نَارًا لَّعَلِّي
آتِيكُم مِّنْهَا بِقَبَسٍ أَوْ أَجِدُ عَلَى النَّارِ هُدًى
Hausa
A lõkacin da ya ga wata wuta, sai ya ce wa iyãlinsa, "Ku dãkata. Lalle ne nĩ, na
tsinkãyi wata wuta tsammãnĩna in zo mukuda makãmashi daga gare ta, kõ kuwa in
sãmi wata shiriya a kan wutar."
|
Ayah 20:11 الأية
فَلَمَّا أَتَاهَا نُودِيَ يَا مُوسَىٰ
Hausa
Sa'an nan a lõkacin da ya je mata, aka kira shi, "Ya Mũsã!"
|
Ayah 20:12 الأية
إِنِّي أَنَا رَبُّكَ فَاخْلَعْ نَعْلَيْكَ ۖ إِنَّكَ بِالْوَادِ الْمُقَدَّسِ
طُوًى
Hausa
"Lalle ne, Nĩ ne Ubangijnka, sai ka ɗẽbe takalmanka Lalle ne kanã a rãfin nan
abin tsarkakẽwa, ¦uwa."
|
Ayah 20:13 الأية
وَأَنَا اخْتَرْتُكَ فَاسْتَمِعْ لِمَا يُوحَىٰ
Hausa
"Kuma Nĩ Nã zãɓe ka. Sai ka saurãra ga abin da ake yin wahayi."
|
Ayah 20:14 الأية
إِنَّنِي أَنَا اللَّهُ لَا إِلَٰهَ إِلَّا أَنَا فَاعْبُدْنِي وَأَقِمِ الصَّلَاةَ
لِذِكْرِي
Hausa
"Lalle, Nĩ Ni ne Allah. Bãbu abin bautawa fãce Ni. Sai ka bauta Mini, kuma ka
tsayar da salla dõmin tuna Ni."
|
Ayah 20:15 الأية
إِنَّ السَّاعَةَ آتِيَةٌ أَكَادُ أُخْفِيهَا لِتُجْزَىٰ كُلُّ نَفْسٍ بِمَا
تَسْعَىٰ
Hausa
"Lalle ne Sa'a mai zuwa ce, lnã kusa da In ɓõye ta dõmin a sãka wa dukan rai da
abin da yake aikatãwa."
|
Ayah 20:16 الأية
فَلَا يَصُدَّنَّكَ عَنْهَا مَن لَّا يُؤْمِنُ بِهَا وَاتَّبَعَ هَوَاهُ فَتَرْدَىٰ
Hausa
"Sabõda haka, kada wanda bã ya yin ĩmãni da ita kumaya bi son zuciyarsa, ya
taushe ka daga gare ta har ka halaka."
|
Ayah 20:17 الأية
وَمَا تِلْكَ بِيَمِينِكَ يَا مُوسَىٰ
Hausa
"Kuma wãce ce waccan ga dãmanka yã Mũsa!"
|
Ayah 20:18 الأية
قَالَ هِيَ عَصَايَ أَتَوَكَّأُ عَلَيْهَا وَأَهُشُّ بِهَا عَلَىٰ غَنَمِي وَلِيَ
فِيهَا مَآرِبُ أُخْرَىٰ
Hausa
Ya ce: "Ita sandãta ce, inã dõgara a kanta, kuma inã kakkaɓar ganye da ita a kan
ƙananan bisãshẽna kuma inã da waɗansu bukãtõci na dabam a gare ta."
|
Ayah 20:19 الأية
قَالَ أَلْقِهَا يَا مُوسَىٰ
Hausa
Ya ce: "Ka yi jĩfa da ĩta, yã Mũsã!"
|
Ayah 20:20 الأية
فَأَلْقَاهَا فَإِذَا هِيَ حَيَّةٌ تَسْعَىٰ
Hausa
Sai ya jẽfa ta. Sai gã ta dabbar macĩjiya, tanã tafiya da gaggãwa.
|
Ayah 20:21 الأية
قَالَ خُذْهَا وَلَا تَخَفْ ۖ سَنُعِيدُهَا سِيرَتَهَا الْأُولَىٰ
Hausa
Ya ce: "Ka kãma ta kuma kada ka ji tsõro. Za Mu mayar da ita ga hãlinta na
farko."
|
Ayah 20:22 الأية
وَاضْمُمْ يَدَكَ إِلَىٰ جَنَاحِكَ تَخْرُجْ بَيْضَاءَ مِنْ غَيْرِ سُوءٍ آيَةً
أُخْرَىٰ
Hausa
"Kuma ka haɗa hannunka zuwa ga damtsenka, ya fita yanã fari, bãbu sõfane, wata
ãyã ta dabam."
|
Ayah 20:23 الأية
لِنُرِيَكَ مِنْ آيَاتِنَا الْكُبْرَى
Hausa
"Dõmin Mu nũna maka daga ãyõyinMu manya."
|
Ayah 20:24 الأية
اذْهَبْ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ إِنَّهُ طَغَىٰ
Hausa
"Ka tafi zuwa ga Fĩr'auna. Lalle shĩ ya ƙẽtare haddi (da girman kai)."
|
Ayah 20:25 الأية
قَالَ رَبِّ اشْرَحْ لِي صَدْرِي
Hausa
Ya ce: "Ya Ubangiji! Ka buɗa mini, ƙirjĩna.
|
Ayah 20:26 الأية
وَيَسِّرْ لِي أَمْرِي
Hausa
"Kuma ka sauƙaƙe mini al'amarĩna."
|
Ayah 20:27 الأية
وَاحْلُلْ عُقْدَةً مِّن لِّسَانِي
Hausa
"Kuma Ka warware mini wani ƙulli daga harshẽna."
|
Ayah 20:28 الأية
يَفْقَهُوا قَوْلِي
Hausa
"Su fahimci maganãta."
|
Ayah 20:29 الأية
وَاجْعَل لِّي وَزِيرًا مِّنْ أَهْلِي
Hausa
"Kuma Ka sanya mini wani mataimaki daga mutãnena."
|
Ayah 20:30 الأية
هَارُونَ أَخِي
Hausa
"Hãrũna ɗan'uwana."
|
Ayah 20:31 الأية
اشْدُدْ بِهِ أَزْرِي
Hausa
"Ka ƙarfafa halittata da shi."
|
Ayah 20:32 الأية
وَأَشْرِكْهُ فِي أَمْرِي
Hausa
"Kuma Ka shigar da shi a cikin al'amarina."
|
Ayah 20:33 الأية
كَيْ نُسَبِّحَكَ كَثِيرًا
Hausa
"Dõmin mu tsarkake Ka da yawa."
|
Ayah 20:34 الأية
وَنَذْكُرَكَ كَثِيرًا
Hausa
"Kuma mu tuna Ka da yawa."
|
Ayah 20:35 الأية
إِنَّكَ كُنتَ بِنَا بَصِيرًا
Hausa
"Lalle Kai, Ka kasance Mai gani gare mu."
|
Ayah 20:36 الأية
قَالَ قَدْ أُوتِيتَ سُؤْلَكَ يَا مُوسَىٰ
Hausa
Ya ce: "Lalle ne, an bã ka rõƙonka, yã Mũsã!"
|
Ayah 20:37 الأية
وَلَقَدْ مَنَنَّا عَلَيْكَ مَرَّةً أُخْرَىٰ
Hausa
"Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun yi wata baiwa gare ka a wani lõkacin na dabam."
|
Ayah 20:38 الأية
إِذْ أَوْحَيْنَا إِلَىٰ أُمِّكَ مَا يُوحَىٰ
Hausa
"A lõkacin da Muka yi wahayin abin da aka yi wahayi zuwa ga uwarka."
|
Ayah 20:39 الأية
أَنِ اقْذِفِيهِ فِي التَّابُوتِ فَاقْذِفِيهِ فِي الْيَمِّ فَلْيُلْقِهِ الْيَمُّ
بِالسَّاحِلِ يَأْخُذْهُ عَدُوٌّ لِّي وَعَدُوٌّ لَّهُ ۚ وَأَلْقَيْتُ عَلَيْكَ
مَحَبَّةً مِّنِّي وَلِتُصْنَعَ عَلَىٰ عَيْنِي
Hausa
"Cẽwa, Ki jẽfa shi a cikin akwatin nan, sa'an nan ki jẽfa shi a cikin kõgi,
sa'an nan kogin ya jefa shi a gãɓa, wani maƙiyi Nãwa kuma maƙiyi nãsa ya ɗauke
shi.' Kuma Na jẽfa wani so daga gare Ni a kanka. Kuma dõmin a riƙe ka da kyau a
kan ganiNa."
|
Ayah 20:40 الأية
إِذْ تَمْشِي أُخْتُكَ فَتَقُولُ هَلْ أَدُلُّكُمْ عَلَىٰ مَن يَكْفُلُهُ ۖ
فَرَجَعْنَاكَ إِلَىٰ أُمِّكَ كَيْ تَقَرَّ عَيْنُهَا وَلَا تَحْزَنَ ۚ وَقَتَلْتَ
نَفْسًا فَنَجَّيْنَاكَ مِنَ الْغَمِّ وَفَتَنَّاكَ فُتُونًا ۚ فَلَبِثْتَ سِنِينَ
فِي أَهْلِ مَدْيَنَ ثُمَّ جِئْتَ عَلَىٰ قَدَرٍ يَا مُوسَىٰ
Hausa
"A sa'ad da 'yar'uwrka ke tafiya har ta ce, shin, in shiryar da ku ga wanda ke
rẽnonsa?' Sai Muka mayar da kai zuwa ga uwarka dõmin idonta ya yi sanyi kuma bã
zã ta yi baƙin ciki ba. Kuma kã kashe wani rai, sa'an nan Muka tsẽrar da kai
daga baƙin ciki, kuma Muka fitine ka da waɗansu fitinõni. Sa'an nan ka zauna
shẽkaru a cikin mutãnen Madyana. Sa'an nan kuma ka zo a kan wata ƙaddara, yã
Mũsã!
|
Ayah 20:41 الأية
وَاصْطَنَعْتُكَ لِنَفْسِي
Hausa
"Kuma Na zãɓe ka dõmin Kaina."
|
Ayah 20:42 الأية
اذْهَبْ أَنتَ وَأَخُوكَ بِآيَاتِي وَلَا تَنِيَا فِي ذِكْرِي
Hausa
"Ka tafi kai da ɗan'uwanka game da ãyõyiNa, kuma kada ku yi rauni ga ambatõNa."
|
Ayah 20:43 الأية
اذْهَبَا إِلَىٰ فِرْعَوْنَ إِنَّهُ طَغَىٰ
Hausa
"Ku tafi kũ biyu zuwa ga Fir'auna. Lalle shĩ ya ƙẽtare haddi (ga girman kai)."
|
Ayah 20:44 الأية
فَقُولَا لَهُ قَوْلًا لَّيِّنًا لَّعَلَّهُ يَتَذَكَّرُ أَوْ يَخْشَىٰ
Hausa
"Sai ku gaya masa magana mai laushi, tsammãninsa yanã tunãwa kõ kuwa ya ji
tsõro."
|
Ayah 20:45 الأية
قَالَا رَبَّنَا إِنَّنَا نَخَافُ أَن يَفْرُطَ عَلَيْنَا أَوْ أَن يَطْغَىٰ
Hausa
Su biyu suka ce: "Ya Ubangijinmu! Lalle ne munã tsõron ya yi gaggawa a kanmu, kõ
ya ƙẽtare haddi."
|
Ayah 20:46 الأية
قَالَ لَا تَخَافَا ۖ إِنَّنِي مَعَكُمَا أَسْمَعُ وَأَرَىٰ
Hausa
Ya ce: "Kada ku ji tsõro. Lalle Nĩ, Inã tãre da ku, Inaji, kuma Inã gani."
|
Ayah 20:47 الأية
فَأْتِيَاهُ فَقُولَا إِنَّا رَسُولَا رَبِّكَ فَأَرْسِلْ مَعَنَا بَنِي
إِسْرَائِيلَ وَلَا تُعَذِّبْهُمْ ۖ قَدْ جِئْنَاكَ بِآيَةٍ مِّن رَّبِّكَ ۖ
وَالسَّلَامُ عَلَىٰ مَنِ اتَّبَعَ الْهُدَىٰ
Hausa
"Sai ku jẽ masa sa'an nan ku ce, Lalle mũ, Manzanni biyune na Ubangijinka, sai
ka saki Banĩ Isrã'ĩla tãre da mu. Kuma kada ka yi musu azãba. Haƙĩƙa mun zomaka
da wata ãyã daga, Ubangijinka. Kuma aminci ya tabbata ga wanda ya bi shiriya."
|
Ayah 20:48 الأية
إِنَّا قَدْ أُوحِيَ إِلَيْنَا أَنَّ الْعَذَابَ عَلَىٰ مَن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ
Hausa
"Lalle mũ, haƙĩƙa, an yi wahayi zuwa gare mu, cẽwaazãba tanã a kan wanda ya
ƙaryata, kuma ya jũya bãya."
|
Ayah 20:49 الأية
قَالَ فَمَن رَّبُّكُمَا يَا مُوسَىٰ
Hausa
Ya ce: "To, wãne ne Ubangijinku? Ya Mũsã!"
|
Ayah 20:50 الأية
قَالَ رَبُّنَا الَّذِي أَعْطَىٰ كُلَّ شَيْءٍ خَلْقَهُ ثُمَّ هَدَىٰ
Hausa
Ya ce: "Ubangijinmu Shi ne wanda Ya bai wa dukan kõme halittarsa, sa'an nan Ya
shiryar."
|
Ayah 20:51 الأية
قَالَ فَمَا بَالُ الْقُرُونِ الْأُولَىٰ
Hausa
Ya ce: "To, mẽne hãlin ƙarnõnin farko?"
|
Ayah 20:52 الأية
قَالَ عِلْمُهَا عِندَ رَبِّي فِي كِتَابٍ ۖ لَّا يَضِلُّ رَبِّي وَلَا يَنسَى
Hausa
Ya ce: "Saninsu yanã a wurin Ubangijĩna, Ubangijĩna bã Ya ɓacẽwa kuma bã Ya
mantuwa."
|
Ayah 20:53 الأية
الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ الْأَرْضَ مَهْدًا وَسَلَكَ لَكُمْ فِيهَا سُبُلًا وَأَنزَلَ
مِنَ السَّمَاءِ مَاءً فَأَخْرَجْنَا بِهِ أَزْوَاجًا مِّن نَّبَاتٍ شَتَّىٰ
Hausa
"Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma Ya shigar muku da hanyõyi a cikinta,
kuma Ya saukar da ruwa daga sama." Sa'an nan game da shi Muka fitar da
nau'i-nau'i daga tsirũruwa dabam-dabam.
|
Ayah 20:54 الأية
كُلُوا وَارْعَوْا أَنْعَامَكُمْ ۗ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّأُولِي النُّهَىٰ
Hausa
Ku ci kuma ku yi kiwon dabbõbin ni'imarku. Lalle ne, a cikin wannan akwai ãyõyi
ga masu hankali.
|
Ayah 20:55 الأية
مِنْهَا خَلَقْنَاكُمْ وَفِيهَا نُعِيدُكُمْ وَمِنْهَا نُخْرِجُكُمْ تَارَةً
أُخْرَىٰ
Hausa
Daga gare ta Muka halitta ku, kuma a cikinta Muke mayar da ku, kuma daga gare ta
Muke fitar da ku a wani lõkaci na dabam.
|
Ayah 20:56 الأية
وَلَقَدْ أَرَيْنَاهُ آيَاتِنَا كُلَّهَا فَكَذَّبَ وَأَبَىٰ
Hausa
Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun nũna masa ãyõyinMu dukansu sai ya ƙaryata, kuma ya ƙiya!
|
Ayah 20:57 الأية
قَالَ أَجِئْتَنَا لِتُخْرِجَنَا مِنْ أَرْضِنَا بِسِحْرِكَ يَا مُوسَىٰ
Hausa
Ya ce: "Shin kã zo mana ne dõmin ka fitar da mu daga ƙasarmu game da sihirinka,
yã Mũsã?"
|
Ayah 20:58 الأية
فَلَنَأْتِيَنَّكَ بِسِحْرٍ مِّثْلِهِ فَاجْعَلْ بَيْنَنَا وَبَيْنَكَ مَوْعِدًا
لَّا نُخْلِفُهُ نَحْنُ وَلَا أَنتَ مَكَانًا سُوًى
Hausa
"To, lalle ne munã zo maka da wani sihiri irinsa. Sai ka sanya wani wa'adi a
tsakãninmu da tsakãninka bã mu sãɓa masa mũ kai kuma, bã ka sãɓãwa, a wani wuri
mai dãcẽwa."
|
Ayah 20:59 الأية
قَالَ مَوْعِدُكُمْ يَوْمُ الزِّينَةِ وَأَن يُحْشَرَ النَّاسُ ضُحًى
Hausa
Ya ce: "Wa'adinku shi ne rãnar ƙawa kuma a tãra mutãne da hantsi."
|
Ayah 20:60 الأية
فَتَوَلَّىٰ فِرْعَوْنُ فَجَمَعَ كَيْدَهُ ثُمَّ أَتَىٰ
Hausa
Sai Fir'auna ya jũya, sa'an nan ya tãra mugunyar dabãrarsa, sa'an nan kuma ya
zo.
|
Ayah 20:61 الأية
قَالَ لَهُم مُّوسَىٰ وَيْلَكُمْ لَا تَفْتَرُوا عَلَى اللَّهِ كَذِبًا
فَيُسْحِتَكُم بِعَذَابٍ ۖ وَقَدْ خَابَ مَنِ افْتَرَىٰ
Hausa
Mũsã ya ce musu, "Kaitõnku! Kada ku ƙirƙira ƙarya ga Allah har Ya tumɓuke ku da
wata azãba. Kuma wanda ya ƙirƙira ƙarya, yã tãɓe."
|
Ayah 20:62 الأية
فَتَنَازَعُوا أَمْرَهُم بَيْنَهُمْ وَأَسَرُّوا النَّجْوَىٰ
Hausa
Sai suka yi jãyayya ga al'amarinsu a tsakãninsu kuma suka asirta gãnawa.
|
Ayah 20:63 الأية
قَالُوا إِنْ هَٰذَانِ لَسَاحِرَانِ يُرِيدَانِ أَن يُخْرِجَاكُم مِّنْ أَرْضِكُم
بِسِحْرِهِمَا وَيَذْهَبَا بِطَرِيقَتِكُمُ الْمُثْلَىٰ
Hausa
Suka ce: "Lalle ne waɗannan biyun, haƙĩƙa masihirta ne sunã nufin su fitar da ku
daga ƙasarku game da sihirinsu kuma su tafi da tabĩ'arku mafĩficiya."
|
Ayah 20:64 الأية
فَأَجْمِعُوا كَيْدَكُمْ ثُمَّ ائْتُوا صَفًّا ۚ وَقَدْ أَفْلَحَ الْيَوْمَ مَنِ
اسْتَعْلَىٰ
Hausa
"Sai ku haɗa dabãrarku sa'an nan kuma ku tafi a sahu guda, kuma haƙĩƙa, wanda ya
rinjãya, a yau, ya rabbanta."
|
Ayah 20:65 الأية
قَالُوا يَا مُوسَىٰ إِمَّا أَن تُلْقِيَ وَإِمَّا أَن نَّكُونَ أَوَّلَ مَنْ
أَلْقَىٰ
Hausa
Suka ce: "Ya Mũsã! Imma ka jefa, ko kuma mu kasance farkon mai jẽfawa."
|
Ayah 20:66 الأية
قَالَ بَلْ أَلْقُوا ۖ فَإِذَا حِبَالُهُمْ وَعِصِيُّهُمْ يُخَيَّلُ إِلَيْهِ مِن
سِحْرِهِمْ أَنَّهَا تَسْعَىٰ
Hausa
Ya ce: "Ã'a, ku jẽfa." Sai gã igiyoyinsu da sandunansu anã sũranta su a gare
shi, daga sihirinsu, lalle sunã tafiya da sauri.
|
Ayah 20:67 الأية
فَأَوْجَسَ فِي نَفْسِهِ خِيفَةً مُّوسَىٰ
Hausa
Sai Mũsã ya ji tsõro a cikin ransa.
|
Ayah 20:68 الأية
قُلْنَا لَا تَخَفْ إِنَّكَ أَنتَ الْأَعْلَىٰ
Hausa
Muka ce: "Kada ka ji tsõro. lalle kai ne mafi ɗaukaka."
|
Ayah 20:69 الأية
وَأَلْقِ مَا فِي يَمِينِكَ تَلْقَفْ مَا صَنَعُوا ۖ إِنَّمَا صَنَعُوا كَيْدُ
سَاحِرٍ ۖ وَلَا يُفْلِحُ السَّاحِرُ حَيْثُ أَتَىٰ
Hausa
"Kuma ka jẽfa abin da ke a cikin hannun dãmanka, ta cafe abin da suka aikata.
Lalle ne abin da suka aikata mãkircin masihirci ne kuma masihirci bã ya cin
nasara a duk inda ya je."
|
Ayah 20:70 الأية
فَأُلْقِيَ السَّحَرَةُ سُجَّدًا قَالُوا آمَنَّا بِرَبِّ هَارُونَ وَمُوسَىٰ
Hausa
Sai aka jẽfar da masihirtan sunã mãsu sujada, suka ce: "Mun yi ĩmãni da
Ubangijin Hãrũna da Mũsã."
|
Ayah 20:71 الأية
قَالَ آمَنتُمْ لَهُ قَبْلَ أَنْ آذَنَ لَكُمْ ۖ إِنَّهُ لَكَبِيرُكُمُ الَّذِي
عَلَّمَكُمُ السِّحْرَ ۖ فَلَأُقَطِّعَنَّ أَيْدِيَكُمْ وَأَرْجُلَكُم مِّنْ
خِلَافٍ وَلَأُصَلِّبَنَّكُمْ فِي جُذُوعِ النَّخْلِ وَلَتَعْلَمُنَّ أَيُّنَا
أَشَدُّ عَذَابًا وَأَبْقَىٰ
Hausa
Ya ce: "Kun yi ĩmãni sabõda shi a gabãnin in yi muku izni? Lalle shĩ, haƙĩƙa,
babbanku ne wanda ya sanar da ku sihirin! To, lalle ne zan kakkãtse hannayenku
da ƙafãfunku a tarnaƙi kuma lalle zan tsĩre ku a cikin kututturan itãcen dabĩno,
kuma lalle zã ku sani wanenmu ne mafi tsananin azãba kuma wãne ne mafi wanzuwar
(azãba)."
|
Ayah 20:72 الأية
قَالُوا لَن نُّؤْثِرَكَ عَلَىٰ مَا جَاءَنَا مِنَ الْبَيِّنَاتِ وَالَّذِي
فَطَرَنَا ۖ فَاقْضِ مَا أَنتَ قَاضٍ ۖ إِنَّمَا تَقْضِي هَٰذِهِ الْحَيَاةَ
الدُّنْيَا
Hausa
Suka ce: "Bã zã mu fĩfĩta ka ba faufau a kan abin da ya zo mana na hujjõji. Munã
rantsuwa da wanda Ya ƙãga halittarmu sai ka hukunta abin da kake mai hukuntãwa,
ai kanã ƙãre wannan rãyuwar dũniya kawai ne."
|
Ayah 20:73 الأية
إِنَّا آمَنَّا بِرَبِّنَا لِيَغْفِرَ لَنَا خَطَايَانَا وَمَا أَكْرَهْتَنَا
عَلَيْهِ مِنَ السِّحْرِ ۗ وَاللَّهُ خَيْرٌ وَأَبْقَىٰ
Hausa
"Lalle mũ, mun yi ĩmãni da Ubangijinmu dõmin Ya gãfarta mana laifuffukanmu da
abin da ka tĩlasta mu a kansa na sihiri. Kuma Allah ne Mafi alhẽri, kumaMafi
wanzuwa."
|
Ayah 20:74 الأية
إِنَّهُ مَن يَأْتِ رَبَّهُ مُجْرِمًا فَإِنَّ لَهُ جَهَنَّمَ لَا يَمُوتُ فِيهَا
وَلَا يَحْيَىٰ
Hausa
Lalle shĩ wanda ya je wa Ubangijinsa yanã mai laifi, to lalle ne yanã da
Jahannama, bã ya mutuwa a cikinta kuma bã ya rãyuwa.
|
Ayah 20:75 الأية
وَمَن يَأْتِهِ مُؤْمِنًا قَدْ عَمِلَ الصَّالِحَاتِ فَأُولَٰئِكَ لَهُمُ
الدَّرَجَاتُ الْعُلَىٰ
Hausa
Kuma wanda ya je Masa yanã mai ĩmãni, alhãli kuwaya aikata aikin ƙwarai to
waɗannan sunã da darajõji maɗaukaka.
|
Ayah 20:76 الأية
جَنَّاتُ عَدْنٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا ۚ وَذَٰلِكَ
جَزَاءُ مَن تَزَكَّىٰ
Hausa
Gidãjen Aljannar zama kõguna na gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a
cikinsu. Kuma wannan ne sakamakon wanda ya tsarkaku.
|
Ayah 20:77 الأية
وَلَقَدْ أَوْحَيْنَا إِلَىٰ مُوسَىٰ أَنْ أَسْرِ بِعِبَادِي فَاضْرِبْ لَهُمْ
طَرِيقًا فِي الْبَحْرِ يَبَسًا لَّا تَخَافُ دَرَكًا وَلَا تَخْشَىٰ
Hausa
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa, "Ka yi tafiyar dare da
bãyiNa. Sa'an nan ka dõka musu hanya a cikin tẽku tana ƙẽƙasasshiya, bã ka
tsõron riskuwa, kuma bã ka fargabar nutsẽwa."
|
Ayah 20:78 الأية
فَأَتْبَعَهُمْ فِرْعَوْنُ بِجُنُودِهِ فَغَشِيَهُم مِّنَ الْيَمِّ مَا غَشِيَهُمْ
Hausa
Sai Fir'auna ya bi su game da rundunarsa. Sai abin da ya rufe su daga tẽku ya
rufe su.
|
Ayah 20:79 الأية
وَأَضَلَّ فِرْعَوْنُ قَوْمَهُ وَمَا هَدَىٰ
Hausa
Kuma Fir'auna ya ɓatar da mutãnensa, kuma bai shiryar(dasu) ba.
|
Ayah 20:80 الأية
يَا بَنِي إِسْرَائِيلَ قَدْ أَنجَيْنَاكُم مِّنْ عَدُوِّكُمْ وَوَاعَدْنَاكُمْ
جَانِبَ الطُّورِ الْأَيْمَنَ وَنَزَّلْنَا عَلَيْكُمُ الْمَنَّ وَالسَّلْوَىٰ
Hausa
Yã Banĩ Isrã'ĩla! Lalle Mun tsẽrar da ku daga maƙiyinku, kuma mun yi muku wa'adi
a gẽfen Dũtsen nan na dãma, kuma Mun sassaukar da darɓa da tattabaru dõminku.
|
Ayah 20:81 الأية
كُلُوا مِن طَيِّبَاتِ مَا رَزَقْنَاكُمْ وَلَا تَطْغَوْا فِيهِ فَيَحِلَّ
عَلَيْكُمْ غَضَبِي ۖ وَمَن يَحْلِلْ عَلَيْهِ غَضَبِي فَقَدْ هَوَىٰ
Hausa
Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurtã ku kuma kada ku ƙẽtare haddi a cikinsa
har hushĩNa ya sauka a kanku. Kuma wanda hushĩNa ya sauka a kansa, to, lalle ne,
ya fãɗi.
|
Ayah 20:82 الأية
وَإِنِّي لَغَفَّارٌ لِّمَن تَابَ وَآمَنَ وَعَمِلَ صَالِحًا ثُمَّ اهْتَدَىٰ
Hausa
Kuma lalle Nĩ haƙĩƙa Mai gãfara ne ga wanda ya tũba kuma ya yi ĩmãni, kuma ya
aikata aikin ƙwarai, sa'an nan kuma ya nẽmi shiryuwa.
|
Ayah 20:83 الأية
وَمَا أَعْجَلَكَ عَن قَوْمِكَ يَا مُوسَىٰ
Hausa
"Kuma mẽne ne ya gaggautar da kai ga barin mutãnenka? Yã Mũsã!"
|
Ayah 20:84 الأية
قَالَ هُمْ أُولَاءِ عَلَىٰ أَثَرِي وَعَجِلْتُ إِلَيْكَ رَبِّ لِتَرْضَىٰ
Hausa
Ya ce: "Su ne waɗannan a kan sãwũna, kuma na yi gaggãwa zuwa gare Ka, yã
Ubangiji! Dõmin Ka yarda."
|
Ayah 20:85 الأية
قَالَ فَإِنَّا قَدْ فَتَنَّا قَوْمَكَ مِن بَعْدِكَ وَأَضَلَّهُمُ السَّامِرِيُّ
Hausa
Ya ce: "To, lalle ne, haƙĩƙa, Mun fitini, mutãnenka daga bayãnka, kuma sãmiri ya
ɓatar da su."
|
Ayah 20:86 الأية
فَرَجَعَ مُوسَىٰ إِلَىٰ قَوْمِهِ غَضْبَانَ أَسِفًا ۚ قَالَ يَا قَوْمِ أَلَمْ
يَعِدْكُمْ رَبُّكُمْ وَعْدًا حَسَنًا ۚ أَفَطَالَ عَلَيْكُمُ الْعَهْدُ أَمْ
أَرَدتُّمْ أَن يَحِلَّ عَلَيْكُمْ غَضَبٌ مِّن رَّبِّكُمْ فَأَخْلَفْتُم
مَّوْعِدِي
Hausa
Sai Mũsã ya kõma zuwa ga mutãnensa yanã mai hushi, mai baƙin ciki, ya ce: "Yã
mutãnẽna! shin, Ubangijinku bai yi muku wa'adi ba, wa'adi mai kyau? Shin,
lõkacin ya yi tsãwo a kanku ne, kõ kun yi nufi ne wani hushi ya sauka a kanku
daga Ubangijinku, sabõda haka kuka sãɓã wa alkawarĩna?"
|
Ayah 20:87 الأية
قَالُوا مَا أَخْلَفْنَا مَوْعِدَكَ بِمَلْكِنَا وَلَٰكِنَّا حُمِّلْنَا أَوْزَارًا
مِّن زِينَةِ الْقَوْمِ فَقَذَفْنَاهَا فَكَذَٰلِكَ أَلْقَى السَّامِرِيُّ
Hausa
Suka ce: "Ba mu sãɓa wa alkawarinka ba da ĩkonmu kuma amma an ɗõra mana waɗansu
kãya masu nauyi daga abin ƙawar mutãnen ne, sai muka jẽfar da su. Sa'an nan
kamar haka ne sãmiri ya jẽfa."
|
Ayah 20:88 الأية
فَأَخْرَجَ لَهُمْ عِجْلًا جَسَدًا لَّهُ خُوَارٌ فَقَالُوا هَٰذَا إِلَٰهُكُمْ
وَإِلَٰهُ مُوسَىٰ فَنَسِيَ
Hausa
"Sai ya fitar musu da wani maraƙi, jikin mutãne, yanã rũri, sa'an nan suka ce:
wannan ne gunkinku kuma gunkin Mũsã, sai ya manta."
|
Ayah 20:89 الأية
أَفَلَا يَرَوْنَ أَلَّا يَرْجِعُ إِلَيْهِمْ قَوْلًا وَلَا يَمْلِكُ لَهُمْ ضَرًّا
وَلَا نَفْعًا
Hausa
Shin, to, bã su ganin cẽwabã ya mayar musu da magana, kuma bã ya mallakar wata
cũta a gare su, kuma bã ya mallakar amfãni?
|
Ayah 20:90 الأية
وَلَقَدْ قَالَ لَهُمْ هَارُونُ مِن قَبْلُ يَا قَوْمِ إِنَّمَا فُتِنتُم بِهِ ۖ
وَإِنَّ رَبَّكُمُ الرَّحْمَٰنُ فَاتَّبِعُونِي وَأَطِيعُوا أَمْرِي
Hausa
Kuma, haƙĩƙa, Hãrũna yã ce musu daga gabãni, "Yã mutãnẽna! Lalle an fitinẽ ku da
shi ne kawai. Kuma lalle Ubangijinku Mai rahama ne, sai ku bi ni, kuma ku yi
ɗã'ã ga umurnĩna."
|
Ayah 20:91 الأية
قَالُوا لَن نَّبْرَحَ عَلَيْهِ عَاكِفِينَ حَتَّىٰ يَرْجِعَ إِلَيْنَا مُوسَىٰ
Hausa
Suka ce: "Ba zã mu gushe ba faufau a kansa munã mãsu lazimta, sai Mũsã ya kõmo
zuwa gare mu."
|
Ayah 20:92 الأية
قَالَ يَا هَارُونُ مَا مَنَعَكَ إِذْ رَأَيْتَهُمْ ضَلُّوا
Hausa
(Mũsã) ya ce: "Yã Hãrũna! Mẽ ya hane ka, sa'ad da kagan su sun ɓace."
|
Ayah 20:93 الأية
أَلَّا تَتَّبِعَنِ ۖ أَفَعَصَيْتَ أَمْرِي
Hausa
"Ba ka bĩ ni ba! Shin, to, ka sãɓã wa umurnina ne?"
|
Ayah 20:94 الأية
قَالَ يَا ابْنَ أُمَّ لَا تَأْخُذْ بِلِحْيَتِي وَلَا بِرَأْسِي ۖ إِنِّي خَشِيتُ
أَن تَقُولَ فَرَّقْتَ بَيْنَ بَنِي إِسْرَائِيلَ وَلَمْ تَرْقُبْ قَوْلِي
Hausa
(Hãrũna) ya ce: "Yã ɗãn'uwãna! Kada ka yi kãmu ga gẽmũna kõ ga kaina. Lalle nĩ,
nã ji tsõron ka ce: Ka rarraba a tsakãnin Banĩ Isrã'ĩla kuma ba ka tsare
maganata ba."
|
Ayah 20:95 الأية
قَالَ فَمَا خَطْبُكَ يَا سَامِرِيُّ
Hausa
(Mũsã) ya ce: "Mẽne ne babban al'amarinka? Ya Sãmiri!"
|
Ayah 20:96 الأية
قَالَ بَصُرْتُ بِمَا لَمْ يَبْصُرُوا بِهِ فَقَبَضْتُ قَبْضَةً مِّنْ أَثَرِ
الرَّسُولِ فَنَبَذْتُهَا وَكَذَٰلِكَ سَوَّلَتْ لِي نَفْسِي
Hausa
(Sãmiri) ya ce: "Nã ga abin da ba su gan shi ba shi, sai na yi damƙa, damƙa guda
daga kufan sãwun Manzon, sa'an nan na jẽfa ta. Kuma haka dai raina ya ƙawãta
mini."
|
Ayah 20:97 الأية
قَالَ فَاذْهَبْ فَإِنَّ لَكَ فِي الْحَيَاةِ أَن تَقُولَ لَا مِسَاسَ ۖ وَإِنَّ
لَكَ مَوْعِدًا لَّن تُخْلَفَهُ ۖ وَانظُرْ إِلَىٰ إِلَٰهِكَ الَّذِي ظَلْتَ
عَلَيْهِ عَاكِفًا ۖ لَّنُحَرِّقَنَّهُ ثُمَّ لَنَنسِفَنَّهُ فِي الْيَمِّ نَسْفًا
Hausa
(Mũsã) ya ce: "To, ka tafi, sabõda haka lalle ne kanã da a cikin rãyuwarka, ka
ce 'Bãbu shãfa' kuma kanã da wani ma'alkawarta, bã zã a sãɓa maka gare ta ba.
Kuma ka dũba zuwa ga gunkinka wanda ka yini a kansa kanã mai lazimta. Lalle ne
muna ƙõne shi, sa'an nan kuma munã shẽƙe shi, a cikin tẽku, shẽƙẽwa."
|
Ayah 20:98 الأية
إِنَّمَا إِلَٰهُكُمُ اللَّهُ الَّذِي لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ۚ وَسِعَ كُلَّ
شَيْءٍ عِلْمًا
Hausa
Abin sani kawai abin bautãwarku Allah kawai ne wanda bãbu wani abin bautãwa,
fãce Shi kuma Yã yalwaci dukkan kõme da ilmi.
|
Ayah 20:99 الأية
كَذَٰلِكَ نَقُصُّ عَلَيْكَ مِنْ أَنبَاءِ مَا قَدْ سَبَقَ ۚ وَقَدْ آتَيْنَاكَ مِن
لَّدُنَّا ذِكْرًا
Hausa
Kamar wancan ne Muke lãbartãwa a gare ka, daga lãbãran abin da ya gabãta, alhãli
kuwa haƙĩƙa, Mun bã ka zikiri (Alƙur'ãni) daga gunMu.
|
Ayah 20:100 الأية
مَّنْ أَعْرَضَ عَنْهُ فَإِنَّهُ يَحْمِلُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وِزْرًا
Hausa
Wanda ya kau da kai daga gare shi, to, lalle shĩ, yanãɗaukar wani nauyi a Rãnar
¡iyãma.
|
Ayah 20:101 الأية
خَالِدِينَ فِيهِ ۖ وَسَاءَ لَهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ حِمْلًا
Hausa
Sunã madawwama a cikinsa, kuma yã mũnana ya zama abin ɗauka, a Rãnar ¡iyãma.
|
Ayah 20:102 الأية
يَوْمَ يُنفَخُ فِي الصُّورِ ۚ وَنَحْشُرُ الْمُجْرِمِينَ يَوْمَئِذٍ زُرْقًا
Hausa
A Rãnar da ake hũrãwa a cikin ƙãho kuma Munã tãra mãsu laifi, a rãnar nan, sunã
mãsu shũɗãyen idãnu.
|
Ayah 20:103 الأية
يَتَخَافَتُونَ بَيْنَهُمْ إِن لَّبِثْتُمْ إِلَّا عَشْرًا
Hausa
Suna ɓõye magana a tsakãninsu, (Sunã ce wa jũna) "Ba ku zauna ba (a cikin
dũniya) fãce kwãna gõma."
|
Ayah 20:104 الأية
نَّحْنُ أَعْلَمُ بِمَا يَقُولُونَ إِذْ يَقُولُ أَمْثَلُهُمْ طَرِيقَةً إِن
لَّبِثْتُمْ إِلَّا يَوْمًا
Hausa
Mu ne mafi sani ga abin da suke faɗa a sa'ad da mafĩficinsu ga hanya ke cẽwa,
"Ba ku zauna ba fãce a yini guda."
|
Ayah 20:105 الأية
وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْجِبَالِ فَقُلْ يَنسِفُهَا رَبِّي نَسْفًا
Hausa
Kuma sunã tambayar ka daga duwãtsu sai ka ce: "Ubangijina Yana shẽƙe su shẽƙẽwa,
|
Ayah 20:106 الأية
فَيَذَرُهَا قَاعًا صَفْصَفًا
Hausa
Sa'an nan Yanã barin (wurinsu) faƙo mai santsi.
|
Ayah 20:107 الأية
لَّا تَرَىٰ فِيهَا عِوَجًا وَلَا أَمْتًا
Hausa
"Bã ka ganin karkata a cikinsa, kuma bã ka ganin wani tudu."
|
Ayah 20:108 الأية
يَوْمَئِذٍ يَتَّبِعُونَ الدَّاعِيَ لَا عِوَجَ لَهُ ۖ وَخَشَعَتِ الْأَصْوَاتُ
لِلرَّحْمَٰنِ فَلَا تَسْمَعُ إِلَّا هَمْسًا
Hausa
A rãnar nan sunã biyar mai kira, bãbu karkata a gare shi, kuma sautuka suka yi
kawaici ga Mai rahama, bã ka sauraren kõme fãce sautin tafiya.
|
Ayah 20:109 الأية
يَوْمَئِذٍ لَّا تَنفَعُ الشَّفَاعَةُ إِلَّا مَنْ أَذِنَ لَهُ الرَّحْمَٰنُ
وَرَضِيَ لَهُ قَوْلًا
Hausa
A yinin nan cẽto bã ya yin amfãni fãce wanda Mai rahama Ya yi masa izni kuma Ya
yarda da shi, da magan
|
Ayah 20:110 الأية
يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلَا يُحِيطُونَ بِهِ عِلْمًا
Hausa
Yanã sanin abin da ke a gaba gare su da abin da ke bãyansu, kuma bã su kẽwayẽwa
da shi ga sani.
|
Ayah 20:111 الأية
وَعَنَتِ الْوُجُوهُ لِلْحَيِّ الْقَيُّومِ ۖ وَقَدْ خَابَ مَنْ حَمَلَ ظُلْمًا
Hausa
Kuma fuskõki suka ƙanƙan da kai ga Rãyayye,Tsayayye, alhãli kuwa wanda ya ɗauko
wani zãlunci ya tãɓe.
|
Ayah 20:112 الأية
وَمَن يَعْمَلْ مِنَ الصَّالِحَاتِ وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَلَا يَخَافُ ظُلْمًا وَلَا
هَضْمًا
Hausa
Kuma wanda ya aikata wani abu daga ayyukan ƙwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni,
to, bã ya tsõron wani zãlunci ko wata naƙasa.
|
Ayah 20:113 الأية
وَكَذَٰلِكَ أَنزَلْنَاهُ قُرْآنًا عَرَبِيًّا وَصَرَّفْنَا فِيهِ مِنَ الْوَعِيدِ
لَعَلَّهُمْ يَتَّقُونَ أَوْ يُحْدِثُ لَهُمْ ذِكْرًا
Hausa
Kuma haka Muka saukar da shi, Alƙur'ãni, yanã abin karantãwa, da Larabci kuma
Muka jujjuya misãlai, a cikinsa, na tsõratarwa, tsammãninsu, sunã yin taƙawa ko
ya sabbaba musu wata wa'aztuwa.
|
Ayah 20:114 الأية
فَتَعَالَى اللَّهُ الْمَلِكُ الْحَقُّ ۗ وَلَا تَعْجَلْ بِالْقُرْآنِ مِن قَبْلِ
أَن يُقْضَىٰ إِلَيْكَ وَحْيُهُ ۖ وَقُل رَّبِّ زِدْنِي عِلْمًا
Hausa
Sa'an nan Allah Mamallaki, Tabbatacce Yã ɗaukaka. Kuma kada ka yi gaggãwa da
Alƙur'ãni a gabãnin a ƙãre wahayinsa zuwa gare ka. Kuma ka ce: "Yã Ubangiji! Ka
ƙãra mini ilmi."
|
Ayah 20:115 الأية
وَلَقَدْ عَهِدْنَا إِلَىٰ آدَمَ مِن قَبْلُ فَنَسِيَ وَلَمْ نَجِدْ لَهُ عَزْمًا
Hausa
Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun yi alkawari zuwa ga Ãdamu a gabãnin wannan, sai ya
manta, kuma ba Mu sãmi ƙarfin zũciya a gare shiba.
|
Ayah 20:116 الأية
وَإِذْ قُلْنَا لِلْمَلَائِكَةِ اسْجُدُوا لِآدَمَ فَسَجَدُوا إِلَّا إِبْلِيسَ
أَبَىٰ
Hausa
Kuma sa'ad da Muka ce wa malã'iku, "Ku yi sujada ga Ãdamu." Sai suka yi sujada,
fãce Iblĩsa, yã ƙiya.
|
Ayah 20:117 الأية
فَقُلْنَا يَا آدَمُ إِنَّ هَٰذَا عَدُوٌّ لَّكَ وَلِزَوْجِكَ فَلَا
يُخْرِجَنَّكُمَا مِنَ الْجَنَّةِ فَتَشْقَىٰ
Hausa
Sai Muka ce: "Ya Ãdamu! Lalle ne wannan maƙiyi ne gare ka da kuma ga mãtarka,
sabõda haka kada ya fitar da ku daga Aljanna har ku wahala."
|
|